Zimbabwe na tsaka-mai-wuya kan hare-haren da giwaye ke kai wa jama'a

.

Asalin hoton, AFP

Babban aikin da Tinashe Farawo ya gamu da shi shi ne na dauko gawar wani mutum dan shekara 30 da giwaye suka tattaka har ya mutu domin ya kai ta wurin iyalansa da suke cikin alhini.

Wannan shi ne irin aikin da masu kula da gandun daji na Zimbabwe Parks and Wildlife Management Authority (Zimparks) suke yawaita yi a yayin da suke sanya ido kan rigimar da ke faruwa tsakanin mutane da kuma dabbobin da ke yin kutse a muhallansu.

Manomin na yankin Mbire yana daya daga cikin mutanen 46 da dabbobin daji suka kashe a wannan shekarar a Zimbabwe.

Gidan adana dabbobi na Hwange National Park, da ke arewa maso yammacin Zimbabwe, wanda shi ne mafi girma a kasar, yana da fadin rubabba'i 14,600, yana iya daukar giwaye 15,000.

Sai dai jami'ai sun ce a yanzu haka yana dauke da kusan giwaye 55,000, inda da dama daga cikinsu sukan shiga garuruwan da ke kusa da gidan adana su domin neman abinci da ruwan sha.

Manyan giwaye na matukar jin yunwa - giwa daya takan sha ruwa galan 44 a kullum sannan takan ci ganye kusan kilogiram 400 - abin da kan jefa manoman da ke hannu-baka-hannu-kwarya cikin mawuyacin hali.

Manoma da ke kusa da kauyen Hwange suna daure kwalaben da ke dauke da wasu abubuwa masu wari domin hana giwaye zuwa kusa da inda suke

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manoma da ke kusa da kauyen Hwange suna daure kwalaben da ke dauke da wasu abubuwa masu wari domin hana giwaye zuwa kusa da inda suke

A yayin da wakilai daga kasashe fiye da 180 suke gudanar da taron mako biyu a Panama kan yarjejeniyar hana cinikin dabbobin da ke fuskantar barazanar bacewa, Mr Farawo ya yi amannar cewa ana mantawa da al'ummomin da ke zaune a yankunan da ake adana dabbobin.

"Ba ko wanne lokaci ba ne ake samun mafita ga irin wadannan matsaloli a tarukan shan shayi," a cewar mai magana da yawun Zimparks a tattaunwarsa da BBC.

Zimbabwe za ta gabatar da wasu shawarwari da ke neman a sassauta haramcin kasuwancin zallan hauren giwa da kuma fatunta, tana mai cewa za a iya amfani da kudaden da aka samu idan an sayar da su wajen kara yawan giwaye.

'Ba ma bukatar taimako'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A watan Mayu, Zimbabwe ta gudanar da taro na kasashen Afirka sai dai ta gaza hada kan kasashen wajen haramta kasuwancin hauren giwa a duniya, kamar yadda dokar 1989 ta tanada.

Kasashen Zambia, Namibia da kuma Botswana ne kawai suka goyi bayan shirin Zimbabwe na neman izinin sayar da tarin hauren giwarta, wadanda aka samu galibi daga giwayen da suka mutu wadanda suka kai miliyoyin dalar Amurka.

"Ba ma bukatar taimako, muna bukatar samun damar yin kasuwancin [hauren giwa] ta yadda za mu samu kudin tafiyar da shirye-shiryenmu ," in ji Mr Farawo.

Sai dai kasar Kenya, wadda ke adawa da farautar giwaye da kuma sayar da haurenta, ba ta halarci taron ba.

Ta ƙona tarin hauren giwar da ta kwace daga masu farautar giwaye ba bisa ka'ida ba da kuma masu kasuwancinsu a 2016.

Yayin da Burkina Faso, Equatorial Guinea, Mali da kuma Senegal suka bayar da shawarwarin inganta yanayin giwaye a kudancin Afirka "da ke fuskantar barazanar karewa", lamarin da zai hana ci gaba da kasuwancinsu.

Jim Nyamu, shugaban cibiyar kare giwaye ta Elephant Neighbours Centre da ke Kneya, ya ce dage haramcin kasuwancin hauren giwa a kudancin Afirka zai yi tasiri a Gabashin Afirka, inda adadin giwaye yake sanya fargaba a zukatan jama'a.

Ya yi nuna da matakin da aka amince da shi na barin kasashen Botswana, Namibia da Zimbabwe su sayar da hauren giwa sau daya ga Japan da China a 1997 da 2008, yana mai cewa hakan ya sa an samu karuwar farautar hauren giwa ba bisa ka'ida ba.

Mugayen dabbobi

Ba a samu goyon baya kan wannan batu ba a Botswana, wadda ta koma farautar giwaye cikin wani yanayi mai cike da ce-ce-ku-ce a 2019 a matsayin wata hanya ta rageyawan giwaye daga adadinsu 130,000.

A lardin Chobe da ke kasar Botswana, wanda ke da makwabtaka da Zimbabwe, giwaye sun fi jama'a yawa inda suka kai 28,000. Kamar makwabtansu Hwange, ba a shinge gandun dabbobin yankin ba.

Wata sarauniya a lardin na Chobe, Rebecca Banika, ta shaida wa BBC cewa sun samu ribar $560,000 daga farautar giwaye a shekarar da ta gabata.

"Muna shan wahala amma ko da yake mun fusata, ba ma fada da dabbobi saboda muna samun wani alheri daga gare su," in ji ta.

Frank Limbo, mai shekara 64, wani tsohon ma'aikacin banki ne kuma a yanzu manomi ne, ya ce ganin hatsabiban dabbobi ba abu ne da aka saba da shi ba lokacin da yake matashi, amma yanzu lamarin ya zama ruwan dare a garin Kasane da ke lardin Chobe.

Giwaye uku sun kade Frank Limbo a 2015 - inda ya ji rauni a kafarsa
Bayanan hoto, Giwaye uku sun kade Frank Limbo a 2015 - inda ya ji rauni a kafarsa

Suna yawo a bayan gidajensu kuma sun kashe da dama daga cikin 'yan uwansa sannan suka cinye abincinsu wata rana da daddare.

Shi ne kadai ya sha da kyar a yayin farmakin da suka kai musu sau biyu.

A 2004 wata zakanya ta bi karensa da gudu a gonarsa, kuma shi kansa ta kai masa hari - sai dai ya tsira bayan wani abokinsa ya harbe ta da bindiga.

Shekaru goma sha daya bayan haka, a yayin da yake shirin yin shuka a gonarsa, wani garken giwaye ya fice ta gabansa. Jim kadan bayan haka uku daga cikinsu suka dawo suka kai masa hari.

Ya ruga a guje ya buya a bayan wata bishiya: "Ba su same ni ba amma daya daga cikinsu ta cije ni a gwiwata. Na yi tsammanin na mutu."