Yadda karuwar matsalar tsaro ke barazana ga samar da abinci a Taraba

.

Al’ummar kabilar Kuteb dake jihar Taraba na kokawa kan hare-hare da suka ce wasu mutane da basu san ko su wanene ba na kaiwa a kauyukansu. Wadannan hare-haren na zuwa ne a yayin da Kutebawan ke kokarin girbe amfanin gonakinsu da suka noma bana. A tattaunawarsu da Salihu Adamu Usman, Mai magana da yawun kungiyar kabilar Ure Caleb Danjuma ya ce lamarin yafi kamari ne a kananan hukumomin Takum da Ussa da Donga da kuma sauransu.

Mista Danjuma ya kara da cewa duk abincin da ake ci a Kudancin Taraba, Kutebawa ne ke yi, "inda nake maka maganar nan, sun je suna ta kone abinci da gidaje da yawa."

Ya ce ba zai iya cewa ga wanda yake musu aika-aikar ba shi yasa ya ce suna kai kukansu ne ga gwamnati, "ta fitar da mutanen da ke wadan nan abubuwan." A cewarsa, babbar bukatarsu a yanzu ita ce ya tura wata tawaga da za ta je ta duba irin girman barnar da aka tafka a wajen.

Danjuma ya ce ayyukan da aka kone sun fi150, ba abinci kuma babu magani, mutane kuma suna mutawa. Ya kuma shaida cewa a shirye suke su ga komai ya daidaita.