Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afcon Morocco: Me kuke son sani kan wasan Super Eagles da Tunisia?
Super Eagles za ta buga wasa da Tunisia a karawa ta bibiyu a rukuni na uku ranar Asabar a gasar cin kofin Afirka da ake buga wa a Morocco.
Dukkan tawagaogin biyu na fatan kaiwa zagaye na biyu a babbar gasar tamaula ta Afirka da za su kece raini a Complexe Sportif de Fes in Fes.
Super Eagles ta yi nasarar doke Tanzania 2-1, yayin da Tunisia ta ci Uganga 3-1 a wasannin farko a karawar rukuni na uku.
Shin sau nawa kasashen suka fuskanci juna a tsakaninsu?
Haɗuwar farko tsakanin ƙasashen biyu an fara ne tun a 1961, lokacin da suka fafata gida da waje a matakin neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Afirka ta 1962.
Najeriya ta yi nasara a gida da ci 2–1, amma a Tunisiya, Najeriya ta fice daga fili domin nuna adawa yayin da aka tashi 2–2.
Daga baya aka yanke hukuncin bai wa Tunisiya nasara da ci 2–0, wadda ta samu nasara da cin 3–2 gida da waje.
Najeriya da Tunisiya sun haɗu a wasannin neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA sau huɗu, wato a 1978 da 1982 da 1986 da kuma a 2010.
A neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya a 1978, Najeriya da Tunisiya sun hadu a zagayen ƙarshe na tantancewa a rukuni mai ɗauke da ƙasashe uku, wanda ya haɗa har da Masar.
Najeriya ta tashi ba ci 0-0 a gidan Tunisiya, kafin Tunisiya ta doke Super Eagles da ci 1–0 a Legas, hakan ya sa ta ta zama ta ɗaya a rukuni kuma ta samu tikitin shiga gasar.
A neman shiga Gasar Cin Kofin Duniya a 1982 kuwa, Tunisiya da Najeriya sun hadu a zagayen farko, inda kowacce ta ci wasan gidanta 2–0.
Daga nan Najeriya ta yi nasara a bugun fenariti da ci 4–3, duk da cewa babu wacce daga cikinsu ta samu shiga gasar ƙarshe da aka yi a Sifaniya.
A neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya a 1986, tawagogin sun fafata a zagaye na uku a wasa biyu.
Najeriya ta ci 1–0 a gida, yayin da Tunisiya ta ci 2–0 a Tunis, kenan ta yi nasara 2-1 gida da waje, hakan ya sa ta tsallaka zuwa zagayen ƙarshe na tantancewa, sai dai daga baya ta kasa samun shiga gasar kofin duniya.
Bayan sun haɗu a neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya guda uku a jere (1978 da1982 da kuma 1986), Tunisiya da Najeriya sun sake haɗuwa a zagaye na uku a tantancewar shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta 2010, wanda kuma hanyar neman gurbin shiga gasar AFCON a 2010 kenan.
Najeriya ta zama ta ɗaya a rukunin, bayan canjaras biyu: 0–0 a Tunisiya da 2–2 a Najeriya, ta haka ta samu cancantar shiga Gasar Cin Kofin Duniya.
Tunisiya ta zo ta biyu da tazarar maki ɗaya kacal a bayan Najeriya, amma ta samu gurbin shiga AFCON 2010.
Najeriya da Tunisiya sun hadu sau shida a baya a wasannin Gasar Cin Kofin Afirka. Najeriya ta samu nasara uku, Tunisiya sau ɗaya, yayin da wasa biyu suka yi canjaras a 2004 da 2006, inda aka yi bugun fenariti, kowacce ƙasa ta samu nasara ɗaya.
Haduwarsu ta farko a wasannin AFCON shi ne a 1978, a wasan neman matsayi na uku.
An bai wa Najeriya nasara da ci 2–0, bayan Tunisiya ta fice daga fili yayin da aka tashi 1–1.
Sun sake haɗuwa a wasan farko a rukuni a AFCON 2000, inda Najeriya ta yi nasara cin 4–2, duk da cewa dukkan tawagar biyu sun tsallaka daga rukuni.
Babban kocin Tunisiya na yanzu, Sami Trabelsi, ya taka leda a wancan wasan a rukuni na hɗ da aka buga a Legas ranar 23 ga Janairu, 2000.
A matsayin mai masaukin baki a 2004, Tunisiya ta haɗu da Najeriya a wasan daf da na ƙarshe. Jay-Jay Okocha ne ya ci wa Najeriya ƙwallon, kafin Khaled Badra ya farke wa Tunisiya. Wasan an tashi 1–1, inda Tunisiya ta yi nasara da ci 5–3 a bugun fenariti.
