Abu 10 a kan riga-kafin kansar bakin mahaifa don kare 'yan matan Najeriya

Asalin hoton, Unicef Nigeria/X
Hukumomin lafiya a Najeriya na ci gaba da gangamin riga-kafin kansar bakin mahaifa na tsawon kwana biyar, don kuɓutar da mata dubu takwas da ke mutuwa duk shekara a ƙasar.
Kansar bakin mahaifa tana cikin manyan cutukan kansa guda uku - kamar kansar nono da kansar mafitsara - waɗanda suka fi hallaka 'yan Najeriya.
Babbar jami'ar asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (Unicef) a Najeriya, Dr Rownak Khan ta ce duk da lahanin cutar kansar bakin mahaifa, amma ana iya rage yawan masu kamuwa da ita a Najeriya da kaso kimanin 90, matukar an yi wa 'yan matan ƙasar riga-kafi.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce fatan mahukunta shi ne su iya kare 'yan matan Najeriya sama da miliyan 16 daga kamuwa da cutar kansar bakin mahaifa nan da shekara ta 2025.
Daga lokacin da aka ƙaddamar da riga-kafin ranar Talata a Abuja, za a kwashe tsawon kwana biyar, ana bin 'yan mata masu tasowa a cikin jiha 15 da kuma babban birnin ƙasar, ana yi musu wannan allura.
1. kansar bakin mahaifa
Wannan nau'in kansa yana tsirowa ne a bakin mahaifar mace (daidai ƙofar mahaifa daga al'aurar mace).
Kusan duk cutukan kansar mahaifa (kashi 99) suna da alaƙa da ƙwayoyin cuta da ake kira human papillomaviruses (HPV) masu matuƙar hatsari. Ƙwayoyin cutar bairas ne da suka zama ruwan dare waɗanda kuma ake ɗauka ta hanyar jima'i.
Ko da yake, mafi yawan ƙwayoyin cutar HPV da ake ɗauka, suna warkewa haka kawai ba tare da ma sun nuna waɗansu alamomi ba. Sai dai, idan mace ta ci gaba da ɗaukar ƙwayoyin cutar, suna iya haddasa mata kansar bakin mahaifa.
Kansar bakin mahaifa, ita ce cutar kansa ta huɗu mafi yawa da ke addabar mata.
A shekara ta 2018, an yi ƙiyasi mata 570,000 ne aka gano suna da cutar a duniya, kuma kimanin 311,000 ne suka mutu sanadin kansar bakin mahaifa a shekarar.
2. Illolin kansar bakin mahaifa
Muguwar cuta ce da ke haddasa mace-mace.
Mata 8,000 ne ke mutuwa duk shekara, sanadin cutar a Najeriya, in ji ministan lafiya na ƙasar Farfesa Muhammad Ali Pate.
Kuma irin wannan asara daga cutar da akasari za a iya kare kai daga kamuwa da ita, in ji Pate, abu ne da kwata-kwata ba za a amince da shi ba.
Matan da ke mutuwa, na cikin adadin mata 12,000 da ke kamuwa da kansar bakin mahaifa duk shekara a ƙasar.
Manajan Daraktan Cibiyar Gavi mai samar da alluran riga-kafi a duniya reshen Najeriya, Thabani Maphosa ya ce a kullum cutar kansar bakin mahaifa, tana haddasa dumbin asara da tagayyara iyalai a faɗin Najeriya.
Kuma ta fi ƙwazzabar mata, duk da yake ana iya riga-kafinta.
Farfesa Muhammad Ali Pate ya ce iyaye na iya kaucewa shiga halin matsin kuɗi da na lafiyar jiki, ta hanyar kare 'ya'yansu da allura guda ɗaya tak ta wannan riga-kafi.
3. Rika-kafin HPV

Asalin hoton, Muhammad Ali Pate/X
A yanzu haka akwai nau'i shida na allurar riga-kafin HPV da aka bai wa lasisi a duniya, cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.
Dukkansu kuma suna da matuƙar tasiri, wajen hana ɗaukar ƙwayoyin cutar bairas nau'i na 16 da na 18, waɗanda idan aka haɗa su wuri ɗaya, su ne ke haddasa kashi 70 cikin 100 na kansar bakin mahaifa a duniya.
Alluran riga-kafin kuma suna da tasirin hana ɗaɗewar sashen jiki da ake samu kafin bayyanar kansar bakin mahaifar.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce bayanai daga gwaje-gwajen riga-kafin da kuma bibiyar waɗanda aka yi wa riga-kafi a nahiyoyi da dama, sun nuna cewa riga-kafin HPV tana da aminci.
