Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barca na son haƙura da Guehi, Onana ya ce yana morewa a Trabzonspor
Barcelona ta gana da wakilan ɗanwasan baya na Crystal Palace Marc Guehi, amma batun kuɗin ɗanwasan ya sanyaya guiwarta kan buƙatar ɗanwasan na Ingila mai shekara 25. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Ɗanwasan Ingila na gaba Marcus Rashford, mai shekara 28 ya ce babban burinsa shi ne ci gaba da taka leda a Barcelona, bayan ya zo a matsayin aro daga Manchester United a bazara. (Sport, via Mirror)
Barcelona na son ɗauko matashin ɗanwasan gaba na Ingila Ajay Tavares, wanda zai cika shekara 16 a ranar 28 ga Disamba daga Norwich City. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Crystal Palace za ta yi hamayya da West Ham wajen ɗauko ɗanwasan gaba na Norway da Wolves Jorgen Strand Larsen a Janairu. (Telegraph, subscription required)
Roma na son ɗanwasan baya na Tottenham Radu Dragusin, mai shekara 23. (La Gazzetta dello Sport, via Football Italia)
Yayin da Antoine Semenyo ke shirin komawa Manchester City, Liverpool ta mayar da hankali kan ɗanwasan gaba na Paris St-Germain da Faransa Bradley Barcola. (CaughtOffside)
Golan Kamaru Andre Onana, mai shekara 29, ya ce yana more rayuwarsa tun da ya koma Trabzonspor a matsayin aro daga Manchester United. (Goal)
Bournemouth da Chelsea na ribibin ɗanwasan baya na Lazio da Spain mai shekara 25 Mario Gila. (Il Messaggero - in Italian)