Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da aka tattauna tsakanin tawagar Najeriya da Traore kan riƙe sojoji
Za a iya cewa Najeriya ta gaji da jira tun bayan da hukumomin Burkina Faso suka "riƙe jirgin samanta na soji" ƙirar C-130 da sojojinta 11 waɗanda suka sauka a ƙasar ranar 8 ga watan Disamba.
Bayan sama da mako ɗaya da faruwar lamarin, wata tawaga daga Najeriya ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin waje Yusuf Tuggar ta je birnin Ouagadougou inda ta tattauna da shugaban ƙasar Kyaftin Ibrahim Traore.
A tattaunawarsa da BBC, Tuggar ya ce "mun je ne domin isar da saƙon shugaba Bola Tinubu ga shugaban Burkina Faso Ibrahim Traore".
Tun bayan sanarwar da ƙungiyar AES ta bayar cewa "tana tsare da sojojin Najeriya 11 da jirgin sojin ƙasar" wanda ya sauka a garin Bobo-Dioulasso, al'ummar Najeriya suke ta sanya ido domin ganin yadda za a warware matsalar, kasancewar dama babu cikakken jituwa tsakanin Najeriya da na ƙasashen na Sahel tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasashen.
Haka nan an shiga ruɗani sanadiyyar bayanai masu cin karo da juna da aka riƙa samu tsakanin hukumomin Najeriya da na Burkina Faso game da batun.
Yayin da Najeriya ta ce "Sojojinmu suna cikin koshin lafiya, kuma hukumomin Burkina Faso sun karɓe su cikin mutunci," a ɓangare daya kuma hukumomin ƙungiyar ƙasashen Sahel ta AES cewa ta yi "an karya dokar sararin samaniya da shiga hakkin kasashe mambobinta".
Abin da ya kai mu Burkina Faso - Tuggar
"Mun je ne a madadin shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya umarce mu mu je mu kai saƙo na musamman ga shugaban Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore dangane da harkokin da suka shafi kasashen biyu da kuma na tsaro na yankinmu na Afirka ta yamma sanadiyyar ta'addanci da ke faruwa," kamar yadda ministan harkokin wajen na Najeriya Yusuf Tuggar ya shaida wa BBC.
Ministan ya ce sun tattauna kan harkokin tsaro da diflomasiyya da tsaro, kamar yadda matsalar yaƙin Libya ta haifar da yaduwar makamai a ƙasashen Afirka da kuma batun dakatar da ƴan ci-rani.
Sai dai minsitan ya ce baya ga haka sun tattauna kan batun jirgin saman Najeriya da ya yi saukar gaggawa a Burkina Faso.
"A kan batun jirgin sojojin sama na Najeriya da ya samu matsala, dole ya sauka a wani filin jirgin sama na Burkina Faso, kuma aka dakatar da shi da matuƙansa, mun tattauna kuma an samu bakin zaren.
"An amince da cewa su dawo gida Najeriya, dama za a kai shi gyara ne a ƙasar Portugal, daga nan ne ya samu matsala," a cewar Tuggar.
Duk da cewa ministan ya amince cewa batun riƙe jirgin saman sojin Najeriya a Burkina Faso na daga cikin manyan abubuwan da ya kai su ƙasar, amma ya ce dama akwai batutuwa na diflomasiyya da tsaro da Najeriyar ke so ta tattauna a kai da shugaban na Burkina Faso.
Yaushe jirgi da kuma sojojin Najeriya za su koma gida?
Babban abin da ƴan Najeriya da sauran masu bibiyar lamarin ke son sani shi ne yaushe sojojin da kuma jirgin sojin na Najeriya zai bar Burkina Faso.
Sai dai a tattaunawar ministan da BBC bai bayyana takaimaiman lokacin da hakan zai faru ba, amma babban abin da ya tabbatar shi ne "an warware matsalar".
"An saki jirgi, to amma dama matsala ya samu, saboda haka dole sai an tabbatar da cewa jirgin zai iya tashi ya kai su (sojoji) Najeriya ba tare da ya sauka a wani wuri ba kafin ya isa," a cewar Tuggar.
Amma me ya sa sojojin ba za su koma Najeriya ba yayin da ake ci gaba da gyaran jirgin a Burkina Faso?
Sai Tuggar ya ce: "(sojojin) su ne masu gyaran, ko da an kawo shi Najeriya su ne za su gyara jirgin".
Ya nuna cewa sojojin na zaune a Burkina Faso ne domin su yi aikin gyaran jirgin kafin su bar ƙasar baki ɗaya.
Wane hali sojojin Najeriya suke ciki?
Ministan Yusuf Tuggar ya ce ya gana da sojojin Najeriya 11 da ke ƙasar ta Burkina Faso, wadanda suka hada da matuƙa da kuma masu gyaran jirgin.
"Mun tarar da su cikin ƙoshin lafiya, sun samu kula sosai daga gwamnatin Burkina Faso, wurin da suke zaune wuri ne mai kyau," in ji Tuggar.
Game da ko ana tsare ne da sojojin a wani wuri, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito a baya, ministan ya ce "Mun same su ne a gida, kuma gida ne har da wurin ninƙaya".
Wani bidiyon ganawar da aka tura wa BBC ya nuna yadda ministan ya gana da sojojin a wni gida mai yalwa, inda ya yi musu jawabi, sannan kuma suka ɗauki hoto a tare.
Bidiyon ya nuna sojojin sanye da kayan matuƙa jirgin saman sojin Najeriya ba tare da wata damuwa a fuskokinsu ba.
Me Ibrahim Traore ya faɗa wa tawagar Najeriya?
Bayanin Yusuf Tuggar ya nuna cewa Ibrahim Traore ya yi maraba da duka saƙon da tawagar Najeriya ta isar masa.
"Shi (Ibrahim Traore) ne ma ya fada mana cewa matar ɗaya daga cikin matuƙa jirgin ta haihu," in ji Tuggar.
"Ya nuna mana cewa ya sanya ido kan kula nagartacce ga sojojinmu da ke can Burkina Faso".
Sannan a game da batun alaƙar Najeriya da Burkina Faso, Tuggar ya ce "Ya (Traore) nuna cewa Burkina Faso da Najeriya suna da tarihi na danƙon zumunci, kuma ya kamata a ƙara danƙon zumuncin da ke tsakanin ƙasashen domin a shawo kan yaƙin da ake yi da ta'addanci a yankin."