Yadda ambaliyar ruwa ta yi ta'adi a Jigawa

Bayanan bidiyo, Yadda ambaliyar ruwa ta yi ta'adi a Jigawa

Al'ummomi da mama ne ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa dake arewa maso yammacin Nigeria, inda aka samu asarar rayuka da ta dukiyoyi.

Fiye da mutum 40 ne suka mutu a ambaliyar ruwan sannn dubban gidaje suka rushe, aka kuma yi asarar amfanin gona na miliyoyin Naira.

Hukumomi a jihar ta Jigawa sun ce fiye da mutum 10,000 ne suka samun mafaka a sansanoni 30 da aka samar musu.

Wannan ce mafi munin ambaliyar ruwa da aka fuskanta a jihar Jigawa cikin shekaru da dama.