Yadda ambaliyar ruwa ya zagaye garin Dabi a Ringim na jihar Jigawa
Yadda ambaliyar ruwa ya zagaye garin Dabi a Ringim na jihar Jigawa
Ambaliyar ruwa na ci gaba da ɓarna a sassa daban-daban a Najeriya, kamar dai yadda yake faruwa a wasu ƙsashen duniya.
Garin Dabi da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar RIngim a jihar Jigawa, arewa maso yammacin ƙasar, na daga cikin wadanda ambaliyar ta yi wa mummunar ɓarna.
Ruwa ya zagaye illahirin ƙauyen inda ta kowace kusurwa ba yadda za a yi a tsallake sai da kwal-kwale.
Sai dai kuma amfani da kwal-kwalen ma na tattare da hatsari, inda yakan kife da mutane da dama a wasu lokutan har ma a yi asarar rayuwa.



