Ana iya kauce wa haihuwar jariri bakwaini?

...

Asalin hoton, CORBIS ROYALTY FREE

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
    • Aiko rahoto daga, Abuja

Ƙwararrun likitoci masu kula da lafiyar yara sun jaddada muhimmancin aiwatar da matakan kauce wa haihuwar jarirai bakwaini, ga mata masu juna biyu.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi ƙiyasi a shekara ta 2020 cewa jarirai kimanin miliyan 13.4 ne aka haifa a matsayin bakwaini, kusan sama da yaro ɗaya cikin 10 kenan.

Hukumar ta kuma ce a shekarar 2019, jarirai kimanin 900,000 ne suka mutu sanadin lalurori masu alaƙa bakwaini.

Haka kuma, jariran da suka rayu, kan fuskanci lalurori tsawon rayuwarsu, ciki har da ƙarancin fahimtar karatu da lalurar ji ko ta gani, in ji Hukumar. Lafiya ta Duniya

Girman wannan matsala ta yawan mutuwar jarirai ne, ya sanya cibiyar da ake kira Gidauniyar kula da Jarirai Sabbin Haihuwa a Turai ta keɓe 7 ga watan Nuwamban kowacce shekara a matsayin ranar wayar da kai game da haihuwar bakwaini da kuma illolin da za ta iya haifarwa ga iyalai.

Taken ranar ta bana shi ne: "ƙanƙanin mataki mai babban tasiri, inganta al'adar jin ɗumin jikin iyaye ga jarirai a ko yaushe".

Dakta Mariya Mukhtar Yola, wata ƙwararriyar likitar jarirai a babban asibiti na ƙasa da ke Abuja, kuma shugabar likitocin jarirai ta Najeriya, ta ce matakan da mai juna biyu za ta ɗauka don kauce wa haihuwar bakwaini suna da yawa kuma sun haɗa da kula da lafiyar jikinta daga farkon shigar ciki har zuwa haihuwa.

Likitar ta ce kamata ya yi mai juna biyu ta dinga cin abinci mai inganci sannan ta dinga samun lokaci tana hutawa.

Ta kuma shawarci mai juna biyu ta guji yin aikin ƙarfi, mai wahalarwa ko da kuwa zirga-zirga ce ta yau da kullum, kamata ya yi ta rage.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr Mariya Yola ta ƙara da yin kira ga masu juna biyu su tabbatar da zuwa awo saboda duba lafiyarsu da na jariransu.

Ta kuma ja hankalin mai juna biyu da cewa idan akwai wata matsala, ta gaggauta tuntuɓar likita saboda kauce wa ƙalubale da dama kamar na wata baiwar Allah da ba ta so a ambaci sunanta, da ta haifi 'yan biyu kuma duk bakwaini.

"Abin da ya fi tayar min da hankali shi ne, ina ji, ina gani ba zan iya shayar da abin da na haifa ba, saboda yana cikin kwalba tsawon wasu kwanaki."

Ta ce ba ta samu labarin bakwaini za ta haifa ba, inda ta kamu da ciwo mai tsanani da har ya kai ga ciro jariran.

"Kawai cikina yana wata shida da kwanaki, na fara wani ciwo mai tsanani, shi ne muka je asibiti."

"Da muka je asibitin, ana tunanin ma zan iya mutuwa a lokacin, ba zan rayu ba, cikina ya girma da yawa, shi ne kawai likita ya ba da shawarar a cire jariran," in ji ta.

Ta ci gaba da cewa: "Gaskiya na fuskanci ƙalubale, saboda yaran sun zo kowanne bai kai nauyin kilogiram ɗaya ba, ƙanana da su, kuma aka hana ni ko taɓa su, ina ji ina gani".

"Likitocin sun ce ba za su ci abinci ba, sai sun yi kwanaki, kuma sai da suka yi kwana tara, kafin fara ba su abinci"

"Sai da na koma ina tausaya musu, da ma sauran yara da ake kai wa ɗakin kula da jarirai bakwaini."

Ta ce bayan wata biyu ne, aka fitar da jariran nata daga kwalba, kuma ko da yake sun fi takwarorinsu ƙanƙanta, amma sun fi su ƙoshi da lafiya.

