Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasashen Afirka 10 da suka fi kashe kuɗi a harkar tsaro a 2025
Masar
Masar ce ta kasance ƙasa ta ɗaya a cikin jerin ƙasashen Afirka goma da suka fi kashe kuɗi a harkar tsaro, a wannan shekara ta 2025, kamar yadda wani shafi na intanet kan harkokin bayanan soji na duniya (2025 Global Firepower), ya nuna.
Bayanan da aka yi la'akari da su wajen haɗa rahoton da ya nuna haka sun haɗa da yawan sojojin ƙasa, da kayan yaƙi na zamani da kuma ƙarfin sojojin ruwa da na sama.
Saboda haka Masar ta kasance kan gaba a nahiyar Afirka, saboda tana da ƙarfin sojojin ƙasa da manyan motocin yaƙi da igwa-igwa da jiragen sama masu sauƙar ungulu na yaƙi, kamar yadda rahoton ya nuna.
Rahoton ya yi ƙiyasin kasafin kuɗin tsaro na sojin Msara ya kai dala biliyan 5.88 a duk shekara.
2. Aljeriya
Rundunar sojin ƙasa ta Aljeriya ta ƙunshi sojoji na ƙasa da sani da kuma da kuma sojoji na zamani - wato na musamman na ƙasa da na sama da kuma na ruwa
Sojojin sama na ƙasar suna da ƙarfi sosai. An ce a kodayaushe sojojin ƙasa na Aljeriya a shirye suke su kare iyakokin ƙasar ta yankin Arewacin Afirka.
Rahoton ya nuna cewa an baza sojojin ƙasar a faɗine tekun Bahar Rum. An kuma ce sojojin ƙasan sun fi ƙarfi idan suka samu tallafin sojojin sama da na ruwa.
Kasafin kuɗi na shekara-shekara na sojojin na Aljeriya kamar yadda rahoton ya nuna ya kai dala biliyan 25.
3. Najeriya
Ana kimanta ƙarfin sojin Najeriya da yawan dakarun da ƙasar ta yankin Afirka ta Yamma take da su.
Ita ce ƙasar da ta fi yawan sojojin sama a Afirka, kamar yadda rahoton ya nuna.
An yi ƙiyasin yawan sojojin Najeriya ya kai 230,000, kuma tana da dakaru na musamman masu yaƙar 'yanbndiga.
Rahoton ya ce kasafin kuɗin tsaro na Najeriya ya kai dala miliyan 3.16.
4. Afirka ta Kudu
An san Afirka ta Kudu wajen ƙwarewa a fannin tsaro, saboda tana da ƙarfin dakaru. Sojojinta na nuna ƙwarewa da aiki idan ana maganar ƙasa da sama da kuma ruwa.
Haka kuma ƙasar tana da jiragen sama na yaƙi na zamani, waɗanda za su kai hari cikin nasara.
Sojojin ƙasa na Afirka ta Kudu suna da dakaru da aka horar wajen kula da jama'a da kuma wanzar da zaman lafiya.
Sojojin ƙasar ba su da yawa idan aka kwatanta su da na takwarorinsu, amma kuma sun fi ƙarfi da ƙwarewa wajen aiki da kayan aiki da ma kayan aiki na zamani.
Ba a san yawan kasafin kuɗi na sojojin yake ba amma ana ganin zai iya kaiwa dala biliyan 3.1 a wannan shekara ta 2025.
5 Ethiopia
Dakarun da suka fi yawa a rundunar sojin Ethiopia su ne na ƙasa, kamar yadda rahoton ya nuna.
Kuma sojojin ƙasar ta gabashin Afirka suna da ƙarfi sosai.
Ƙasar ta yi fice wajen amfani da dakarun ƙasa masu yawa da kuma na sama masu ƙarfi.
Sojojin sama na Ethiopia suna da ƙarfi sosai. Haka kuma sojojin suna mayar da hankali sosai wajen tsare iyakokin ƙasar da tabbatar da tsaro a cikin gida.
Rahoton na duniya ya yi ƙiyasin cewa a bana kasafin kuɗin sojin ƙasar ya kai dala biliyan 2.10.
6 Angola
Angola ta kashe kuɗi sosai a ɓangaren sojojinta na ƙasa. Haka kuma sojojinta na sama da na ruwa ma suna da ƙarfi.
Yawanci sojojinta sun fi mayar da hankali kan tsaron cikin gida da kuma kare iyakokinta.
Kasafin sojojin ƙasar na wannan shekara -2025 ya kai dala biliyan 1.1.
7 Morocco
Rundunar sojojin Moroko ta ƙunshi dakaru masu yawa da manyan motocin yaƙi na zamani da motocin yaƙi iri daban-daban da jiragen yaƙi na sama da kuma sojojin ruwa.
Dakarun ƙasar za su iya aiki daga tekun Bahar rum zuwa tekun Atalantika.
Shafin tattara bayanan tsaron na duniya ya ce kasafin kuɗin sojin ƙasar ya fi dala biliyan 13.
8 JD Kongo
Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo ita ce ta takwas a nahiyar Afirka a ƙarfin soji. Wannan na nufin suna da cikakkun sojoji masu yawa amma kuma ba su da kayan aiki na zamani da kuma horo, kamar yadda rahotonya nuna.
Kasafin sojin ƙasar na wannan shekara ya kai dala miliyan 800.
9 Sudan
Sudan, kasar da ke cikin yaƙin basasa a yanzu a da tana da dakaru na musamman da aka horar a kan tsaron cikin ƙasa to amma kuma yanzu suna yaƙi a tsakaninsu
An san ƙasar da sojoji a ƙaa da na sama da kuma na ruwa ƙwararru.
An yi ƙiyasin kasafin kuɗin sojin ƙasar a shekara-shekara ya kai dala miliyan 342.
10 Libya
Libya ita ce ta goma a ƙarfin soji a nahiyar Afirka. Kodayake a yanzu tsarin rundunar sojin ƙasar ta Afirka ta Arewa ya ruguje, amma a baya ta kasance tana da sojojin ƙasa da na sama da kuma na ruwa masu ƙarfi da kayan aiki.
Libya, kamar Sudan, tana fama da gagarumar matsalar cikin gida.
Kasafin kuɗinta na soji na shekara ya kai dala biliyan uku in ji rahooton.