4. Jihohin da za a yi riga-kafin zagayen farko
Ana yin riga-kafin ne daga ranar Talata 24 ga watan Oktoba zuwa Asabar 28 ga wata.
Ga jerin jihohin da ake riga-kafin:
- Abia
- Adamawa
- Akwa Ibom
- Enugu
- Lagos
- Osun
- Bauchi
- Bayelsa
- Binuwe
- Jigawa
- Nasarawa
- Kano
- Kebbi
- Ogun
- Taraba
- Abuja
Za kuma a ƙaddamar da zagaye na biyu na riga-kafin a watan Mayun 2024 cikin jihohin Najeriya 21.
5. Manufar ɓullo da riga-kafin
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Allurar riga-kafin cutar kansar bakin mahaifa miliyan 15 da Unicef ya kai Najeriya, wani ƙoƙari ne daga asusun ke yi don samar da riga-kafin ceton rayuka a ƙasashe guda huɗu na duniya.
Ƙasashen Najeriya da Bangladesh da Cambodia da Eswatini da Kiribati da Mongoliya da kuma Togo duk sun ɗaura aniyar shigar da allurar cikin shirin riga-kafinsu na ƙasa a wannan shekara.
Unicef ya ce a 2020, matan da suka kamu da cutar kansar bakin mahaifa sun zarce 600,000, yayin da 340,000 suka riga mu gidan gaskiya, sanadin cutar.
A cewar Unicef, kashi 90 na waɗanda suka kamu da cutar da ma waɗanda suka mutu dalilin kansar bakin mahaifa, suna cikin ƙasashe masu ƙaranci da matsakaicin samun kuɗin shiga, inda samun riga-kafi da ayyukan gwaje-gwajen lafiya da maganin cutar suka taƙaita.
Hukumomin lafiya na duniya na yunƙurin kai allurar riga-kafin cikin ƙasashen da ake samun kusan kashi 60 na matan da ke kamuwa da cutar, saboda ba a yi musu riga-kafi ba.
Unicef ya ce ya kai riga-kafin cikin ƙarin ƙasashen duniya 20 da ke da yawan masu fama da cutar a tsawon shekara biyu zuwa uku.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta yaba wa Najeriya saboda ƙaddamar da riga-kafin.
Jami'in hukumar, Alex Chimbara yayin ƙaddamar da allurar a ranar Talata ya ce wannan wani zuba jari ne mai matuƙar amfani da zai taimaka wajen kare 'yan mata a nan gaba bisa manufofin tsarin Najeriya na samar da riga-kafi da taƙaita bazuwar kansar bakin mahaifa.
6. Su wa za a yi wa riga-kafin HPV?
Najeriya dai tana fatan yi wa 'yan mata miliyan bakwai da dubu ɗari bakwai riga-kafin human papillomavirus (HPV).
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce adadin shi ne mafi yawa na 'yan matan da za a yi wa riga-kafin guda ɗaya a faɗin nahiyar Afirka.
Za a gudanar da gangamin allurar tsawon kwana biyar don yi wa ɗumbin 'yan mata riga-kafin a makarantu da unguwanni a zagayen farko.
Daga bisani kuma za a shigar da allurar cikin shirin alluran riga-kafi na ƙasa da aka saba yi musamman a cibiyoyin lafiya na Najeriya.
Idan suka samu ƙarin kuɗi kuma, Gavi da sauran abokan ƙawancensa suna da wani gagarumin buri na tabbatar da yi wa 'yan mata sama da miliyan 86 riga-kafi, don kare su daga mace-macen da ka iya ritsawa da mata kusan miliyan ɗaya da rabi sanadin kansar bakin mahaifa.
7. 'Yan shekara nawa za a yi wa riga-kafin?
Rukunin farko na gangamin riga-kafin zai fi mayar da hankali ne wajen yi wa 'yan mata masu tasowa 'yan shekara 9 zuwa shekara 14.
'Yan mata miliyan 16 ake sa ran yi wa riga-kafin a cikin shekara biyu.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ga duk wani riga-kafi, adadin yawan da za a yi wa mutum, ya danganta ga shekarunsa.
Hukumomi a Najeriya sun ce za a yi wa kowacce yarinya riga-kafi ƙwaya ɗaya, kuma riga-kafin yana da matuƙar inganci wajen hana ɗaukar ƙwayoyin cuta na bairas nau'i mai lamba 16 da kuma mai lamba 18.
