Asalin Maukibin Ƙadiriyya da abin da ya sa ake yin sa

Asalin hoton, Ali Rabiu Sufi
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
A ranar Asabar, 4 ga watan Oktoba na wannan shekarar ta 2025 ne aka gudanar da taron bikin maukibi na ɗarikar Ƙadiriyya a jihar Kano da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Mabiya ɗarikar sun ce suna gudanar da bikin ne a duk ranar Asabar ta farko a watan Rabi al-Thani ta kowace shekara, amma idan Asabar ɗin farko ba ta kai ranar 10 ga watan ba, sai a gudanar da bikin a ranar Asabar ta biyu.
Dubban ƴan ɗarikar Ƙadiriyya daga Najeriya da ma wasu ƙasashen waje ne ke halartar taron bikin, inda ake zagaye a cikin birnin Kano tare da waƙe da yabon Annabi da kuma zama domin karance-karance littafan addini, musamman na tarihin Annabi da Sheikh Abduqadir Jelani da wasu magabata.
A lokacin zagaye, jerin-gwanon mabiya ɗarikar kan taso daga gidan shugaban ɗarikar wato gidan Ƙadiriyya da ke unguwar Kabara zuwa filin masallacin Juma'a na Jami'u Kanzil Mudalsam da ke kan hanyar Katsina duka a birnin na Kano, inda ake gabatar da jawabai da kuma addu'o'i.
Taron na bana, ya samu halartar manyan baƙi irin su ministan tsaron Najeriya da wakilan wasu gwamnoni da sarakuna, kamar yadda Sheikh AbdulGaffar Sheikh Nasiru Kabara ya bayyana a zantawarsa da BBC.
Yaushe aka fara Maukibi?

Asalin hoton, Ali Rabiu Sufi
A game da asalin fara bikin maukibi a Kano, BBC ta zanta da ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayi Sheikh Nasiru Kabara, wanda ya assasa bikin a gomman shekaru da suka gabata.
Sheikh AbdukGaffar Sheikh Nasiru Kabara ya ce an fara maukibin ne shekara 1950 wato shekaru 75 da suka gabata a Kano, kuma kalmar na nufin zagaye, wanda hakan ya sa ake kiran taron da Maukibin Ƙadiriyya.
”Maukibin Ƙadariyya ya samo asali ne daga maulana Amirul Jaishi, Sheikh Muhammadu Nasiru Kabara, kuma ya assasa bikin ne kimanin shekara 75 suka gabata," in ji shi.
Ya ce a lokacin da Marigayi Nasiru Kabara zai assasa bikin, "ya yi duba ne da wasu al'adu da ya ga ana yi a wannan yankin na ƙasar Hausa a wancan lokacin waɗanda ya lura suna da alaƙa da ɓurɓushin zamanin maguzanci kamar irin su yawon tashe da ake yin zagaye ana waƙe-waƙe irin na 'kan kare da daɗi, macukule' da sauran al'adu da suka fara zama ruwan dare a tsakanin al'umma."
AbdulGaffar ya ce wannan ne ya sa marigayi Malam Nasiru Kabara ya assasa bikin na maukibi, "domin maimakon a riƙa fita ana waƙe-waƙe na maguzanci, zai fi kyau a musuluntar da zagayen, sai a mayar da shi kamar kewaye na maulidi da sunan maulidi na Shehu AbdulQadir wanda za a fita ana waƙe-waƙe na yabon Allah da Manzon Allah da wasu bayin Allah da suka yi wa addini hidima."
Jagorancin maukibi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sheikh AbduGaffar ya ce Marigayi Sheikh Muhammadu Nasiru Kabara ne jagoran bikin a lokacin da ya assasa.
Ya ce a lokacin, "shi ne shugaba kuma jagora na ɗarikar Kaɗiriyya na Afirka ta Yamma, kuma ya samu sa hannu da sa albarka tun daga gidan shi Sheikh Abduqadir Jelani ɗin tun a lokacin tare da tabbatar masa da jagorancin ɗarikar a wannan yankin namu na Afirka ta Yamma baki ɗayanta," in ji shi.
Ya ce marigayin ya samu wannan ɗaukakar ce saboda irin ƙoƙarin da asalin gidan suka gani yana yi wajen hidimata wa hanyar karantarwa da kuma yaɗa addinin musulunci.
Ya ƙara da cewa, "sun kasance suna zuwa har Kano domin ƙarfafa masa gwiwa da goya masa baya har suka amince da ɗaura masa jagorancin wannan ɗarikar a yankinmu," in ji shi.
Ya ce an fara maukibin ne da mutum biyar zuwa shida, "amma yanzu miliyoyin mutane ne daga Najeriya baki ɗaya da ma ƙasashe da dama daga wajen ƙasar nan," in ji shi.
Yanzu dai jagoran ɗarikar, kuma khalifanta a Afirka ta Yamma shi ne Sheikh Qaribullahi Sheikh Nasiru Kabara, kuma shi ne yake jagorantar bikin.
Me ake yi a ranar?

