Shin me ya sa Abuja ke fuskantar matsalar tsaro?

Abuja na daya daga cikin birane a Afirka da ke saurin samun yawan al'umma

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Abuja na daya daga cikin birane a Afirka da ke saurin samun yawan al'umma
    • Marubuci, Usman Minjibir
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Wannan tambaya ce da mazauna babban birnin kasar ke ta faman yi a kullum a 'yan watannin nan, tun bayan yawaitar hare-haren 'yan bindiga masu satar jama'a a birnin da kewaye.

Abubakar Isa, wani dan asalin jihar Kano kuma mazaunin Abuja ya shaida wa BBC yadda yake zaman dar-dar a babban birnin.

"Inna lillahi Wa Inna Ilaihirrajiun! Yanzu Abuja babu inda yake da tsaro. Mu kanmu da muke a Gwarinpa muna cikin zulumi.

Yanzu zan daina bin hanyar Bwari idan zan je Kano. Gwara kawai na bi ta Zuba duk da acewa akwai bambancin tazarar kilomita kusan 40," in ji Abubakar.

Irin yanayin da mazauna birnin Abuja ke ciki kenan babu na kwaryar birnin babu na kewaye.

Wata kididdiga da kamfanin tsaro na Beacon Consulting ya fitar ta nuna an samu hare-haren 'yan bindiga guda shida a watan Janairun 2024, inda kuma aka yi garkuwa da akalla mutum 71 a Abujar da kewaye.

Kididdigar ta kuma nuna cewa a shekarar 2023 an samu hare-haren 'yan bindiga guda 50 inda kuma aka sace mutum 247, a babban birnin tarayyar.

Harwayau, kamfanin na Beacon Conculting ya ce an fi samun matsalar tsaron a kananan hukumomi guda hudu daga cikin guda shida.

"Yankin Bwari da Kuje da Kwali an fi samun matsalar satar jama'a domin karbar fansa", in Malam Kabiru Adamu, shugaban kamfanin.

Ta ina 'yan bindiga ke shiga Abuja?

Auja

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hare-haren 'yan bindiga na kara ta'azzara a Abuja da kewaye
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Birnin Abuja dai ya yi iyaka da jihohi hudu masu fama da matsalar tsaro da suka hada da jihar Kaduna daga arewaci da jihar Naija daga yammaci sai kuma jihar Kogi da jihar Nassarawa daga kudanci.

Shugaban kamfanin Beacon Consulting, Malam Kabiru Adamu ya ce "wadannan 'yan bindiga na kwarorowa Abuja ne ta hanyar tsaunuka da suka hade da dazukan wadancan jihohin masu fama da matsalar tsaro kuma da alama ba mu ga wasu matakan da aka dauka ba domin dakile shigowarsu.

A baya-bayan nan mun ga yadda jami'an tsaro suka shiga dazukan da kan duwatsu domin yin abin da suka kira 'shara' to amma ba mu ga hakan ya rage yawaitar hare-hare ba", in ji Malam Kabiru.

Sai dai Group Captain Sadiq Garba mai ritaya wani mai sharhi kan harkar tsaro ya ce shi yana da ra'ayi na daban dangane da yadda batagarin ke shiga Abuja musamman ma cikin birnin.

"Ni a ra'ayina masu satar mutanen Abuja a cikin garin suke kuma idan suka saci mutanen a cikin garin suke boye su. Gazawar birnin ce ta janyo hakan saboda a manyan biranen duniya akwai na'urori da ke hana aikata laifuka".

Me ke jan hankalin 'yan bindigar zuwa Abuja?

Malam Kabiru Adamu da Group Captain Sadiq Mai ritaya sun ce abubuwa guda hudu ne suka ja hankalin 'yan bindiga suka rinka kwara zuwa Abuja.

  • Dazukan jihohin da ke makwabtaka da Abuja sun hade da juna kuma Abujar ce ta zama a tsakiya kamar wata mahada da za su rinka bi suna wucewa - idan an biyo su daga can sai su nufi.
  • A lokacin da suke wucewa ta tsaunuka da dazukan Abuja sun dauka Abujar tana da tsaron da ya kamata. Da farko suna kauce mata saboda rashin sanin abin da za su tarar. To amma da tafiya ta yi tafiya suka fahimci Abujar ba ta da tsaron da suke zato da farko sai suka fara latsa ta kuma suka ga jini. Yanzu sun mayar da birnin tamkar karkatacciyar kuka.
  • 'Yan bindigar da ke ratse dazuka da tsaunukan Abujar sun fahimci cewa akwai tarin manya masu kudi wato manyan jami'an gwamnati. Hakan ne ya sa suke sace mutane kuma su karbi kudin fansa.
  • Kasancewar da an yi garkuwa da mutane a kan samu yanayin da jama'a kan shela ta neman tallafi inda ake bude asusu na tara taimkon kudin a bainar jama'a domin biyan 'yan bindigar kudin fansar da suka sanya kafin su sake wadanda suka sace din.

Mece ce mafita?

Police

Asalin hoton, Getty Images

Matsalar hare-hare dai na nuna irin gazawa na tsarin tsaron Najeriya kuma masana na ganin mafita ita ce komawa tsarin domin inganta shi.

"Shi tsarin tsaro yana amfani da Dan adam, kimiyya da tsari", in ji Kabiru Adamu.

Malam Kabiru Adamu ya ce akwai wasu tsare-tsare guda biyar da ya kamata jami'an tsaron birnin tarayyar su dabbaka kamar haka:

1- Damar hana bata-gari aiwatar da mugun aiki da ake kira da Turanci 'Deter'.

2- Daukar matakan da za su janyo wa mai son aikata laifi jinkiri da ake kira 'delay.

3- Agaji da za a kai wa wanda abin ya shafa wanda ake kira 'response' da turanci.

4- Bibiyar masu laifi bayan aikata laifi wanda zai bayar da damar kai wa ga kama mai laifi abin da ake kira 'tracing or tracking'.

5 - Yin waiwaye ga tsarin domin gyara inda aka samu matsala.

Daga karshe Malam Kabiru Adamu da Group Captain Sadiq Garba mai ritaya sun amince cewa dole ne jami'an tsaron Abuja da na jihohi masu makwabta su yi aiki tare sannan a yi aiki da fasaha kamar sanya kamarori masu daukar hoton masu laifi.

"Kari a nan shi ne ya kamata kuma a sanya al'umma da sarakunansu cikin al'amarin," in ji Malam Kabiru.

Masanan dai na da kwarin gwiwar cewa idan har aka aiwatar da wadannan shawarwari batun matsalar 'yan bindiga a babban birnin tarayya za zama sai dai wata matsal kuma ba ita ba.

Hakan kuma zai bai wa mazauna birnin irin su Abubakar Isa dan asalin Kano mazaunin Abuja kyakkayan fata na ci gaba da zama a birnin cikin aminci.