Zaɓen Amurka: Me nasarar Trump ke nufi ga ƙasashen duniya?

Donald Trump da Vladmir Putin

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaban Rasha Vladmir Putin kenan tare da Donald Trump yayin wani taron ƙasashe 20 mafiya girman tattalin arziki a Japan a 2019
Lokacin karatu: Minti 5

Komawar Donald Trump fadar White House na shirin sake fasalin manufofin Amurka ta fannin ma'amalarta da sauran ƙasashen duniya, inda ake tunanin za a samu muhimman sauye-sauye da dama a lokacin da yaƙe-yaƙe da rashin tabbas suka mamaye sassan duniya.

A lokacin yaƙin neman zaɓensa, Trump ya yi alƙawurran manufofin siyasa ba tare da yin takamaiman bayanai ba, yayin da yake iƙirarin dawo da martabar Amurka ta hanyar ɗaukaka kirarin ''America First'' - wato Amurka Farko.

Nasarar da ya yi tana nuni da ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za su iya kawo cikas a tsarin Washington a fannin harkokin ƙasashen waje, yayin da ake fama da rikice-rikice masu yanayi da juna a sassan duniya.

Za mu iya hasashen wasu daga cikin matakan da zai iya ɗauka a sassan duniya daga kalamansa a lokacin yaƙin neman zaɓe da tarihinsa a kan karagar mulki daga 2017 zuwa 2021.

Rasha, Ukraine, Nato

A lokacin yaƙin neman zaɓe, Trump ya sha nanata cewa zai iya kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine "a cikin kwana ɗaya". Lokacin da aka tambaye shi ta yaya, sai ya ce ta hanyar ƙulla da yarjejeniyar amma ya ƙi bayar da takamaiman bayani.

A wani bincike da wasu tsoffin masu bai wa Trump shawara kan tsaron ƙasa suka wallafa a watan Mayu sun ce ya kamata Amurka ta ci gaba da samar da makaman da take bai wa Ukraine amma ta sanya sharaɗin cewa sai Kyiv ta shiga tattaunawar sulhu da Rasha.

Don shawo kan Rasha, ƙasashen Yamma za su yi alƙawarin jinkirta shigar da Ukraine ƙungiyar NATO. Tsofaffin masu ba da shawarar sun ce bai kamata Ukraine ta yi watsi da fatanta na dawo da dukkan yankunanta daga mamayar Rasha ba, amma kamata ya yi ta gudanar da tattaunawar bisa matsayar da ake kai a halin yanzu.

Abokan hamayyar Trump na Democrat, waɗanda ke zarginsa da abota da shugaban Rasha Vladimir Putin, sun ce matakin da ya ke shrin ɗauka zai zama tamkar miƙa wuya ne a ɓangaren Ukraine, kuma za ta jefa dukkan ƙasashen Turai cikin haɗari.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya yi ta nanata cewa abin da ya sa a gaba shi ne kawo ƙarshen yaƙin da kuma daƙile kuɗaɗen da Amurka ke kashewa a kai.

Babu tabbas kan irin tasirin da takardar binciken tsoffin masu ba da shawarar ta yi a tunanin Trump, amma yana yiwuwa ta ba mu damar yin hasashe kan irin shawarwarin da zai iya samu.

Amfani da manufarsa ta "America First" don kawo ƙarshen yaƙin zai yi matuƙar tasiri kan makomar ƙungiyar NATO, haɗakar tsaron da aka ƙirƙira bayan yaƙin duniya na biyu musamman domin takawa tarayyar soviet birki.

Yanzu dai ƙungiyar ta Nato ta na da ƙasashe sama da 30 kuma Trump ya daɗe yana nuna shakku kan kawancen, yana mai zargin ƙasashen Turai da yin rawa da bazar kariyar da Amurka ke bayarwa.

Babu dai tabbas ko a zahiri zai janye Amurka daga ƙungiyar tsaron ta NATO, wanda hakan zai kawo gagarumin sauyi a huldar tsaro a yankin tekun Atlantika da ba a gani ba cikin kusan karni guda.

Wasu daga cikin abokansa na nuni da cewa wannan matsayar tasa barazana ce kawai domin samun galaba a tattaunawa da sauran mambobin haɗakar domin su cika ka'idojin kashe kuɗi a fannin tsaro na ƙungiyar.

Amma gaskiyar magana ita ce, shugabannin NATO za su damu matuƙa game da abin da nasararsa ke nufi ga makomar ƙawancen da kuma yadda shugabannin ƙasashen da ke adawa da su za su kalli tasirin ƙungiyar ko kuma akasin haka.

Yankin Gabas ta Tsakiya

Kamar yadda ya yi kan Ukraine, Trump ya yi alƙawarin samar da "zaman lafiya" a Gabas ta Tsakiya - yana nufin zai kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila da Hamas a Gaza, da yaƙin Isra'ila da Hezbollah a Lebanon, amma bai bayyana yadda zai cimma wannan manufa ba.

Ya sha nanata cewa, da a ce yana kan karagar mulki maimakon Joe Biden, da Hamas ba za ta kai wa Isra'ila hari ba, saboda manufarsa ta "matsin lamba" kan Iran, wadda ke goyon bayan ƙungiyar.

