'Yadda na kuɓuce wa ƴanbindigar da suka sace mu a Kaduna'

Asalin hoton, KADUNA STATE GOVERNMENT
Daya daga cikin daliban da 'yan bindiga suka sace a garin Kuriga na jihar Kaduna, ya bayyana yadda ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutanen.
A ranar Alhamis ne ƴanbindiga suka sace dalibai na makarantun firamare da sakandire su kimanin 270 a Kauyen Kuriga na Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya
Kawo yanzu ba a ji ɗuriyar inda 'yanbindigan ke garkuwa da kananan yaran ba wadanda galibinsu 'yan shekaru 5 ne zuwa 18. Sai dai akwai wasu daga cikin ɗaliban da suka samu tserewa.
Mustapha Abubakar ya shaidawa BBC cewa 'yanbindigar sun kora su kamar shanu, inda suka yi ta tafiya a cikin daji wani lokacin kuma da sassarfa.
''Mun fara fama da kishin ruwa, wasu daga cikin matan sun fara galabaita suna faduwa saboda gajiya, 'yanbindigar sun yi ta daukar wadanda suka fadi tare da dora su akan babura.''
Ya ce a haka suka isa wani babban rafi, suka samu shan ruwa kafin daga bisani su ci gaba da tafiya. Ya ce wani jirgin sama ya yi ta zagayawa inda suke, "a nan 'yanbindigar suka umarci duk wanda ya ke da riga guda biyu ya cire daya kuma su kwanta a kasa."
''Su kansu 'yan bindigar sun gaji, ba su da abin da za su ci sai tsinkar gaude da taura suke yi a dajin suna ci, ba su ba mu komai ba."
"Lokacin da muke tafiya na ga wani haki mai ruwan kasa irin na wandona sai na faɗa ciki tare da jan jiki kamar maciji. Na dauki awanni a ciki, sai da suka gama wucewa baki ɗaya yadda ko motsin komai ba na ji kafin na samu damar fitowa na yanki daji,'' in ji shi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce ya haɗu da wani tsoho da yake tafiya da kyar, domin ya nuna masa hanyar da za ta kai shi bakin titi ko wani garin domin ya samu ruwan sha.
Mustapha ya ce ya yi tafiya mai nisa cikin gudun fanfalaki, ga jiri na dibarsa amma haka ya daure, ga kuma yamma na kawo jiki har Allah ya kai shi wani gari da ake kira Gayan, daga nan ne ya kubuta.
Sauran iyaye da 'yan uwan wadanda aka sace na cikin tashin hankali da rashin madafa.
Sun yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da tarayya su kawo musu ɗauki domin kuɓutar da sauran daliban da ke hannun 'yan bindigar.
Da safiyar ranar Alhamis din makon da ya wuce ne 'yanbindiga suka kai hari kauyen Kuriga, a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna, tare da sace daliban firamare da na sakandare su kusan 287.
Wani malamin makarantar mai suna Sani Abdullahi wanda ya kubuta ya bayyana cewa an sace dalibai na bangaren sakandare 187, sai kuma bangaren firamare ɗalibai 125, amma daga bisani wasu 25 sun dawo.
Gwamnatin jihar Kaduna ta sha alwashin kubutar da daliban inda ta yi alkawarin za ta sake gini ofishin 'yansanda a garin wanda rahotanni ke cewa babu shi sam a kauyen.
Satar mutane domin neman kudin fansa dai na kara ta'azzara matsalar tsaro a sassan Najeriya musamman yankin arewacin kasar, inda makarantu suka zama wurin da 'yanbindigar ke kai wa hare-hare da sace su.