Asalin hoton, Ali Rabiu Sufi
A game da abubuwan da suka kamata a riƙa aiwatarwa a wannan rana ta maukibi, Sheikh AbdulGaffar ya ce babban maƙasudin shi ne a musanya abubuwan da ake yi a baya da suke da alaƙa da maguzanci a ƙasar Hausa, sai su kasance ana gudanar da abubuwa na addini.
A cewarsa, "Alhamdulillah, an samu nasara sosai domin a sanadiyar assasa wannan biki na maukibi, wasu taruka da dama sun fito waɗanda ake aiwatar da bukukuwa na zagaye na addini, waɗanda kuma sun taimaka wajen ɓatar da wadancan da ake yi a baya da suke da alaƙa da al'adun na maguzanci," in ji AbduGaffar, wanda BBC ta tattauna da shi daga filin maukibi na bana.
Ya ce kamar yadda suka aiwatar a yau, haka ake gudanar da bikin tun shekaru aru-aru.
"Abin da ake gudanarwa shi ne tun daga hudowar rana ta ranar bikin, za ka ga muƙaddamai na wannan ɗarika daga jihohin Najeriya baki ɗaya da ma ƙasashe maƙwabta sun yi sammako, sun taru a wannan gida na ƙadariya. Za a taru ana ta ambaton sunan Allah ana ta zikirin Annabi."
"Za ka ga an yi ɗango ƙungiya bayan ƙungiya suna wucewa kowa na ta ambaton Allah da zikirin Annabi daga alfijir har zuwa Isha na ranar. Ko ta ina, ambaton Allah kawai da salatin Annabi za ka ji ana yi."
Ya ƙara da cewa bayan zagayen, ana kuma gudanar da zama na musamman, inda "ake tattauna rayuwar Shehu AbdulQadir da ƙoƙarinsa wajen yaɗa addini domin mutane su samu abin koyi."
Ƙasashen da suke halartar bikin
Da BBC ta tambayi mabiyin na Ƙadiriyya yadda taron ke gudana da kuma ƙasashen da ke halarta, ya bayyana cewa akwai wakilai daga ƙasashen waje irin su:
- Masar
- Nijar
- Chadi
- Libya
- Kamaru
- Da wasu ƙasashen
Ya ce dukkan ƙasashen akwai mahalarta bikin da suke zuwa a duk shekara, "kuma ana gudanar da taron cikin lumana."
Tasirin bikin

Asalin hoton, Ali Rabiu Sufi
A ɓangaren amfani da tasirin ranar, AbdulGaffar ya ce babban tasirinsa shi ne nuna ƙarfin addinin musulunci.
Ya ce, "babban abin da wannan biki yake nunawa shi ne ƙarfin musulunci da ƙarfin haɗin kan musulmi. Ka ga duk inda aka haska wannan taron a duniya, duk wani masoyi da ma maƙiyi da ya ga zai gane cewa lallai addinin musulunci yana da ƙarfi a wannan jiha da ma wannan ƙasa," in ji shi.
Ya ƙara da cewa bikin yana da tasiri wajen nuna ƙarfin addinin musulunci a Afirka "saboda mutanen da miliyoyin nan duk sun taru ne a ƙarƙashin tutar musulunci a soyayyar Annabi."










