Su wane ne za su fafata a zaɓen gwamnan jihar Ondo?

'Yantakara

Asalin hoton, @LuckyAiyedatiwa, @Iwillvote Sola Ebiseni, @A_AgboolaAjayi, @Abbas Mimiko/Facebook/X

Lokacin karatu: Minti 5

A ranar Asabar ne za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Ondo da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Jihar Ondo na daga cikin jihohin ƙasar ba a gudanar da zaɓukansu lokaci guda da na sauran jihohi.

Zaɓen na zuwa ne wata 11 bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, wanda ya shafe tsawon lokaci yana da fama da jinya.

Hukumar zaɓen ƙasar, INEC ta ce mutum miliyan 2,053,061 ne suka yi rajistar zaɓe a faɗin jihar, yayin da matasa ke da kasi 35.41 cikin 100 na waɗanda suka yi rajistar zaɓen.

Kammala yaƙin neman zaɓe

Tuni dai manyan jam'iyyun siyasar jihar ke ta kokawar yaƙin neman zaɓe domin farauto ƙuri'un masu zaɓe.

A ranar Laraba ne jam'iyyar APC mai mulkin jihar ta ƙarƙare yaƙin neman zaɓenta a babban filin wasa na Akure, babban birnin jihar.

Inda manyan jiga-jigan jam'iyyar na ƙasa ciki har da mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje da wasu gwamnonin APC da ministoci da wasu 'yan majalisar dokokin ƙasar suka halarta.

Daraktan yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Ondo na jam'iiyar APC, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya yi kira ga al'ummar jihar su mara wa jam'iyyarsa baya a zaɓen da ke tafe.

Ita ma babbar jam'iyyar hamayyar jihar, wato PDP a yau Alhamis ne za ta ƙarƙare nata yaƙin neman zaɓen a birnin Akuren, kamar yadda jam'iyyar ta wallafa a shafinta na X.

Cikin wata sanarwar da sakataren yaƙin neman zaɓen jam'iyyar a zaɓen jihar, Princess Bunmi Oguntibeju ya fitar, ya ambato daraktan yaƙin neman zaɓen jam'iyyar a zaɓen, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke, na gayyatar shugaban riƙo na jam'iyar Amb. Ilya Damagum da tsoffin shugabannin ƙasar da mataimakansu ('yan jam'iyyar).

Sanarwar ta kuma gayyaci duka gwamnonin jam'iyyar da mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar da 'yan majalisar dokokin jam'iyyar da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da su halarci gangamin rufe yaƙin zamen zaɓe a yau Alhamis.

Fafatawa tsakanin tsoffin mataimakan gwamna

Duka manyan 'yan takara biyu a zaɓen, tsoffin mataimakan tsohon gwamnan jihar, marigayi Rotimi Akeredolu ne.

Agboola Ajayi na jam'iyyar PDP da Lucky Aiyedatiwa na APC mai mulkin jihar sun yi wa marigayi Akeredolu mataimaki a wa'adin mulki daban-daban.

Ajayi ne ya fara yi masa mataimaki a wa'adin mulkinsa na farko daga 2016 kafin wani saɓani ya shiga tsakaninsu a 2020.

Lamarin da ya sa suka raba gari a 2020, inda har Ajayi ya tsaya takara a zaɓen 2020 a jam'iyyar hamayya ta ZLP.

Bayan samun saɓani tsakanin Akeredolu da Ajayi a 2020, a wa'adinsa na biyu ya ɗauki Aiyedatiwa a matsayin mataimaki.

Daga baya kuma Aiyedatiwa shi ma ya riƙa samun saɓani da Akeredolu a lokacin rashin lafiyarsa, lamarin da har ta kai ga fadar shugaban ƙasa kiran duka ɓangarorin biyu domin yi musu sulhu.

'Yan sanda sun sanar da dokar taƙaita zirga-zirga

Babban sifeton 'yansandan ƙasar, Kayode Egbetokun, ya sanar da dokar taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a kan tituna da ruwa da sauran hanyoyin sufurin jihar daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa ƙarfe 6:00 na maraice a ranar zaɓen.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yansandan ƙasar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar ranar Alhamis ya ce dokar taƙaita zirga-zirga na daga cikin matakan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a lokacin zaɓukan.

To sai dai dokar ta keɓe masu muhimman ayyuka kamar motocin ɗaukar marasa lafiya da jam'ian kashe gobara da 'yanjaridar da aka tantance.