A 2006 kuma, ƙasashen biyu sun haɗu a wasan daf da na kusa da ƙarshe (kwata fainals). Victor Obinna ne ya ci wa Najeriya ƙwallon, daga baya Karim Haggui ya farke wa Tunisiya, wasan ya tashi 1–1, daga baya Najeriya ta yi nasara da ci 6–5 a bugun fenariti.
Sun kuma haɗu a wasan neman matsayi na uku a AFCON 2019, inda Najeriya ta yi nasarar cin 1–0 sakamakon ƙwallon da Odion Ighalo ya zura a raga.
Haduwarsu ta baya-bayan nan ita ce a AFCON 2021, inda Tunisiya ta doke Najeriya da ci 1–0 a zagayen ƴan 16, inda Youssef Msakni ne ya ci ƙwallon kaɗai a minti na 47.
Wasannin da aka buga tsakanin Najeriya da Tunisia:
Sun fuskanci juna sau 21 jimilla, inda Najeriya ta ci wasa biyar, Tunisia ta yi nasara shida da canjaras 10, Najeriya ta ci ƙwallo 21 aka zura mata 26 a raga a tsakaninsu.
Wannan shi ne karo na bakwai da za su kara a Afcon:
Najeriya ta samu nasara uku, Tunisia tana da ɗaya da canjaras biyu, Super Eagles ta ci ƙwallo tara aka zura mata biyar a raga a tsakaninsu.
Tarihin fafatawar da suka yi a Afcon:
Ranar 16 ga watan Maris 1978, Accra
- Najeriya 2-0 Tunisia
Super Eagles ce ta yi ta uku, wadda aka baiwa ƙwallo 2-0, bayan da Tunisia ta ƙi karasa wasan tun daga minti na 42 a lokacin suna 1-1.
Ranar 23 ga watan Janairun 2000, Legas wasan cikin rukuni
- Najeriya 4-2 Tunisia
Ranar 11 ga watan Fabrairun 2004, Radès (Zagayen daf da karshe)
- Tunisia 1-1 Najeriya
(Tunisia ta yi nasara 5–3 a bugun fenariti)
Ranar 4 ga watan Fabrairun 2006, Port Said (Zagayen kwata-fainals)
- Najeriya 1-1 Tunisia
(Najeriya ta yi nasara 6–5 a bugun fenariti)
Ranar 17 ga watan Yulin 2019, Cairo (Wasan neman mataki na uku)
- Tunisia 0-1 Najeriya
(Ighalo ne ya ci ƙwallon a minti na uku da take leda)
Ranar 23 ga watan Janairun 2022, Garoua (Zagayen tawaga 16)
- Najeriya 0-1 Tunisia
(Msakni ne ya ci ƙwallon a minti na 47)
Bajintar da Najeriya ke yi a Afcon
- Super Eagles ta fara da cin Tanzania 2–1 a wasan farko a rukuni a Morocco.
- Kenan karo na 14 da take fara yin nasara a wasan farko a cikin rukuni a Afcon.
- Ba a doke Najeriya ba a wasa bakwai baya a cikin rukuni a Afcon, ta yi nasara shida da canjaras ɗaya, tun bayan da Madagascar ta yi nasara a kanta a 2019.
- Super Eagles ta yi nasara uku a Afcon a karawar cikin rukuni da cin kodai ƙwallo ɗaya ko tazarar ɗaya.
- Najeriya ta fara da cin wasa biyu a jere a cikin rukuni da fara Afcon a 2021, irin bajintar da ta yi a 2019 kenan.
- Wasa ɗaya ne aka doke Super Eagles daga 15 baya a zagayen cikin rukuni a Afcon shi ne 2-0 da Madagascar ta yi nasara a 2019.
- Najeriya ta zura ƙwallo a raga a wasa bakwai a fafatawar cikin rukuni a Afcon.
- Karawa biyu ce kacal Super Eagles ba ta zura ƙwallo ba a raga a bayan nan daga wasa 26 a Afcon, shi ne a hannun Madagascar a 2019 da kuma Tunisia a 2021 a zagayen ƴan 16.
- Semi Ajayi ya ci ƙwallonsa ta farko a Afcon a karawa da Tanzania, kuma wasa na 10 da ya buga kenan.
- Ademola Lookman ne ya ci wa Super Eagles na biyu a wasan Tanzania, kuma na huɗu kenan da ya zura a raga a Afcon.
- Ƙwallon da Lookman ya ci ya zama na biyu da ya zura a raga daga wajen da'ira a karon farko a Afcon tun bayan wadda Emmanuel Emenike ya ci Mali a 2013 a zagayen daf da karshe.
