Bayanan da suka kamata ku sani game da cutar kansar mahaifa

Bayanan bidiyo, Bayanan da ya kamata ku sani game da kansar mahaifa

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Janairu ne watan wayar da kai a kan yadda za a kauce wa kamuwa da cutar kansar mahaifa domin fadakar da matan da ke da muhimmanci a rayuwarmu.

A duk minti biyu a fadin duniya, mace daya na mutuwa ta dalilin cutar kansar mahaifa.

A nan Najeriya, mata 30 ne ciki har da 'ya'yanmu da 'yan uwanmu da matanmu da ma uwayenmu ake rasawa ta dalilin wannan cuta mai kisa.

Kansar mahaifa na kama kasan mahaifa kuma tana jefa mata fiye da miliyan 50 a Najeriya cikin hadari, daga lokacin da suka balaga har su kai shekara 65.

Takan dauki kusan shekara 30 kafin ta gama bunkasa.

Hakan ne ya sa cutar ta zama ta daya a cikin nau'ukan cutar kansa masu kashe mata 'yan shekara 15 zuwa 44 a Najeriya.

Amma ana iya hana kamuwa da cutar dari bisa dari idan har aka gano wanzuwar kwayar cutar da ke haddasa ta da wuri.

Ta hanyar yin gwajin da ake kira PAP SMEAR akai-akai da kuma riga-kafin HPV.

Bayanai: Kungiyar Chain Reaction Nigeria

Bidiyo: Abdulbaki Jari

Shiryawa da tsarawa: Halima Umar Saleh da Muhammad Kabir Muhammad