Ko rikici tsakanin gwamnoni da Wike zai bar PDP ta yi kataɓus?

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Sake ɗage taron Majalisar Zartarwar jam’iyyar PDP ya sake buɗe wani giɓin da ake ƙoƙarin rufewa game da saɓani a tsakanin ɓangarorin jam’iyyar.

Asali an shirya gudanar da taron ne a watan Agusta, amma aka ɗage zuwa ranar 24 ga Oktoban bana.

A taron ne ake tunanin za a zaɓi shugaban jam’iyyar domin maye gurbin shugaban riƙo, Ambasada Umar Damagun.

Wannan dai shi ne kusan karo na uku da ake ɗage taron na Majalisar Zartarwar jam'iyyar mai adawa wanda a farko aka shirya gudanarwa a 15 ga Agusta, aka mayar 26 ga Satumba, yanzu kuma aka mayar Oktoba domin gudanar da taron na NEC karo na 99.

Yadda rikicin ya samo asali

A siyasa, ba a rasa jam’iyyu da rigimar cikin gida, musamman ma dai jam’iyya mai mulki da babbar jam’iyyar adawa.

Rikicin PDP ya faro ne daga zaɓen fid-da-gwani na takarar shugabancin ƙasar na 2023. Aminu Waziri Tambuwal ya janye wa Atiku a filin zaɓen, wanda shi kuma Wiken ya bayyana da rashin kyautawa.

Bayan zaɓen ne da Wike da wasu gwamnoni na wancan lokacin guda huɗu suka ware, suka ce ba za su yi Atiku ba har sai an cika musu wasu sharuɗɗai, ciki har da neman shugaban PDP na wancan lokacin Iyorchia Ayu ya sauka.

Gwamnonin su ne Nyesome Wike na Rivers da Seyi Makinde na Oyo da Samuel Ortom na Benue da Okezie Ikpeazu na Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Bayan babban zaɓen, wanda Bola Tinubu na APC ya doke Atiku Abubakar na PDP, inda aka yi zargin Wike ya yi wa APC aiki ne, Tinubu ya naɗa shi Ministan Abuja.

Tun lokacin ne aka buɗe wata sabuwar ƙofar rikicin tsakanin Wike da mutanen Atiku.

Mutanen Atiku suna cewa Damagun ya sauka daga shugabancin jam’iyar, su kuma mutanen Wike suna so ya ci gaba.

A game da asalin rikicin PDP, Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin harkokin siyasa a Najeriya ya bayyana wa BBC cewa rikicin yana da alaƙa da rashin aƙida.

“Ka ga ba a gina jam’iyyar a kan wata aƙida ba, mutane masu ra’ayi daban-daban ne suka haɗu. Abin da ya sa ba a ga wannan rikicin sosai shi ne lokacin da suke da mulki na shekara 16.

Rikici ya koma tsakanin gwamnoni da Wike

Bayan dogon lokaci ana tata-ɓurza tsakanin ɓangarori biyu, sai gwanonin PDP suka nuna goyon bayansu ga Gwamnan River Siminalaye Fubara.

Fubara dai na hannun daman Wike ne, amma bayan ya ɗare karagar mulki, sai rikici ya ɓarke a tsakaninsu, inda su kuma gwamnonin na PDP suka zaɓi goyon bayan Gwamna Fubara, wanda hakan ya haifar da wata rigimar tsakanin Wike da gwamnonin na PDP.

Ya zuwa yanzu za a iya cewa rikicin ya raba jam'iyyar zuwa ɓangarori uku: ɓangaren Atiku, da gwamnoni, da kuma Wike.

A zaɓen shugabannin PDP na Rivers da aka yi, ɓangaren Wike ya samu nasara, bayan majalisar zartarwa ta jam’iyyar ƙarƙashin Umar Damagun ta tabbatar da nasarar ɓangaren na Wike, wanda gwamnonin PDP suka ce ba daidai ba ne, tare da nanata cewa lallai Fubara ne jagoran PDP a Rivers.

Saboda wannan ne Ministan Abuja Nyesom Wike ya sha alwashin rura wutar rikicin siyasa a jihar duk wani gwamna da ya goyi bayan ɓangaren Fubara a Rivers.

Wike ya ce, “Ina tabbatar muku cewa matuƙar muna raye, babu wanda ya isa ya ƙwace PDP daga wajenmu a Rivers. Na ji wasu gwamnoni na so su shiga rikicin domin ƙwace shugabancin su miƙa ga wani. Ina tausaya musu domin zan kunna musu wuta a jihohinsu.

“Ko daga Bauchi kake ko daga wace jiha kake, idan ka shiga rikicinmu, to ba za ka yi barci a jiharka ba.”

Sai dai Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya mayar da martani ga Wike, inda ya ce, “babu wanda ya isa ya kunna wuta a Bauchi. Muna da isasshen ruwan kashe wutar.”

Gwamnonin dai sun dage a soke zaɓen shugabannin PDP na Rivers tare da mayar da jagorancin jam’iyyar ga gwamna Fubara.

Ko rikicin Wike da gwamnoni zai cinye PDP?

Yadda rikicin ke faɗaɗa ne ya sa ake muhawarar ko yaushe jam’iyyar za ta ɗinke ɓarakarta, ta fara shirin fafata wa da APC mai mulki har wasu suke fargabar rikicin zai iya lakume jam’iyyar.

Farfesa Fagge ya ce lallai rikicin zai iya cinye jam’iyyar baki ɗayanta idan ba a yi abun da ya dace ba.

“Ko dai bai cinye PDP ba, zai mata raunin da ba za ta yi wani tasirin da ake zato a siyasa ba saboda idan aka tafi a haka, za ta riƙa yaƙi biyu ne. Tana yaƙi a cikin gida tana yi a waje.

To wannan zai sa ta kasa samun tasirin da ake zato, sannan akwai alamu idan ba a shawo kan rikicin ba, zai iya jawo rushewar jam’iyyar baki ɗaya, amma a nan kusa dai rikicin zai mata tarnaƙi ya hana ta kataɓus.” In ji Farfesa Kamilu Fagge.

Ya ce kasancewar Wike a jam’iyyar kuma yana riƙe da muƙamin minista a gwamnatin APC zai yi tasiri a jam’iyyar, saboda a cewarsa ana fifita buƙatar kai sama da aƙida.

“Amma idan ana so a samu maslaha, kowa ya sauko, su gane cewa rarrabuwar ba za ta yi wa ƙasar da jam’iyyar amfani ba, a zauna a teburin siyasa a tattauna a warware matsalar. Kowa ya sauko daga buƙatar kansa, a haɗu tsakiya ko a dauko wani daban.”

Bayanai na nuna cewa jam'iyya mai mulki ba ta rasa hannu a irin wannan turka-turkar da ke dakushe ƙimar jam'iyyar adawa.

Da aka tambayi Farfesa Fagge ko APC na da hannu a rikicin, sai ya ce ba za ta rasa hannu ba, amma ya ce ba yau aka fara ba.

“A zamanin Obasanjo an yi hakan inda ita PDP ta ɗauko ƴan jam'iyyar adawa ta APP na wancan lokacin aka ba su muƙamai daga ƙarshe bayan sun yaƙi jam’iyyarsu suka narke a PDP. Don haka wannan ba sabon salo ba ne a assasa rigima a jam’iyyun hamayya. To ba ta ƙirƙira ba, za ta rura," kamar yadda Fagge ya yi ƙarin haske.

A ƙarshe Farfesa Fage ya ce matuƙar PDP ta shiga taron Majalisar Zartarwa a yadda take a yanzu, za a iya samun matsala.