Real Madrid ta doke Celta tana nan ta biyu a La Liga

Real Madrid ta doke Celta Vigo 2-0 a wasan mako na 30 a gasar La Liga da suka kara ranar Asabar a Santiago Bernabeu.

Saura minti uku su je hutun rabin lokaci, Marco Asensio ya ci kwallo, sannan Eder Militao ya kara na biyu a minti na uku da suka koma zagaye na biyu.

Da wannan sakamakon Real Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da maki 65, ita kuwa Celta tana nan da maki 36 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Barcelona ce kan gaba a matakin farko mai maki 73, wadda za ta karbi bakuncin Atletico Madrid ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

Resl Madrid da Celta sun fara wasa a bana a La Liga ranar 20 ga watan Agustan 2022, inda kungiyar Santigo Bernabeu ta je ta ci 4-1.

Real ta ci kwallayen ta hannun Karim Benzema a bugun fenariti da Luka Modric da Vinicius Junior da Federico Valverde.

Ita kuwa mai masaukin baki, Celta ta zare daya ta hannun Iago Aspas a minti na 23 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Sakamakon wasannin da aka buga ranar Asabar 22 ga watan Afirilu:

  • Osasuna 3 - 2 Real Betis
  • Almeria 1 - 2 Athletic Bilbao
  • Real Sociedad da Rayo Vallecano
  • Real Valladolid 2 - 1 Girona
  • Real Madrid 2 - 0 Celta Vigo

Karawar mako na 30 ranar Lahadi 23 ga watan Afirilu

  • Elche da Valencia
  • Barcelona da Atletico Madrid
  • Real Mallorca da Getafe
  • Sevilla da Villarreal

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye:

  • Robert Lewandowski FC Barcelona 17
  • Karim Benzema Real Madrid CF 14
  • Enes Unal Getafe CF 13
  • Joselu RCD Espanyol 12
  • Borja Iglesias Real Betis 12
  • Vedat Muriqi Real Mallorca 12
  • Iago Aspas Celta de Vigo 12
  • Antoine Griezmann Atletico de Madrid 11
  • Alvaro Morata Atletico de Madrid 10
  • Gabriel Veiga Celta de Vigo 9
  • Vinicius Junior Real Madrid CF 9
  • Alexander Sorloth Real Sociedad 9
  • Martin Braithwaite RCD Espanyol 9