Mutum 570 aka kashe a Najeriya a watan Afrilun 2025 — Rahoto

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya ta ce adadin mutum ɗari biyar da saba'in (570) aka kashe a watan Afrilun bana, a cewar wani sabon rahoto da ta fitar.
Hukumar ta kuma ce mutum ɗari biyu da saba'in da takwas (278) aka yi garkuwa da su daga alƙaluman da ta tattara.
A shafinta na intanet, hukumar ta ce ta tattara alƙaluman ne daga koken da ta samu na keta haƙƙin ɗan adam daga ofisoshinta da ke sassan Najeriya.
Rahoton dai ya yi nazari ne tun daga watan Janairun 2025, zuwa watan Afrilun shekarar.
Hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta Najeriyar ta ce an samu ƙaruwar kisan mutane da kashi 160 daga watan Maris na 2025, yayin da aka samu ƙaruwar satar mutane da kashi 240.
Rahoton hukumar ya ce daga watan Janairun 2025 zuwa Afrilu, an kashe mutum 1,290.
Kuma a cewar rahoton, 'yan bindiga masu fashin daji ne suka fi yin kisan, sai mayaƙan Boko Haram da kuma mayaƙan Lakurawa.
Kazalika rahoton ya nuna cewa an fi kashe mutane a yankin arewa ta tsakiya inda jihar Benue ta zamo kan gaba inda aka kashe mutum 139, sai jihar Filato da ke bi mata sai kuma jihar Borno.
Rahoton ya kuma ambato jihohin Katsina da Kaduna a cikin jerin jihohi biyar da matsalar ta fi ƙamari, to amma kuma bai ambato jihar Zamfara ba.
A ɓangare guda kuma wani rahoton kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin al'amuran tsaro a shiyyar Afirka ta yamma da yankin Sahel, ya ce sama da mutum 1,092 aka kashe a watan Afrilun shekarar 2025, yayin da aka yi garkuwa da mutum 1,178.
Rahoton na kamfanin Beacon, ya nuna jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto ne matsalar ta fi ƙamari.
Masana dai na ganin akwai buƙatar ɗaukar matakai musamman tsarin da zai rage talauci a tsakanin al'umma da kyautata tsarin yaƙi da ta'addanci ta hanyar sanya al'umma a ciki.
Ta hakan ne za a riƙa samar da bayanai ga jami'an tsaro da kuma ɓangarorin da yaƙi da ta'addanci ya shafa.











