Ubangidan ƴan siyasar da zai jagoranci Najeriya

Asalin hoton, AFP
An ayyana Bola Tinubu, mai shekara 70 a duniya a matsayin mutumin da ya ci zaɓen Najeriya mafi zafi tun bayan mulkin sojoji a 1999.
Tinubu, wanda ake kallo a matsayin jajirtaccen ɗan siyasa da ya kawo ci-gaba a jihar Legas - cibiyar kasuwancin ƙasar, ya yi nasara ne kan babbar Jam'iyyar hamayya mai fama da ɓaraka da kuma ɗan takara na uku da ke da magoya bayan matasa.
A ranar 29 ga watan Mayu, na wannan shekara ta 2023, zai maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari a kan mulki.
Najeriya - ƙasa mafi yawan al'umma a Afirka na fuskantar ƙalubalen da suka haɗa da matsalar tattalin arziƙi da matsalar tsaro da kuma hauhawar farashin kayan masarufi.
Da yawa na fatan Tinubu ya fara aiki a ƙasar ba tare da ɓata lokaci ba.
Mutumin da ya taɓa tserewa gudun hijira a lokacin mulkin sojin marigayi Sani Abacha, Tinubu ya san darajar ‘yanci, shi ya sa yake ɗaukar shi a matsayin abu mai muhimmanci.
Ƙwararre kan gudanarwar tattalin arziƙi, yana cikin ƙungiyar nan mai rajin kare demokuraɗiyya da ake kira (Nadeco), kuma wannan ne mafarin rikicinsu da Abacha.
Ƙoƙarin irin waɗannan ƙungiyoyin irin su Nadeco da kuma mutuwar Abacha a 1998, suna cikin abubuwan da suka haifar da dawowar demokuraɗiyya a 1999 ta hanyoyi da dama.
Tinubu yana jin cewa yana da haƙƙin shugabancin Najeriya.
Mutumin wanda mafiya yawan magoya bayansa ke kira da laƙabinsa na sarautar gargajiya, “Jagaban”, ya ce, yanzu zai duƙufa fara aikin haɗa kan Najeriya - wata ƙasa da ta samu rabuwar kai ta ɓangaren yankuna da addini, kamar yadda sakamakon zaɓen ƙasar ya nuna.
Amma wannan aikin da ke gabansa ba zai tsorata shi ba, saboda ya yi makamancinsa lokacin da yake gwamnan Legas tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 abin da ya ƙara haskaka shi ke nan a siyasa.
A lokacin shugabancinsa, Legas ta samu kuɗaɗe masu yawa saboda masu zuba jari na ƙasashen ƙetare.
Ya kuma fito da tsarin sufuri da ya bai wa masu mota damar zuwa inda za su cikin gaggawa, sannan ya rage mummunan cunkoson ababen hawan da ake fama da shi a jihar.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amma duk da wannan, birnin mai mutane miliyan 25 har yanzu bai kai matuƙarsa ba duk da iƙirarin cewa sun kai shi haka.
Yawancin manyan ayyukan birnin duk sun lalace – abubuwan more rayuwa irin su ruwa da gidaje su ma sun taɓarɓare.
Sai kuma tashar jirgin ƙasa mai amfani da lantarki da aka fara a lokacinsa har yanzu ba a gama ba kusan shekara 20 duk da arziƙin da jihar ke samu.
Ana zargin sa da sanya idanu kan abin da jihar ke samu duk da ya bar mulkinta tun 2007.
Dukkan gwamnan da ya gaje shi dole ya zama tamkar ɗalibinsa “ya kuma bi sawunsa.”
Duk wanda ya yi ƙoƙarin fanɗarewa nan da nan sai a yi waje da shi, tare da taimakon mambobin kungiyar sufuri da suke da tasirin gaske.
Akwai kuma zarge-zargen da ake masa sai dai ya sha musanta su.
Shekaru biyu baya, Dapo Apara wani akawu a kamfanin Alpha-beta, wani kamfani da Tinubu ke da hannun jari mai yawa ta dalilin abokansa, ya zarge shi da amfani da kamfanin wajen halasta kuɗin haram, da kuɗin bogi da ƙin biyan haraji da sauran zarge-zargen cin hanci da rashawa.
An shigar da Tinubu ƙara duk da cewa shi da Alpha_beta sun musanta zarge-zargen sai dai duka ɓangarorin biyu sun amince su daidaita tsakaninsu a wajen kotu a watan Yunin da ya gabata.
Waɗannan zarge-zarge da aka riƙa yi masa sun sanya abokan takarar Tinubu ganin cewa ba shi ba ne mutumin da ya dace da jagorancin Najeriya, ƙasar da harkokin cin hanci ke da wurin zama.