Su ne suke haddasa aƙalla kashi 70 cikin 100 na cutukan kansar bakin mahaifa.

Asalin hoton, Daular Usmaniyya
8. Za mu ba da goyon baya - Sarkin Musulmi
Cikin ɗumbin jami'an da suka halarci ƙaddamar da riga-kafin a ranar Talata, har da Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, wanda shi ma ya sanya albarka kan wannan yunƙuri.
An ambato babbar basaraken yana cewa "Da tallafin gwamnati a dukkan matakai, za mu ga yadda za mu iya aiki tare don kai wannan riga-kafi lungu da saƙo na ƙasar nan.
"Ta yadda 'ya'yanmu za su kasance cikin aminci idan Allah ya raya su, suka girma.”
Haka zalika, ita ma shugabar Gidauniyar Medicaid Cancer Foundation, Hajiya Zainab Bagudu ta ce su ma a nasu ɓangare za su ci gaba da aiki don tabbatar da kai saƙon da ya dace ga jama'ar ƙasar ta yadda Najeriya za ta cimma burin kakkaɓe cutar kansar bakin mahaifa nan gaba kaɗan.
Ta ce abin tayar da hankali ne ganin ɗumbin mata da 'yan mata ba sa iya samun gwajin gano cutar da riga-kafi da kuma maganin kawar da kansar bakin mahaifa.
Ministan lafiya na Najeriya ya ce a matsayinsa na mahaifi shi ma, ya tabbatar da ganin an yi wa dukkan ‘ya’yansa mata guda huɗu riga-kafin don kare su daga cutar kansar bakin mahaifa.
Kuma ya yi kira ga takwarorinsa iyaye, su tabbatar a matsayin nauyin da ya rataya a wuyansu cewa wannan zuri’a ta ‘ya’ya mata ta katse asarar rayukan da ake samu sanadin cutar kansar bakin mahaifa da za a iya karewa, baya ga tsananin matsi da asara da kuma ciwon da takan haifar.
9. Riga-kafin kyauta ne
Ma'aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya ta samar da allurar riga-kafin HVP kyauta ta hanyar hukumar bunƙasa ayyukan kula da lafiya a matakin farko ta ƙasar.
Najeriya ta samu tallafin Gavi da shirin ƙawancen samar da alluran riga-kafi wato Vaccine Alliance da asusun kula da yara na duniya Unicef da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya da sauran abokan ƙawance.
Sanarwar hukumar lafiya ta duniya ta ce an horas da ma'aikatan lafiya sama da 35,000 zuwa yanzu don gangamin riga-kafin na tsawon kwana biyar da kuma sauran shirye-shiryen yin allurar na gaba a duk cibiyoyin lafiya na Najeriya.
Ta ce an ware cibiyoyin riga-kafi a dukkan mazaɓu guda 4,163 na jihohin ƙasar 15 da kuma babban birnin tarayya, a ƙoƙarin ganin duk yarinyar da ta cancanci samun riga-kafin, ba a bar ta a baya ba.
Haka zalika, an tanadi tasoshin riga-kafi na tafi da gidanka don ganin sun shiga garuruwa da ƙauyuka masu nisa, ta yadda su ma al'ummomin irin waɗannan wurare za su samu allurar.
10. Riga-kafin na da aminci
Ministan lafiya na Najeriya, Farfesa Muhammad Ali Pate ya ce riga-kafin tana da aminci da kuma inganci, don kuwa an yi wa mata a ƙasashe da dama cikin faɗin duniya, kafin ma a kawo ta Najeriya.
Ya ce duk da yake, riga-kafi ce da ake yi bisa raɗin kai, amma ya yi imani babu mahaifin da zai jefa rayuwar 'ya yi hatsari irin na cutar kansar bakin mahaifa, wadda ana iya tsare kai daga kamuwa da ita.
Mata fiye da miliyan 56 ne suke cikin hatsarin ɗaukar ƙwayar cutar bairas ta humanpapiloma a Najeriya.
Cutar kansar bakin mahaifar wadda ƙwayar cutar HPV ke haddasawa ita ce cutar kansa ta uku mafi yawa a ƙasar kuma ta biyu mafi hallaka mata a Najeriya.
Matan da ke tsakanin shekara 15 zuwa 44 su ne suka fi zama cikin hatsari.











