Tambayoyin da ƴan Afirka ke yi game da dokar hana shiga Amurka da Trump ya sa

Hoton wata mata a filin jirgin sama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu suka na ganin akwai rashin inganci da kuma wariyar launin fata a dokar.
    • Marubuci, Jelilat Olawale
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da sabuwar dokar hana tafiye-tafiye da ta shafi ƙasashe 12 - bakwai daga ciki sun fito daga Afrika.

Mun bi diddigin abin da mutane a faɗin nahiyar suke tambaya a intanet ta hanyar amfani da manhajar Google Trends da kuma shafukan sada zumunta na BBC Afrika.

Ga wasu daga cikin tambayoyi da damuwar da mutane suka bayyana.

Waɗanne ƙasashe sabuwar dokar ta shafa?

Bakwai daga cikin ƙasashe 12 da dokar ta hana shiga Amurka sun haɗa:

  • Chadi da Congo-Brazzaville da Equatorial Guinea da Eritrea da Libya da Somalia da kuma Sudan.

Sauran su ne Afghanistan da Myanmar da Haiti da Iran da kuma Yemen.

Dokar ta kuma sanya wa wasu ƙasashe sharuɗa, da suka haɗa da:

  • Burundi da Togo da kuma Saliyo daga Afrika, da kuma Cuba da Laos da Turkmenistan da kuma Venezuela.

An hana al'ummar waɗannan ƙasashen neman biza don karatu ko yawon buɗe ido, amma sauran biza na iya samuwa.

Yaushe dokar za ta fara aiki? Kuma me ƙasashe za su yi don a janye ta?

Dokar hana shiga Amurka za ta fara aiki daga karfe 12:01 na dare agogon Washington wato karfe 04:01 kenan agogon GMT ranar Litinin, 9 ga watan Yuni.

Dokar ba ta da ranar karewa amma ba za a soke bizar da aka bayar kafin lokacin dokar ba.

Shugaban Amurka ya ce za a iya sake duba jadawalin, idan aka samu ci gaba kuma za a iya ƙara wa wasu ƙasashen yayin da barazana ke ƙaruwa a duniya.

Mene ne dalilin zaɓar waɗannan ƙasashen Afirka?

Kowacce daga cikin ƙasashen Afrikan na da alamar tambaya game da kwarewa wajen bayar da fasfo ko kuma suna da tarihin rashin amincewa su kwashe al'ummar su.

Sauran dalilan sun haɗa da zargin karya ka'idojin bayar da biza daga mutanen ƙasashen da kuma barazanar tsaro ga rayuwar al'ummar Amurka.

Kakakin fadar White House Abigail Jackson ta shaida wa BBC cewa matakin zai kare Amurkawa daga ɓata-gari ƴan ƙasashen ketare.

Shin wannan mataki ya shafi tsaro, ko kuwa siyasa ce kawai?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaba Trump ya bayar da misali da harin ta'addanci da aka kai Boulder da Colorado a baya-bayan nan.

Sai dai wanda ake zargi da aikata lamarin ɗan ƙasar Masar ne - duk da haka Masar ba ta cikin ƙasashen da sabuwar dokar hana zirga-zirga ta shafa.

Masu suka sun yi iƙirarin cewa rashin tsarin wannan mataki ya tabbatar siyasa ce ko wariyar launin fata, musamman ganin cewa ba duk ƙasashen da ke da matsalar tsaro dokar ta shafa ba - bugu da kari yawancin ƙasashen da aka lissafa ba su da tarihin ayyukan ta'addancin da suka shafi Amurka.

Ƙungiyar Tarayyar Afrika AU ta bayyana damuwa game da mummunan tasirin da wannan tsari zai haifar sannan ta nemi Amurka ta zauna tare da wadannan 'kasashe don samar da mafita.

Amnesty International ta Amurka ta bayyana dokar a matsayin wariyar launin fata, da kuma rashin tausayi yayin da ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam a Amurka ta bayyana lamarin a matsayin sabuwar hanyar nuna adawa ga bakin haure da shugaban ya ɗauka.

Jakadan Somaliya a Amurka a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce gwamnatinsa a shirye take ta shiga tattaunawa don magance matsalolin da aka bayyana.

