PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen jihar Ondo

Asalin hoton, @OfficialPDPNig
Jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben jihar Ondo, bayan hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Gwamna Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben.
PDP ta ce za ta garzaya kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar.
Muƙaddashin hulda da manema labarai na Jam’iyyar PDP ya yi zargin cewa an tafka magudi da amfani da karfin tsiya aka kada dan takararsu Mr. Agboola Ajayi.
Hakan na zuwa ne bayan wasu korafe-korafe da wakilin jam’iyyar PDP na karamar hukumar Idanre ya yi zargin cewa ba a yi zabe a unguwar Ofosun Oniseri ba, yayin da aka kori ƴan PDP, aka ƙwace ƙuri’u a Alade.
Alhaji Abdullahi Ibrahim ya yi zargin cewa zaben ya saɓa wa tsarin dimokuradiyya inda ya ce za su dauki mataki na gaba.
"Za mu garzaya kotu a matsayinmu na jam'iya, da muke sukar lamirin wannan zaɓe, mun yi tir da Allah wadai da hukuncin da hukumar zaɓe ta bayar."
Tuni jam'iyyar PDP ta ce za ta yi nazari kan zaben da kuma sakamakonsa kafin ɗaukar mataki na gaba kan abin da ta kira kare dimokuraɗiyya a Najeriya.
Martanin APC
Da yake mayar da martani, Daraktan watsa labarai na jam’iyyar APC, Malam Bala Ibrahim, ya bayyana cewa nasarar da jam’iyyarsu ta samu ya nuna farin jininsu da kasancewar jama’a sun yi na’am da kyawawan ayyukansu ne a jihar.
Ya ce zafin shan kaye ne ke damun PDP, domin a cewarsa ta saba yin ƙorafi bayan zaɓe.
"Ƙorafi da jam'iyar PDP ke yi daman wannan ba sabon abu ba ne, duk lokacin da aka yi zaɓe aka kada ita, kullum tana ɗora alhakin hakan ne kan jam'iyar APC."
Babban jami'in tattara sakamakon, Farfesa Olayemi Akinwunmi, shugaban jami'an gwamnatin tarayya da ke Lokoja, ya ce Aiyedatiwa ya smu ƙuri'a 366,781, yayin da Agboola Ajayi na PDP ya samu ƙuri'a 117, 845, sai jam'iyyar LP da ta samu ƙuri'a 1,162.
Jam'iyyu 18 ne suka fafata a zaɓen na Ondo, sai dai fafatawar ta fi zafi ne tsakanin 'yan takara biyu, wato gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa na APC da Agboola Ajayi na PDP.
Wakilin BBC da ke birnin Akure ya ce an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana, kuma babu labarin wani tashin hankali a sassan jihar a yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen.
Ana kallon sake zaben Aiyedatiwa a matsayin kara karfin jam’iyyar APC a jihar. Aiyedatiwa dai na fuskantar kalubalen hada kan jihar musamman bayan zaben da aka yi ta cece-kuce.