Me ke haddasa haihuwar jarirai bakwaini?

Dakta Mariya Yola ta ce akwai dalilai da yawa da suke haddasa haihuwar jarirai bakwaini.

"Dalilan na farko dai zai iya kasancewa mahaifiyar ce ba ta da lafiya kuma cutuka daban-daban za su iya shafar ta da za su iya sanya ta haifi jariri bakwaini, misali hawan jini, ciwon suga ko kuma zazzaɓi mai zafi kamar su ciwon cizon soro, typhiod ko ciwon mafitsari"

"Kuma zai iya yiwuwa cewa yawan aikin wahala da ɗaukar abubuwa masu nauyi ga mai ciki, za su iya jawowa ta haihu kafin lokaci."

"Wasu mata kuma halittasu ce, bakin mahaifarsu yakan buɗe kafin lokacin da ya kamata ya buɗe, toh, idan haka ta faru, sai kiga yaran sun fito bakwani ko kofin wata bakwai din."

Likitar ta ƙara da cewa zai iya kasancewa matsalar ba daga wurin uwar bane, daga wurin jaririn ne wanda Allah a cikin hukunci shi wani lokaci idan halitta bata cika ba ta jariri wato wani abun shi ba ya aiki daidai, zai iya fitowa kafin lokacin haihuwan shi.

Waɗanne matsaloli bakwaini ke fuskanta bayan haihuwa?

...

Asalin hoton, HANNAH COOK

Dakta Mariya ta ce akwai matsaloli da dama da jarirai bakwaini ke gamuwa da su, bayan haihuwa, ciki har da ma girmansu, ko da yake ba duka ba.

Ta ce ya danganta da watannin da aka haife su, ko wata biyar ne, ko shida, ko bakwai ko ma takwas, amma waɗanda suka fito da wuri ne suka fi samun matsala.

"Babbar matsalar da bakwaini ke fuskanta ita ce ta numfashi saboda halittar huhunsu ba ta gama cika ba."

"Suna da kuma jin sanyi saboda ba su da kitse da ƙibar da za su kare su."

"Na uku ba wuya sun kamu da cuta saboda rashin ƙarfin garkuwar jikinsu, sannan suna samun matsalar karɓar abinci ko ruwan nono saboda halittarsu, ta tsotsar nono da haɗiyewa ba ta kammala ba."

"Kuma sukan kamu da cutar shawara, ka ga idonsu ya canza ya koma ruwan ɗorawa, jikinsu ma ya canza kala, da kuma saurin zuƙewar jini, saboda yawan rashin lafiya da makamantansu.

Saboda haka duk sai an kula da waɗannan, an kiyaye da wuri-wuri."

"Wani lokacin idan bakwaini suka girma, za a ga abubuwansu ba sa tafiya kamar na sauran yara, saboda matsaloli na ido, ko kunne ko huhu."

Yaya likitoci da iyaye ke kula da bakwaini?

Ƙwararriyar likitar jariran ta ce likitoci da iyaye suna haɗa kai domin bai wa jarirai bakwaini kulawar da suke buƙata a lokacin kwanciyarsu a asibiti, da kuma bayan an sallame su.

Ta ce ana koyar da iyaye yadda za su ɗauki jariransu a jikinsu domin jiyar da su ɗumin jikin iyaye da kuma muhimmancin hakan.

Ta ce muhimmancin rungume jariri a jikin uwa ko uba shi ne bugawar zuciyar iyayen tana taimakawa jaririn ya ci gaba da numfashi, kuma yakan sanya da zarar sun ji yunwa, suna kusa da mahaifiyarsu, za ta shayar da su nan da nan.

"Sauran abubuwa da ake koya wa iyaye sun haɗar da fa'idar wanke hannu, kafin a taɓa jariri saboda gudun shafa musu ƙwayoyin cuta."

"Ana kuma nuna musu fa'idar komawa asibiti saboda su zo a sake duba lafiyarsu, da kuma ta iyayensu, da kuma amfanin karɓar riga-kafi da dai sauransu."

Dakta Mariya ta ce iyayen da suka taɓa haifar bakwaini waɗanda sun riga sun koyi hanyoyin kula da su, za su iya taimakawa iyaye sabbin shiga cikin sha'anin.