Shugaba Trump ya bayyana Somaliya a matsayin "maɓoyar ƴan ta'adda".

Wane tasiri dokar za ta yi ga iyalai da ƴan ciranin da ke Amurka?

A karkashin sabuwar dokar hana tafiye-tafiye, an keɓe wasu baki da kuma iyalan da suke zaune a Amurka.

Masu riƙe da Green Card za su iya ci gaba da shiga cikin ƙasar.

  • Yaran da ƴan ƙasar Amurka suke rikonsu.
  • Masu riƙe da shaidar zama 'yan ƙasashe biyu waɗanda ke riƙe da izinin zama Amurka.
  • Dangin iyalan da ke zaune a Amurka, miji ko mata ko yara da iyaye za su iya neman biza.
  • Wasu ma'aikatan ƙasashen waje na gwamnatin Amurka waɗanda suka yi hidima a ƙasashen waje aƙlla 15 da ƴaƴansu da matansu.
  • Waɗanda ke fuskantar tsangwama a Iran.
  • Ƴan Afghanistan masu biza ta musamman za su shiga.

Wannan na nufin yayin da dokar ta hana shigar ƙasashe 12 galibi daga Afirka, ba za ta yi aiki kan waɗannan mutanen da aka keɓe ba.

Ko akwai yiwuwar kalubalantar sabuwar dokar a kotu?

Jeff Mason, wakilin kamfanin dillancin labarai na Reuters a fadar White House, ya shaida wa BBC cewar dokar ta yi kama da wadda Trump ya ayyana a wa'adin mulkinsa na farko a shekara ta 2017, akan da dama daga cikin ƙasashen Musulmi - sai dai a wannan karon an kara yawan ƙasashen.

Ko dokar ta bayar da mamaki?

Ga waɗanda ke bibiyar Trump sama da shekara ɗaya, wannan sanarwa ba za ta bayar da mamaki ba.

Tun komawarsa fadar White House ya kaddamar da sabon tsari kan bakin haure.

A shekara ta 2017 ya kaddamar da irin wannan doka wadda ta shafi ƙasashen Somalia da Chadi waɗanda suke cikin sabon jadawalin na wannan lokaci.

Ko dokar za ta shafi ƙungiyoyin da suke shirin halartar gasar cin Kofin Duniya a 2026 a Amurka?

Labari mai daɗi ga FIFA shi ne dokar Trump ta ware 'yan wasannin motsa jiki da mambobin tawagarsu da masu horas da 'yan wasa da masu goyon baya da iyalansu da za su yi tafiya irin ta halartar gasar wasannin duniya kamar Olympics.

Wannan na nufin Iran wadda ta samu nasarar zuwa gasar ta shekara ta 2026 za ta samu damar aikawa da tawagarta da jami'anta da suka cancanta.

Sai dai 'yan wasan Iran ba za su samu damar kai abokansu da iyalansu ba.

Mene ne bambancin wannan dokar da ta 2017?

Yayin wa'adin mulkinsa na farko, Shugaba Trump ya bayar da dokar hana ƙasashen Musulmi bakwai shiga Amurka, abin da masu suka bayyana a matsayin ''hana Musulmi shiga Amurka''.

Dokar ta fuskanci kalubale da dama na shari'a kuma an sake waiwayar ta kafin kotun kolin Amurka ta tabbatar da ita a shekara ta 2018.

Daga baya shugaba Joe Biden ya soke ta a shekara ta 2021.

Wakilinmu na Arewacin Amurka Jake Kwon, ya ce sabuwar dokar wadda aka tsara cikin hikima, a wannan karon ta karkata daga addini zuwa batutuwan zama a ƙasar ba bisa ka'ida ba bayan biza ta kare da matsalolin siyasa.

Yayin da ƙasashe irinsu Iran da Libya da Somalia suka bayyana a cikin jadawalin, sabuwar dokar ta shafi ƙasashe 12.

Wannan sabuwar dokar hana shiga Amurkan ba ta da lokacin karewa, ba kamar ta baya ba wadda ta ɗebi wa'adin kwanaki 90 zuwa 120.