Kone zai koma Man U, Chelsea da Leeds United na zawarcin McAtee

Lokacin karatu: Minti 2

Chelsea da Leeds United suna cikin kungiyoyin gasar firimiya da ke bibiyar halin da dan wasan tsakiya na Ingila, James McAtee mai shekara 23 ya ke ciki a Nottingham Forest. (Mail), external

Arsenal na tunanin daukar dan wasan AC Milan da Italiya Davide Bartesaghi mai shekara 19 .(Caughtoffside), external

Rahotani sun ce dan wasan tsakiya na Roma da Faransa Manu Kone, mai shekara 24, zai koma Manchester United a bazara mai zuwa.(Sportsmole), external

Tottenham na son ta sanya dan wasan Netherlands Micky van de Ven, mai shekara 24, a kwantaragi iri daya da na dan wasan Argentina kuma kyaftin din Spurs Cristian Romero, mai shekara 27. (Teamtalk), external

Dan wasan Brighton da Ingila Lewis Dunk, mai shekara 34, ya tsawaita kwantagarinsa da kungiyar na tsawon shekara guda. (Athletic - subscription required), external

Kocin Roma Gian Piero Gasperini ya tabbatar wa dan wasan Manchester United da Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 24 cewa yana da gurbi a cikin tsarin wasan sa na 3-4-2-1. (Gazzetta - in Italian), external

Nottingham Forest da Chelsea da Aston Villa duk suna zawarcin dan wasan Bologna dan kasar Argentina Santiago Castro mai shekaru 21. (Gazzetta dello Sport via Sport Witness), external

Oxford United na tunanin bai wa tsohon dan wasan bayan Chelsea John Terry aikin sa na farko a hukumar gudanarwa ta kungiyar .(Sun), external