- Alex Iwobi ne ya bayar da ƙwallo biyun da Super Eagles ta ci Tanzania, karon farko da ya yi wannan bajintar a Afcon a fafatawarsa ta 19.
- Kenan Iwobi ya ƙirƙiri dama 18 a gasar cin kofin Afirka.
- Victor Osimhen ya nemi ragar Tanzania karo bakwai, hare-hare mai yawa da ɗan Najeriya ya yi kenan a Afcon tun bayan Victor Obinna a karawa da Algeria a wasaneman matakin na uku a 2010.
- Wasa shida da Najeriya ta ci a karawar takwas a cikin rukuni tana yin nasara da tazarar ƙwallo ɗaya har da karo biyar da take cin 1-0.
- Super Eagles ta ci ƙwallo 13 a wasa 14 baya a Afcon.
- A karawa da Tanzania Najeriya ta raba ƙwallo ta bani in baka sau 451 daga 501.
- Kuma Alex Iwobi da Calvin Bassey suke kan gaba a raba ƙwallayen har sau 71 kowanne.
- Najeriya ta kai hari 11 da suka nufi ragar Tanzania, kuma Osimhen yana da uku daga ciki.
- Samuel Chukwueze ya yi yanka sau10 a fatawa da Tanzania, kuma shida daga ciki ya yi nasara ba tare da an ɓata ƙwallon ba.
Ƙwazon da Tunisia take yi a Afcon
- Tunisiya ta fara gasar da nasara 3–1 a kan Uganda.
- Ellyes Skhiri ne ya ci kwallon farko a Tunisiya, wadda ita ce ta 100 da suka ci a wasannin AFCON.
- Tunisiya ta zama kasa ta shida da ta kai ga zura kwallaye 100 a raga a AFCON, daga baya Aljeriya ta zama ta bakwai da yin wannan bajintar.
- Ƙwallon da Skhiri ya ci bayan minti 10 na nufin cewa Masar ta ci (22) da Najeriya (16) kaɗai ne suka fi Tunisiya mai (12) yawan cin ƙwallaye a cikin minti 10 da farko wasa a AFCON.
- Wannan shi ne karon farko da Tunisiya ta ci ƙwallo a cikin minti 10 na farko da fara wasan farko a rukuni tun lokacin Issam Jemâa a karawa da Senegal a 2008.
- Skhiri ya ci ƙwallonsa ta farko a AFCON ne a wasansa na 16 a gasar.
- Elias Achouri ya ci ƙwallo ta huɗu da ta biyar a tarihin wasanninsa a Tunisia.
- Achouri ya zama ɗan Tunisiya na farko da ya ci ƙwallo biyu a wasa ɗaya a AFCON tun bayan Wahbi Khazri a fafatawa da Mauritania a 2021.
- Nasarar da suka samu a kan Uganda ta kawo ƙarshen wasa huɗu ba tare da nasara ba ga Tunisiya a AFCON, wadda ta yi canjaras biyu aka doke ta biyu daga ciki.
- Haka kuma ta kawo ƙarshen wasa huɗu ba tare da nasara ba a wasannin rukuni a AFCON, tun bayan da ta doke Mauritania a 2021.
- Tunisiya ta lashe wasan buɗe gasar AFCON karo na farko tun 2013, bayan da ta kasa yin hakan a wasannin buɗe gasar guda biyar da suka gabata.
- Sau uku kacal Tunisiya ta fara AFCON da nasara biyu a jere, wato a gasar da aka buga a 2004 da 2006 da kuma ta 2012.
- Karon ƙarshe da Tunisiya ta fara AFCON da nasara biyu a jere shi ne a 2012, inda ta doke Morocco da Niger da ci 2–1 kowanne.
- Tunisiya ba ta sha kashi ba a wasan rukuni karo biyar a Afcon, wadda ta ci wasa uku da canjaras biyu daga ciki.
- Karon ƙarshe da ta sha kashi a wasa na biyu a rukuni shi ne a 2013, inda Côte d'Ivoire ta doke ta 3–0.
- Karon ƙarshe da Tunisiya ta ci wasan farko a cikin rukuni, amma ta kasa tsallakawa zuwa zagaye na biyu shi ne a 2013.
- Hannibal Mejbri, wanda ya taimaka aka ci ƙwallon farko a kan Uganda, ya samar da damar cin guda huɗu, mafi yawa a wasan da suka buga na farko a Afcon.
- Montassar Talbi ne kan gaba a yawan raba ƙwallo (51) kuma (48) sun je inda ake bukata a wasan da suka kara da Uganda.