Yadda amfani da waya ya shafi ƙwaƙwalwar ɗana

Lokacin da yara ke ɓatawa suna kallo tun suna ƙanana, matsala ce da ke da mummunan tasiri ga lafiyarsu, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana.
Jinkirin fara magana, ɗaya ne daga cikin tarin matsalolin da ke tattare da yawan amfani da wayar hannu a tsakanin yara ƴan ƙasa da shekara biyar.
Irin wannan matsala ce ta shafi Mohammed, mai shekara huɗu wanda mahaifiyarsa ta shaida wa BBC cewa har yanzu ba ya magana kamar sa'anninsa wadanda tun fiye da shekara biyu suka buɗe baki.
Hakan ya jefa mahaifiyar Mohammed cikin damuwa saboda yadda mutane ke yi wa ɗan nata kallon mai aljanu ko galhanga.
Ta ce idan mutane suna alaƙanta halin da ɗanta ke ciki da batun aljanu tana hana idonta barci, ta yi ta addu'a tare da saƙe-saƙe iri daban-daban.
Sai dai tana cikin wannan hali ne masana fannin zance suka ankarar da ita, kan cewa ita ce da kanta ta haddasa masa wannan matsala.
'Kallon da nasa shi yi ne ya shafi ƙwaƙwalwarsa'

Asalin hoton, Getty Images
Mahaifiyar Mohammed ta ce a lokacin "da na samu cikin ƙaninsa, sai na ɗan janye, saboda nima ina son lokacina kullum dai yadda ciki yake zuwa a gajiye, sai na zo duk abin da yake idan ya zo, ko zai dame ni sai na ce a bashi ipad ya kalla,"
"Ko kuma ya je ya yi kallon cartoon, babau rana babu dare kallo yake yi." in ji ta.
Ta ce a lokacin da Mohammed ya kai kusan shekara uku ne da kuma gwajin da aka yi masa ya taimaka musu wajen gano cewa "kallon da na sa shi yana yi, gaskiya shi ne ya shafi ƙwaƙwalwarsa."
'Kallon waya na nunawa yaro idan an masa magana, ba sai ya amsa ba'
Likitoci irin su Dakta Zainab Yaro wadda aka fi sani da Dr Mims a Abuja, babban birnin Najeriya ta bayyana abubuwan da suke kawo jinkirin magana a tsakanin yara da kuma irin tsarin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce abi.
A cewarta, "ba wai abubuwan nan ba su da kyau ba amma [lokacin da yara ke ɓatawa kan waya] yana nunawa yaro cewa magana hanya ɗaya ce - a yi min magana, ba sai na yi magana ba."
"Idan an min magana daga talabijin, ba sai na yi magana ba, sai yaro ya girma yana tunanin haka dama rayuwa take - ai ana min magana ma, ana ci gabawa, ba sai na amsa ba, ba sai na ce eh ba." in ji likitan.
Dakta Yaro ta ce kallon talabijin na nunawa ƙananan yara cewa ba sai sun amsa ba a duk lokacin da aka yi musu magana.
Likitan ta bayyana cewa a ƙasashen da suka ci gaba kamar Amurka, sun ba da dokar cewa yara kar su fara kallon talabijin ko riƙe waya sai sun yi wata 18.
Yadda za a taimaka wa yara masu jinkirin magana
Masana na kira ga iyaye ka da su yi ƙasa a gwiwa wajen ilmantar da yaran da suke fama da irin wannan matsala ta rashin iya magana kamar yadda Malama Tajira Badi Adam wata mai koyar da yara masu matsalar zance a jamhuriyar Nijar ta bayyana.
Yin hakan, a faɗarta, zai taimaka "a san me ke burge su, mai suke so, mene ne ba sa so, ya suke tafiya da rayuwarsu."
Ta ce akwai wasanni da suke tsarawa kuma mafi muhimmanci cikinsu waƙa ce da ke kawowa yara sauƙi wajen soma magana.
Masana fannin halayyar ɗan adam sun ce a duk yara biyar a kan samu ɗaya daga cikin su da ka iya fuskantar matsalar rashin iya magana da wuri saboda tsabar amfani da waya ko komputa.











