Abubuwan da muka sani game da sabuwar dokar hana shiga Amurka da Trump ya sanya

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Victoria Bourne
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanya hannu kan dokar hana 'yan kasashe 12 shiga Amurka, bisa dalilan barazanar tsaron kasa, kamar yadda Fadar White House ta bayyana.
Haka kuma, akwai ƙarin ƙasashe bakwai da 'yan kasarsu za su fuskanci takunkumin shiga Amurka na ɗan wani lokaci.
Shugaban Amurka ya ce za a iya sake duba jerin ƙasashen idan aka samu "ingantattun sauye-sauye," kuma za a iya ƙara wasu ƙasashen idan "barazanar tsaro ta sake bayyana a sassan duniya."
Wannan shi ne karo na biyu da Trump ke bada umarnin hana wasu ƙasashe shiga ƙasar.
A karo na farko ya yi hakan a shekarar 2017, lokacin wa'adin mulkinsa na farko.
Waɗanne ƙasashe ne dokar ya shafa?
Donald Trump dai ƙasashe 12 ne ya haramta wa shiga Amurka, kuma sun haɗa da:
- Afghanistan
- Myanmar
- Chadi
- Jamhuriyar Congo
- Equatorial Guinea
- Eritrea
- Haiti
- Iran
- Libya
- Somalia
- Sudan
- Yemen
Ƙarin ƙasashe bakwai da Trump ya ce 'yan kasarsu za su fuskanci takunkumin shiga Amurka na ɗan wani lokaci sun haɗa da:
- Burundi
- Cuba
- Laos
- Sierra Leone
- Togo
- Turkmenistan
- Venezuela
Wannan dokar za ta fara aiki ne daga ranar Litinin da karfe 12:01 na safe wato ƙarfe 05:01 agogon BST.
An tsara wannan lokacin haka ne domin kauce wa hargitsi a filayen jiragen sama kamar yadda aka gani shekaru takwas da suka gabata lokacin da aka aiwatar da irin wannan mataki ba tare da gargaɗi ba.
Ba a bayyana ranar da dokar za ta ƙare ba, amma an tanadi duba dokar lokaci-lokaci domin kimantawa da sabuntawa.
Me ya sa aka sanar da dokar?
Fadar White House ta ce waɗannan "matakai na haramta wa wasu ƙasashe shiga Amurka" an ɗauke su ne domin "kare 'yan Amurka daga barazanar wasu 'yan ƙasashen waje masu haɗari."
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Donald Trump ya ce harin da ake zargi da faruwa kwanan nan a Boulder da Colorado, ya "bayyana irin haɗarin da 'yan ƙasashen waje da ba a tantance su yadda ya kamata ba ke kawowa."
A ranar Lahadi da ta gabata, wani mutum ya kai hari a wajen taron masu nuna goyon baya ga fursunonin Isra'ila, inda ya jefa wasu abubuwan fashewa guda biyu, lamarin da ya jikkata mutum12.
Mutumin da ake zargi da kai harin an bayyana shi a matsayin dan ƙasar Masar. Sai dai kuma Masar ba ta cikin jerin ƙasashen da aka hana shiga Amurka.
Trump na da kusanci da Shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi, wanda ya taɓa bayyana shi a baya a matsayin "masoyinsa cikin shugabannin kama-karya."
Waɗanda dokar ba ta shafa ba
Akwai wasu mutane daga cikin ƙasashen da dokar ta shafa da za su iya samun izinin shiga Amurka saboda wasu abubuwa kamar haka:
- 'Yan wasa da ke tafiya domin manyan wasannin ƙasashen duniya kamar Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026 ko Wasannin Olympics na 2028
- Masu riƙe da "bizar ƴan ci-rani, waɗanda suke 'yan tsiraru na kabilanci ko addini da ke fuskantar tsanantawa a Iran
- 'Yan kasar Afghanistan da ke da Takardar Musamman ta ci-rani.
- Mutane masu shaidar zama ƴan ƙasa biyu waɗanda ɗayan ƙasarsu ba ta cikin jerin ƙasashen da aka haramta wa shiga Amurka.
Bugu da ƙari, za a iya ɗaga wa wasu mutane ƙafa bisa "shari'a ta musamman," idan har "mutumin zai taka rawa wajen kare muradun kasan Amurka."
Mene ne martanin mutane game da dokar?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ana sa ran sabon umarnin na Trump na haramta wa wasu ƙasashe shiga ƙasar zai fuskanci ƙalubale a kotu yayin da ta janyo martani daga cikin gida da kuma ƙasashen waje.
Somalia ta bayyana shirinta na yin aiki tare da Amurka domin warware duk wata matsalar tsaro.
A cikin wata sanarwa, Jakadan Somalia a Amurka, Dahir Hassan Abdi, ya ce ƙasarsu "na daraja dangantakar tarihi" da ke tsakanin ta da Amurka.
Ministan harkokin cikin gida na Venezuela, Diosdado Cabello, ya yi gargaɗi cewa "kasancewa a Amurka ma babbar barazana ce ga kowa, ba kawai ga 'yan Venezuela ba."
'Yan Democrat kuma sun caccaki wannan mataki.
Pramila Jayapal, 'yar majalisa daga jihar Washington, ta wallafa a shafinta na sada zumunta cewa: "Wannan dokar za ta ƙara ware mu a idon duniya."
Wani dan Democrat, ɗan majalisa, Don Beyer, ya ce Trump "ya cin amanar manufofin ginin Amurka da waɗanda suka kafa ta."
Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan adam ma sun soki wannan dokar.
Kungiyar Amnesty International USA ta bayyana dokar a matsayin "mai nuna wariya da kuma mugunta kai tsaye."
Sai kuma ƙungiyar Human Rights First ta Amurka, ta ce dokar za ta ci zarafin 'yan ci-rani."
Me ya faru a baya da Trump ya hana ƙasashe shiga Amurka?
Trump ya bayar da umarnin dokar hana shiga Amurka ta farko a lokacin wa'adinsa na farko a fadar White House a shekarar 2017.
Dokar ta ƙunshi wasu daga cikin ƙasashen da ke cikin sabon umarninsa, ciki har da Iran da Libya da Somaliya.
Masu suka sun kira dokar da "dokar hana musulmai shiga ƙasar" saboda ƙasashen bakwai cikin waɗanda aka hana shiga Amurka suna da mafi yawan musulmai, kuma nan take aka ƙalubalanci dokar a kotuna daban-daban na Amurka.
Fadar White House dai ta sake gyara wannan doka, inda daga ƙarshe aka ƙara ƙasashen da musulmai ba su fi yawa ba, wato Koriya ta Arewa da Venezuela.
Kotun Koli ta tabbatar da sahihancin dokar a shekarar 2018.
Shugaba Joe Biden, wanda ya gaji Trump, ya soke wannan doka a shekarar 2021, inda ya kira ta a matsayin wadda ba ta dace ba.











