Lafiya Zinariya: Lokacin da ya dace mace ta ga likita idan ta kai shekarun daukewar al'ada

Bayanan sautiLafiya Zinariya kan shekarun daukewar jinin al'adar mata kashi na uku

Latsa hoton da ke sama don sauraron cikakken shirin wanda Habiba Adamu ta gabatar ta kuma tattauna da Dr. Yelwa Usman:

Yana da muhimmancin gaske ma'aurata su fahimci irin sauye-sauyen da mace ke fuskanta kafin daukewar jinin al'ada, domin hakan kan shafi yanayin saduwa.

Likitoci sun bayyana cewa wannan lamari na daga cikin alamomin da wasu matan ke fuskanta gabannin su manyanta.

Sai dai masana a fannin kiwon lafiya na bai wa mata shawarar cewa idan alamomin da suke gani sun tsananta, to su je asibiti su yi cikakken bayani domin a duba hanyar taimaka musu.

Jinin ala'ada kan dauke wa wasu matan masu karancin shekaru, yayin da kuma wasu su kan kai har shekara 55 a duniya kafin su daina jinin na wata-wata.

Ga shirye-shiryen baya da za ku so ku saurara: