Liverpool ta yi wa Semenyo tayin fan miliyan 65, Tottenham na zawarcin Marmoush da Yildiz

Lokacin karatu: Minti 3

Fulham ta sake farfado da zawarcin da take yi wa dan wasa mai kai hari na PSV da kuma Amurka, Ricardo Pepi, mai shekara 22, wanda kungiyar ta Netherlands ta nemi a biya ta fan miliyan 40. (Mail)

Liverpool na shirin yin hammaya da Manchester City kuma za ta karfafa zawarcin da take yi wa dan wasan Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo da kudi fan miliyan 65. (Telegraph)

Bayern Munich ta bai wa Tottenham damar siyan dan wasan tsakiyar Jamus Leon Goretzka mai shekara 30. (Teamtalk)

Crystal Palace da Newcastle United na rige -rigen siyan dan wasan tsakiya na AZ Alkmaar Kees Smit, mai shekara 19, sai dai Real Madrid za ta iya kawo mu su cikas saboda ita ma tana son dan wasan. (Talksport)

Tottenham na neman sabon dan wasa mai kai hari a watan Janairu inda dan wasan Manchester City da Masar Omar Marmoush, mai shekara 26 da dan wasan Porto da Sifaniya Samu Aghehowa, mai shekara 21, da kuma dan wasan Juventus da Turkiyya Kenan Yildiz, mai shekara 20, ke cikin wadanda take son ta dauka. (Standard)

Sunderland na zawarcin dan wasan Lille Ayyoub Bouaddi, mai shekara18, da dan wasan Monaco Lamine Camara mai shekara 21. (Teamtalk)

Manchester City za ta sayar da Nathan Ake, mai shekara 30, a watan Janairu idan kudin da za a biya ya kai fan miliyan 2. (Sport )

Eintracht Frankfurt ta fara tattaunawa kan yuwuwar siyan dan wasan Nottingham Forest Arnaud Kalimuendo, mai shekara 23, wanda suke ganin zai iya zama zabi na biyu idan suka kasa cimma matsaya da dan wasan Newcastle United Will Osula, mai shekara 22. (Florian Plettenberg)

Ajax ta bayyana dan wasan Burnley Quilindschy Hartman, mai shekara 21, a matsayin daya daga cikin 'yan wasan da take son ta saya a watan Janairu. (Fabrizio Romano)

Liverpool na son ta sayi dan wasan tsakiyar Real Madrid Eduardo Camavinga, mai shekara 23 a kan fan miliyan 60 .(Fichajes )

Kungiyar Girona ta Serie A na sha'awar golan Barcelona, Marc-Andre ter Stegen bayan da Aston Villa ta fasa siyan dan wasan kasar Jamus. (Sport)

Real Madrid ba za ta bayar da aron dan wasan tsakiya Franco Mastantuono mai shekara 18 a watan Janairu ba saboda Xabi Alonso na son ya ci gaba da taka leda a kungiyar. (Fabrizio Romano)

Watakila West Ham ta bar dan wasan Brazil Lucas Paqueta ya bar kungiyar a watan Janairu idan ta samu tayin da ya dace da abin da take nema kan dan wasan mai shekara 28. (Football Insider)

Ana sa ran Chelsea za ta sayi sababbin 'yan wasa a bazara ciki har da dan wasan baya. (Standard)