Mai yiwuwa Trump zai yi ƙoƙari ya koma kan wannan manufar, wanda ya sa gwamnatinsa ta janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliya da ta ƙulla da Iran, ta sanya takunkumai masu tsauri kan Iran ɗin tare da kashe Janar Qasem Soleimani - babban kwamandan sojan ƙasar.

A zamansa a fadar White House Trump ya zartar da manufofin goyon bayan Isra'ila masu ƙarfi, inda ya bayyana birnin Ƙudus a matsayin babban birnin Isra'ila tare da mayar da ofishin jakadancin Amurka can daga Tel Aviv - matakin da ya zaburar magoya bayansa na Jam'iyyar Republican.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kira Trump "Abokin mafi aminci da Isra'ila ta taba samu a Fadar White House".

Sai dai masu sukar lamirin nasu na ganin manufarsa ta yi tasiri wurin rura wutar tashin hankali a yankin.

Falasdinawa sun ƙaurace wa gwamnatin Trump, saboda watsi da Washington ta yi na iƙirarin ikon da suke da shi kan birnin Kudus - birnin da ya zama cibiyar tarihin ƙasa da addini ga Falasdinawa.

An kuma mayar da su saniyar ware a lokacin da Trump ya ƙulla yarjejeniyar da ake kira "Abraham Accord" wadda aka cimma yarjejeniya mai cike da tarihi don daidaita alaƙar diflomasiyya tsakanin Isra'ila da wasu ƙasashen Larabawa da na musulmi. Ta yi haka ne ba tare da Isra'ila ta amince da kafa kasar Falasdinawa mai cin gashin kanta a nan gaba ba - wanda shi ne babban sharadi da ƙasashen Larabawan suka bayar kafin kulla irin wannan yarjejeniyar a yankin.

A madadin haka an bai wa ƙasashen da abin ya shafa damar mallakar manyan makaman Amurka domin su amince da Isra’ila.

Trump ya yi jawabai da dama a lokacin yaƙin neman zaɓe yana mai cewa yana son kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

Yana da alaƙa mai sarƙaƙiya da Netanyahu, amma tabbas yana da ikon matsa masa lamba.

Har ila yau yana da tarihin dangantaka mai ƙarfi da shugabanni a manyan ƙasashen Larabawa waɗanda ke da alaƙa da Hamas.

Ba a san yadda zai cimma muradinsa na nuna goyon baya mai ƙarfi ga shugabancin Isra'ila ba yayin da kuma yake ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

Abokan ƙawancen Trump sun bayyana rashin sanin abin da zai aikata a matsayin wata kadara ta diflomasiyya, amma a yankin gabas ta tsakiya da ke fama da rikice-rikice, ba a san yadda hakan zai kasance ba.

China da harkar kasuwanci

Hanyar da Amurka ke bi da ƙasar China ita ce mafi mahimmancin dabarunta na manufofinta na ma'amalla da kasashen ƙetare - kuma wanda ke da muhimmin tasiri ga tsaro da kasuwanci a duniya.

Lokacin da ya ke kan karagar mulki, Trump ya sanya haraji kan wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga China. Wannan ya haifar da harajin musayar haraji tsakanin ƙasashen biyu.

An yi ƙoƙarin warware rikicin kasuwancin amma cutar Korona ta wargaza wannan yunƙurin, kuma dangantakar ta yi muni lokacin da tsohon shugaban ya bayyana Korona a matsayin ''Cutar ƴan China''.

Yayin da gwamnatin Biden ta yi iƙirarin ɗaukar matakin da ya dace game da manufofin China, a zahiri, ta ci gaba da tabbatar da yawancin harajin da aka ƙaƙaba a lokacin Trump.

Tsare-tsaren kasuwanci na da tasiri kan yadda masu kaɗa ƙuri'a a Amurka ke kallon yunƙurin da gwamnati ke yi na kare ayyukan ɓangaren ƙere-ƙere na ƙasar.

Trump ya yaba wa shugaban kasar China Xi Jinping a matsayin mutum "mai kaifin basira" kuma har ila yau "mutum mai hadari" inda ya ce shugaba ne mai matuƙar tasiri wanda ke juya mutane biliyan 1.4 da "hannun ƙarfe" - wani bangare na abin da ƴan adawa suka bayyana a matsayin sha'awar da Trump ya ke nunawa kan masu mulkin kama-karya.

Da alama dai tsohon shugaban zai ƙauracewa tsarin gwamnatin Biden na samar da ingantacciyar ƙawancen tsaro tsakanin Amurka da sauran ƙasashen yankin a wani yunƙuri na taka wa China birki.

Amurka ta ci gaba da ba da taimakon soja ga Taiwan domin cin gashin kanta, wanda ita kuma China ke yi wa kallo a matsayin lardin da nan gaba zai koma ƙarƙashin ikonta.

A watan Oktoba Trump ya bayyana cewa, idan ya koma fadar White House, ba lallai ba ne ya yi amfani da karfin soji don hana China yi wa Taiwan ƙawanya ba saboda shugaba Xi ya san cewa shi 'mahaukaci' ne, kuma zai sanya wa China mummunan haraji kan kayan da ta ke shigarwa Amurka, idan har hakan ta faru.