Me Najeriya ta yi kan matakin Trump na hana 'yan ƙasar shiga Amurka?

Asalin hoton, Getty Images
A kwanan nan ne gwamnatin Trump ta sanar da cewa tana dab da ɓullo da wasu dokoki na hana ƴan Najeriya da Ghana da wasu ƙasashe 34 shiga Amurka, ko da kuwa suna da cikakken izinin shiga ko kuma ci gaba da zama a ƙasar bayan kwana 60 da soke aikinsu.
An ce wannan sabon tsarin shiga Amurka, wanda a yanzu ake sake gyarawa ya zama manufa ta ƙasar, da gwamnatin Trump ta ɓullo da ita da nufin ƙara tsaurara tsaro.
Ƙasashen da dokar za ta shafa
Ƙasashen da ake ganin dokar za ta shafa sun haɗa da Najeriya da Ghana da Nijar da Senegal da Jamhuriyar Benin da Burkina Faso da Kamaru da Ivory Coast da Masar da Gabon da Tanzania da Gambia da Ethiopia.
Akwai kuma Malawi da Liberia da Sudan ta Kudu da Angola Antigua and Barbuda da Bhutan da Cambodia da Cape Verde da Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo da Djibouti.
Sauran su ne, Dominica da Kyrgyzstan da Mauritania da St. Kitts and Nevis da St. Lucia da São Tomé and Príncipe da Syria da Tonga da Tuvalu da Uganda da Vanuatu da Zambia da kuma Zimbabwe.
Me ya sa aka sa wa'adi da kuma yiwuwar hana shiga?
Wa'adin haramcin na kwana 60 ya samo asali ne daga sabon umarni da ofishin shugaban ƙasar ya bayar ne da nufin tsaurara tsaro.
Da kuma kama waɗanda abin ya shafa ta hanyar hana ƙaura daga ƙasashen da ake ganin ba su da cikakken tsarin tantancewa da waɗanda bizarsu ta ƙare suka ci gaba da zama.
Da waɗanda ake ganin haɗarin tsaro ne zamansu a Amurka ko kuma ana zarginsu da alaƙa da ta'addanci.
Amurka ta bai wa gwamnatocin ƙasashen da dokar za ta iya shafa wannan wa'adin miƙa tartibin matakin da suke ɗauka na shawo kan matsalar tsaro.
Da bayanai a kan matsalolin da Amurka ta nuna damuwa da su a kan baƙin haure 'yan waɗannan ƙasashe da ke zaune a Amurkar.
Wannan wa'adi kuma wata dama ce da hukumomin na Amurka suka bai wa ma'aikatan da ba 'yan ci-rani ba, waɗanda aka kore su daga aiki ko kuma suka bar aiki a Amurka don kansu.
Hukumar shige da ficen Amurka ta ce an bayar da wannan wa'adi ne a matsayin wata dama ga wasu ma'aikatan da bizarsu ba ta baƙi ba ce domin su ci gaba da zama a Amurka yayin da suka shigar da buƙatar sauya matsayin bizar tasu zuwa wadda ba ta baƙi ba ce.

Wane mataki Najeriya ke ɗauka a kai yanzu?
Ministan harkokin wajen Najeriya kuma shugaban kwamitin shiga tsakani da tsaro na ECOWAS, Ambassada Yusuf Tuggar, ya bayyana damuwa a kan yadda waɗannan sababbin matakai na hana shiga Amurkar za su shafi ƙasashen Afirka musamman Najeriya.
MInistan ya ce ma'aikatarsa na aiki ba ji ba gani a kan duk wata matsala da aka gano wajen tantance 'yan ƙasar da ma mayar da su Najeriya, kamar yadda takardar da Amurka ta aika musu ta buƙata.
Haka kuma mai taimaka wa ministan na musamman a kan harkokin yaɗa labarai Alkassim Abdul Kadir, shi ma ya yi wa BBC ƙarin bayani cewa takardar da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta aika wa ofisoshin jakadanci ta umarce su, su duba irin matakan da ƙasashen ke ɗauka na inganta tsarin tantance matsayin 'yan ƙasarsu da ke Amurka ba bisa ƙa'ida ba.
Abin da AbdulKadir ya ce Najeriya na aiki tuƙuru da haɗin gwiwar sauran hukumomi don magance matsalolin.

Martanin ECOWAS kan yiwuwar hana shiga Amurkar

Asalin hoton, Google
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ministan harkokin wajen Najeriya, wanda ya yi magana a madadin ƙasashen ECOWAS ya yi gargaɗin cewa idan Shugaba Trump a ƙarshe ya hana 'yan ƙasashen shiga Amurka, ''to ba shakka hakan zai haifar da naƙasu ga kasuwanci da mu'amullar diflomasiyya da kuma bunƙasar nahiyar.
"Zai zama babban abin takaici idan har Amurka ta zartar da matakin, saboda mu yanki ne da ke da damarmaki da dama da kuma a shirye muke mu yi mu'amulla," in ji ministan.
Haka kuma Tuggar ya bayyana manufar a matsayin kuskuren diflomasiyya, yana mai nuna cewa babbar illar manufar ga haɗin kai da mu'amullar tattalin arziƙi a lokacin da Afirka ta cancanci hulɗa mai muhimmanci da ƙasashen duniya.
"Muna da muhimman albarkatun ƙasa hatta wasu ma da ba a samunsu sosai a duniya, (irin su Samarium), da ake samu a jihata, Bauchi," ya ce.
''Mu a wannan sashen na duniya mun daɗe a harkar cinikayya ta duniya tun ma kafin zuwan tsarin ƙasashe na wannan zamanin.''
Ministan wajen na Najeriya ya buƙaci Amurka ta sake shawara kan wannan mataki, yana mai gargaɗin cewa Afirka tana da wasu hanyoyin da za ta iya karkata gare su.
"Ƙasashen ECOWAS da Amurka suna da dama ta daban da za su ƙirƙiri haɗaka bisa manufofi na buƙatun juna.
Haka kuma muna da muhimmanci ga wasu ƙasashen masu samar da makamashi,'' ya ce.
"Za mu yi alaƙa domin cigabanmu; amma maganar ita ce da wa za mu yi ? Wane ne zai yi amfani da damarmakin da ke nahiyarmu ta hanyar barin jami'an gwamnati da ƙwararrun ma'aikata da manyan 'yan kasuwa da masu masana'antu su yi tafiye-tafiye ba tare da wani tarnaƙi ba, su ƙulla yarjeniyoyi?" In ji Tuggar.
Har zuwa yanzu duniya ta zuba ido tare da sauraron wa'adin ya ƙare a san ƙasashen da gwamnatin ta Trump za ta sanya wa takunkumin shiga Amurkar na wucin-gadi da kuma na dindindin, kamar yadda gwamnatin ta tsara.











