Shugabar ƙasar Tanzania ta nemi mata su rage haihuwa

Samia

Asalin hoton, AFP

Shugabar ƙasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta bayyana damuwa kan yawan haihuwar da ake yi a ƙasar tare da neman ƴan ƙasa da suk ɗauki matakan rage haihuwa.

Wannan wani gagarumin sauyi ne daga matsayar wanda ta gada, marigayi John Magufuli, wanda ƙarara ya nuna goyon bayan kar mata su yi tsarin iyali.

Shugaba Samia ta yi wannan magana ce kan haihuwa gaba gaɗi a ƙasar a ƙarshen makon da ya wuce, a lokacin da ta kai ziyara yankin Geita da ke yammacin ƙasar.

"A jiya a mazaɓarn Buselesele da ke yankin Geita an gaya min ce akwai wata cibiyar lafiya da ake haifar yara 1,000 duk wata.

"To yanzu ajujuwa nawa za a buƙata bayan shekara uku? Cibiyoyin lafiya nawa za a buƙata don duba lafiyar yaran nan?

"Tan ɗin abinci nawa za a buƙata? Ya kamata mu rage yawan haihuwar nan," in ji shugabar ƙasar.

A shekarar 2018 a yayin da ya halarci wani gangami a yammacin Tanzania, tsohon shugaban ƙsarMagafuli ya bayyana masu tsarin iyalki a matsayin ragwanci.

Sannan a 2016, bayan ƙaddamar da ilimin firamare da sakandare kyauta a ƙasar, ya ce: "Mata su yi watsi da duk wani tsarin iyali. Ilimi kyauta ne yanzu."

A shekarar 2020, Bankin Duniya ya ƙiyasta cewa duk mace ɗaya kan haifi kusan yara biyar a ƙsar.

An alaƙanta yawan haihuwar da auren wuri da kuma rashin ɗaukar matakan tsarin iyali.

A yayin da hakan ke raguwa a cikin shekara 30 da suka wuce, bai ragu sosai kamar sauran ƙsashen gabashin Afirka irin su Kenya da Habasha ba, kamar yadda alƙaluman Bankin Duniyar ya bayyana.

Yawan al'ummar Tanzaniya ya kai kusan miliyan 60, kashi 49 cikin 100 na yawan na rayuwa kan ƙasa da dala 1,77 a kullum.