End of Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:

A zaɓen da ya gabata, an ga wata motar banki da ta kai kuɗi gidansa da ke Ikoyi a Legas, wanda hakan ya janyo zargin da ake masa na zai sayi ƙuri’a ne lokacin zaɓe, babu dai wani mataki da ya ɗauka na musanta hakan.
“Idan ina da kuɗi, idan ina so, zan iya raba wa mutane su baki ɗaya, matukar ba ƙuri’unsu na saya ba,” in ji shi
Yana ɗaya daga cikin ‘yan siyasar Najeriya masu kuɗi, sai dai kuma akwai tambaya kan dukiyar tasa.
A watan Disamba, ya shaida wa BBC cewa ya gaji wasu daga cikin rukunin gidajen da yake da su waɗanda ya zuba wa jari, amma a baya ya ce ya zama ‘miloniya ne a dare ɗaya’ yayin da yake aiki da mujallar Deloitte & Touche.
Ya ce ya tara dalar Amurka miliyan 1.8 daga albashinsa da sauran alawus-alawus, kwatankwacin wannan adadin aka samu a asusunsa a 1993 abin da ya janyo rikicinsa da hukumomin Amurka.
A wasu bayanai da hukumar tsaro ta Amurka ta wallafa ta ce, daga farkon 1988, an gano wani asusu da aka buɗe da sunan Bola Tinubu ana zuba kuɗin da aka sayar da hodar ibilis a cikinsa.
Kevin Moss, wani babban jami’i da ya ja ragamar binciken, ya yi zargin Tinubu yana wa wani mutum da suke zargi aiki, wanda ake kira Adegoboyega Akande.
Tinubu ya riƙa fuskantar tambayoyi game da lafiyarsa, abin da ya sa ya wallafa wani hoton bidiyo na minti ɗaya da dakiƙa takwas wanda a cikinsa yake tuƙa keken atisaye domin nuna wa duniya cewa lafiyarsa ƙalau.
Abokan hamayyarsa sun ce shekaru sun cimmasa inda suka riƙa wallafa wasu hotunan bidiyoyi da ke nuna shi yana magagi a wajen yaƙin neman zaɓe, abin da yake faɗa ba a fiye ganewa ba.
Da yawan ‘yan Najeriya na nuna damuwa kan matsalar rashin lafiya bayan shugaban da aka taɓa yi mai irin wannan matsalar Umaru Musa ‘YarAdua da ya rasu yana kan mulki a 2010.
Shi ma Shugaba Buhari da yake mulki ya ɗauki lokaci yana fama da rashin lafiya, abin da ya riƙa sanya shi tafiya Turai neman magani akai-akai
Sai dai mabiyansa na cewa yana da ƙwarewar aiki, kuma shugabanci ba tsere ba ne balle a bar shi a baya.

Asalin hoton, AFP
Yayin yaƙin neman zaɓe, an yi ta samun faɗi-tashi game da wanda za su yi takara tare.
Tinubu wanda Musulmi ne daga kudanci, ya ɗauki tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima daga arewaci a matsayin mataimakinsa.
An riƙa yi wa hakan kallon birgewa da neman janyo Musulman da ke yankin arewacin Najeriya waɗanda suke da masu zaɓe da yawa a ƙasar.
Hakan ya janyo ce-ce-ku-ce daga Kiristocin Najeriya da suka ce hakan ya ci karo da yadda aka saba, na haɗa waɗanda ba addinansu ɗaya ba takarar shugabancin Najeriya.
Ya kare matsayarsa kan cewa ya ɗauke shi ne domin cancanta ba wai domin abin da mutane ke so ba.
Ana masa kallon “ubangida” a siyasar kudu maso yammaci kuma mafi ƙarfin faɗi-a-ji, domin shi ne ke faɗin yadda za a yi da iko tsakanin yaransa.
A 2015, ya bayyana kansa a matsayin “ƙwararren mafarauci” kuma shi ne ke kai “ƙwararru ofis.”
Ƙarfin ikonsa ya kai ga yin gamayyar jam’iyyun ‘yan hamayya a 2013 wanda a ƙarshe suka ƙwace iko daga hannun jam’iyya mai mulki ta PDP a 2015 – wani abu da bai fiye faruwa ba a mulkin Najeriya a kayar da shugaba mai mulki.
A lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyarsa, yayin da Tinubu ya nuna buƙatarsa ta tsayawa takarar, ya tunasar da ‘yan Najeriya da bugun ƙirji cewa shi ne ya kawo Shugaba Buhari ga shugabancin Najeriya, bayan tsohon shugaban sojin ya yi ta ƙoƙarin samun nasara amma yana faɗuwa.
Shi ya sa magoya bayansa da dama ke kallon mataimakin Buhari Yemi Osinbajo a matsayin wanda ya yi butulci, saboda a baya ya yi wa Tinubu kwamishina kuma ya zo yana neman karawa da shi a takarar shugaban Najeriya.
Da wannan nasara da ya samu akwai matsalolin da ke gabansa waɗanda dole ya yi aiki a kansu da Buhari ya bari bai yi ba.
Misali, matsalar tsaro da rashin aikin yi da hauhawar farashin kayayyaki ga kuma rabe-raben da ake samu ta ɓangaren ƙabilanci.
Ba wani aiki ba ne da ke da wuya, amma aiwatarwar kan zama mai wuya.











