Me ya sa Amurka ta sauya tsarin bayar da biza ga ƴan Najeriya?

Biza

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Amurka ta sanar da wasu jerin tsauraran sauye-sauye a tsarin bayar da takardar izinin shiga ƙasarta ga masu zuwan wucin-gadi daga Najeriya.

A yanzu ƙasar ta zaftare wa'adin bizar da kuma dalilan bayar da bizar ga yawancin ƴan Najeriya.

Matakin ya fara aiki ne tun daga ranar 8 ga watan Yuli, kuma ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce kusan dukkanin bizar da take ba wa ƴan Najeriya ta masu zuwan wucin-gadi ce, wato ba masu zuwan zaman dindindin ba da kuma bizar da ba ta diflomasiyya ba, da za ta ba ƴan Najeriya za ta kasance ne ta shiga ɗaya kacal .

Ta kuma ce ta iya wa'adin wata uku ne - saɓanin da yadda take bayar da biza ɗaya da wa'adin shekara ɗaya ko ma fin haka kuma ɗan Najeriya ya shiga Amukar sau da dama.

Sanarwar ta ce wannan na daga cikin matakin da Amurka ta ɗauka na sake tsarin alaƙarta ta cuɗan-ni-in-cuɗe-ka da ƙasashen duniya.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce manufofi da tsare-tsaren bayar da biza na daga abubuwan da ake iya sauyawa a kodayaushe - wanda kuma za a iya sauya shi la'akari da yanayin alaƙar diflomasiya da tsaro da ƙa'idoji ko yanayin shige da fice.

A sanarwar gwamnatin Amurka ta ce tana aiki ƙut-da-ƙut da hukumomin Najeriya domin tabbatar da ganin Najeriya ta daidaita al'amuranta kamar yadda ya dace da tsarin manyan ƙasashen duniya - ta fannin :

1 Bayar da takardun tafiye-tafiye masu tsaro

2 Da hana wuce wa'adin da aka ɗiba wa mutum a biza

3 Da kuma musayar bayanan da suka shafi tsaro ko wani mugun laifi saboda dalilai na kare lafiyar jama'a.

Ƴan Najeriya masu yawon buɗe idanu da ƴan kasuwa masu tafiye tafiye na daga cikin waɗanda wannan sauyi mai tsauri na bayar da bizar Amurkar zai shafa.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Donald Trump

Me ya sa Amurka ta ɗauki matakin?

Cikin sanarwar ɗaukar matakin da amurka a fitar ta ce ta yi hakan ne saboda ita ma Najeriya, abin da take yi wa Amurkawa kenan.

Haka kuma ta ce ƴan Najeriya da ta bai wa biza kan wuce wa'adin da aka ba su a hukumance a zamansu a Amurka.

Ambasada Sulaiman Dahiru, tsohon jakadan Najeriya a Sudan kuma masanin harkokin Diplomasiyya ya ce Amurka na da gaskiya, domin ƴan akwai ƴan Anjeriya da dama da ke zuwa Amurka babu gaira babu dalili.

''Ni ina ganin in dai mutum ba kwararre ba ne a wani fanni, kamar likita ko injiniya, babu wani dalilin da zai kai shi Amurka domin ya zauna'', in ji shi.

Tsohon Jakadan na Najeriya ya ce Amurka ƙasa ce mai cikakken ƴanci wadda kuma za ta iya duk abin da take so game da kanta.

Su wa matakin zai shafa?

Masanin harkokin Diplomasiyyar ya ce mutanen da matakin zai shafa su ne amsu ziyarar yawon buɗe idanu da ƙananan ƴan kasuwa masu zuwa Amurka.

''Dama mutanen da bai kamata su je Amurka ba ne matakin ya shafa, dama babu amfanin zuwansu'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa wasu daga cikin wadanda matakin zai shafa su ne wasu rukunin mutane da ake turawa cikin tawagar gwamnatin Anjeriya, domin halartar wani taro na gwamnati, amma idan suka je sai su ƙi dawowa.

''Akwai wasu mutane da ke shiga cikin tawagar gwamnati, domin halartar wani taro ko biki, wadanda da zarar sun je sai su ƙi dawowa, to suma suna cikin waɗanda matakin zai shafa'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa indai ƙa'ida za a bi, ai dama bai kamata mutum a ba shi bizar wata uku ba sannan ya je ya zarta hakan.

Ta yaya matakin zai shafi alaƙa tsakanin ƙasashen biyu?

Ambasada Sulaiman Dahiru ya ce matakin da Amurkan ta ɗauka ba laifi ba ne, domin ita ma Najeriya za ta iya ɗaukar irinsa.

'Ita Amurka tana cewa abinda Najeriya ke yi wa Amurkawa ne, ita ma ta yi wa ƴan Najeriya'', in ji shi.

Ya kuma ce idan aka tafi a haka to za a ci gaba da zaman doya da manja tsakanin ƙasashen biyu.

''Yanzu idan ka duba Sudan, ai da Amurka ta sanyata cikin ƙasashen da ta hana biza, nan take ita ma ta mayar da martani, ina ta bayyana daina bai wa Amurkawa biza zuwa ƙasar'', in ji masanin harkokin diplomasiyyar.