Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Kuɗin aikin Hajjin 2025 ka iya kai wa miliyan 10 ko fiye'
Masana harkar aikin Hajji a Najeriya sun fara tsokaci dangane da makomar cire hannun gwamnati daga aikin hajjin 2025.
Hukumar aikin Hajji ta Najeriya dai, NAHCON ta ce gwamnatin tarayya ba za ta iya ci gaba da biyan tallafi a aikin hajjin 2025 ba.
Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da mai magana da hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar, inda ta ce "An daina bai wa jama'a tallafin rangwamen farashin dala ga maniyyata a jihohi da tarayya."
Da ma dai gwamnati na ba da tallafin ne ta hanyar karyarwa da maniyyata farashin dala a babban bankin Najeriya.
Ko a aikin hajjin bara ma, bayanai sun nuna yadda gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin tsabar kuɗi har naira biliyan 90 domin gudanar da aikin ibadar ba tare da tsawwalawa ba.
Me hakan yake nufi?
Alhaji Nasidi Yahaya Sulaiman wani masanin harkokin aikin Hajji da Umra ya ce abin da hakan yake nufi shi ne farashin aikin hajji a shekarar 2025 zai fi na kowace shekara.
"Ya danganta da farashin dala tunda farashinta ba a tsaye yake ba. Kenan idan aka tafi a farashin da take kai a yanzu kuɗin kujerar zai iya kai wa naira miliyan 10. Zai ma iya fin hakan idan dalar ta tashi. Misali idan farashin dalar ya kai naira 2000 kamar yadda muka gani a baya to farashin kujerar aikin Hajjin ka iya fin naira miliyan 10."
Alhaji Nasidi ya ƙara da cewa "lallai wani abun da hakan yake ƙara fitowa da shi fili shi ne za a samu raguwar matafiya aikin hajjin. Idan mutum dubu 100 sun je aikin Hajji daga Najeriya to yanzu sai dai dubu 50."
A yanzu dai hukumar aikin Hajjin ta Najeriya, NAHCON ba ta fitar da kuɗin aikin hajjin shekara mai zuwa ba, amma hukumomin alhazan jihohi sun fara sanar da kuɗin ajiya, inda da dama suka nemi a fara ajiye naira miliyan 8.5.
Mece ce mafita?
Alhaji Nasidi Yahaya Sulaiman ya ce da ma ƙasashen duniya ba sa biyan tallafi a aikin Hajji. Ƴan ƙasa ne suke ɗaukar nauyin kansu da kansu.
To sai dai ya bayar da shawarwari guda biyu da ya ce za su zama mafita ga ƴan Najeriya kamar haka:
- Aikin Hajji na mai hali ne: Ya kamata al'ummar Musulmin Najeriya su fahimci cewa shi aikin Hajji fa kamar yadda Allah ya ce na mai hali ne. Idan ba haka da hali babu takura kai. Babu matsawa kai domin a tafi aikin Hajji.
- Asusun adashin gata: Ya kamata hukumar aikin Hajjin Najeriya, NAHCON ta farfaɗo da tsarin nan na asusun aikin hajji, inda maniyyata ke kwashe shekaru suna ajiya a asusun har zuwa lokacin da kuɗinsu za su kai yawan da ake so domin tafiya ƙasa mai tsarki.