Haka kuma babban sifeton 'yansandan ya hana jami'an 'yansanda raka manyan mutane zuwa rumfunan zaɓe da wuraren tattara sakamakon zaɓe.

Manyan 'yan takara

Lucky Aiyedatiwa na APC

Lucky Orimisan Aiyedatiwa

Asalin hoton, @LuckyAiyedatiwa/X

An haifi Lucky Aiyedatiwa a garin Obe-Nla na yankin ƙaramar hukumar Ilaje ranar 12 ga watan Janairun 1965.

Ya samu shdar babbar diploma a jami'ar Ibadan a shekarar 2001.

Sannan a shekarar 2013 ya samu shaidar digiri na biyu a fannin kasuwanci a jami'ar Liverpool da ke Birtaniya.

Bayan zamansa mataimakain gwamna a 2020, ya taɓa riƙe muƙamin maƙaddashin gwamnan jihar a lokacin da Rotimi Akeredolu ke jinyar cutar kansa.

Lucky Aiyedatiwa ya ce idan an zaɓe shi, zai mayar da hankali kan samar da tsaro da tsaron kan iyakokin jihar da inganta tattalin arziki da noma da samar da abubuwan ci gaba da gina matasa da ilimi da tallafa wa mata.

Agboola Ajayi na PDP

Agboola Ajayi

Asalin hoton, @A_AgboolaAjayi/x

Shi ne tsohon mataimakin Akeredolu a wa'adin farko, kafin daga baya ya koma jam'iyyar ZLP bayan tsamin dangantaka da ubangidan nasa.

An haifi Agboola Alfred Ajayi ranar 24 ga watan Satumban 1968 a karamar hukumar Ese-Odo.

Ya samu digirinsa na farko a fannin shari'a a jami'ar Igbinedion, Okada da ke jihar.

Dan takarar mai shekarar 54 ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumarsa.

Mista Ajayi ya ce zai mayar da hankali kan manyan manufofi bakwai idan an zaɓe shi.

Manufofin sun haɗa da samar da tsaro da noma da inganta lafiya da ilimi da masana'antu da inganta sufurin jiragen ruwa da raya karkara da muhallai da matasa da wasanni da tallafa wa mata da ma'aikatan gwamnati.

Sola Ebiseni na LP

Sola Ebiseni na LP

Asalin hoton, @Iwillvote Sola Ebiseni/facebook

An haifi Ebiseni ranar 1 ga watan Oktoban 1960, a jihar Ogun, amma iyayensa 'yan asalin Ilaje ne a jihar Ondo.

Ya karanta sashen shari'a a jami'ar Nsukka, inda ya fara shiga harkokin siyasar makaranta ta SUG a 1980.

Mista Sola Ebiseni ya taɓa riƙe muƙamin kwamishina a jihar lokacin tsohon gwamnan jihar Olusegun Mimiko, kafin daga baya ya fice daga PDP zuwa LP.

Fitaccen lauyan ya ce zai mayar da hankali kan samar da ilimi kyauta da walwalar al'umma da ayyuka da haihuwa kyauta ga mata da inganta tattalin arzikin jihar.

Abbas Mimiko na ZLP

Abbas Mimiko na ZLP

Asalin hoton, @Abbas Mimiko/Facebook

Abbas Mimiko, ƙanin tsohon gwamnan jihar ne Olusegun Mimiko.

Likitan halayyar ɗan'adam ɗin shi ne ke yi wa jam'iyyar ZLP takara a zaɓen gwamnan jihar.

Ya kuma ce zai mayar da hankali ka wasu manyan ƙudurori bakwai da suka haɗa da wadatuwar abinci da tsaftataccen ruwan sha da samar da arziki da ilimi, da samar da gidaje da inganta lafiya ƙari kan samar da zaman lafiya ta tsaro.

Sauran 'yan takara

  • Falaiye Abraham Ajibola - A
  • Akinuli Fred Omolere - AA
  • Ajayi Adekunle Oluwaseyi - AAC
  • Nejo Adeyemi - ADC
  • Akinnodi Ayodeji Emmanuel - ADP
  • Popoolqa Olatunji Tunde - APGA
  • Ogunfeyimi Isaac Kolawole - APM
  • Fadoju Amos Babatunde - APP
  • Olugbemiga Omogbemi Edema - NNPP
  • Ajaunoko Funmilayo Jenyo - NRM
  • Alli Babatunde Francis - PRP
  • Akingboye Benson Bamidele - SDP
  • Adegoke Kehinde Paul - YP
  • Akinmurele John Otitoloju - YPP