Yadda wani yaro ya mutu bayan dan uwansa ya gwada maganin bindiga a kansa a Kwara

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar 'yan sandan Jihar Kwara da ke tsakiyar Najeriya ta soma farautar wani matashi da ake zargi da harbe dan uwansa yayin gwajin maganin bindiga da ya yi a kansa.
Lamari, wanda ya faru a garin Dutse Gogo da ke karamar hukumar Kaiama ranar Lahadi, ya tayar da hankalin al'ummar yankin.
A sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kwara, SP Okasanmi Ajayi, ya aike wa BBC ya ce tuni ta tura jami'anta domin kama duk wani da ke da hannu a kisan matashin.
SP Ajayi ya ce sun samu rahoto kisan da wani matashi mai suna Abubakar Abubakar ya yi wa kanensa Yusuf Abubakar, mai shekaru 12.
A cewarsa lamarin ya faru ne lokacin da Abubakar yake gwajin ingancin layar kariya daga harbin bindiga a kan kanensa.
Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewa mahaifin 'yan uwan biyu mai suna Abubakar, mafarauci ne.
Ya tsere cikin daji
Tuni rundunar 'yan sandan ta fara gudanar da bincike kan lamarin kamar yadda Kwamishinan 'yan sandan jihar Kwara, CP Paul Odama ya bayyana.
Rundunar ta ce harbin da Abubakar ya yi wa dan uwansa ya faru ne bayan ya sanya masa layar kariya daga harbin bindiga.
Daga nan ne ya dauki bindigar mahaifinsu ya harbi kaninsa da ita, kuma nan take ya fadi ya mutu.
SP Ajayi ya ce mutumin da ake zargi da aikata laifin ya tsere cikin daji bayan danyen aikin da ya aikata.
Rundunar 'yan sandan ta shawarci iyaye su sanya ido kan abubuwan da 'ya'yansu suke yi da makamai.











