Fitattun 'yan siyasar Najeriya da suka lashe zaɓensu

'Yan siyasa

Asalin hoton, Getty Images/BBC

A Najeriya tun bayan da sakamakon zaɓen 'yan majalisar dokoki na tarayyar ƙasar ya fara fitowa ake ta ganin sunayen wasu fitattun 'yan siyasar ƙasar a matsayin waɗanda suka yi nasara, da waɗanda suka faɗi a zaɓen.

Hukumar zaɓen ƙasar dai ta yi amfani da na'urar BVAS a karon farko don tantance masu kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙasar.

Kuma an samu masu sanya ido da dama daga cikin da wajen ƙasar domin lura da harkokin zaɓen.

An dai gudanar da zaɓen ne a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubalen tsaro da na tattalin arziki.

An samu fitattun 'yan siyasa waɗanda suka zarce a kan kujerunsu, a yayin da wasu kuma suka suka samu nasara, bayan da suka doke abokan karawarsu a zaɓen.

Ahmad Lawan

Ahmed Lawan

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmad Lawan na ɗaya daga cikin fitattun 'yan siyasar ƙasar da suka sake lashe zaɓen kujerunsu.

Sanata Lawan na wakiltar Yobe ta arewa a majalisar dattawan Najeriya, kuma an fara zaɓensa a matsayin sanata a shekarar 2007.

Takarar kujerar sanata da Ahmed Lawan ya yi ta zama mai cike ƙalubale kasancewar a ranar 6 ga watan Fabrairu ne kotun ƙolin ƙasar ta tabbatar masa da takarar, bayan da wata babbar kotu ta tabbatar wa Bashir Machina takarar tun da farko.

Barau Jibrin

Barau

Asalin hoton, Barau Jibrin/Facebook

Sanata Barau Jibrin shi ne ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta arewa.

A shekarar 2015 Sanata Barau ya fara wakiltar Kano ta arewa a majalisar dattawan ƙasar.

Kuma a yanzu shi ne shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar.

Barau ya samu nasara a kan abokan takarsa na jam'iyyar NNPP wato babbar jam'iyyar adawa a jihar Kano, da kuma jam'iyyar PDP

Kawu Sumaila

kAWU

Tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Sumaila da Takai a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ya lashe zaɓen kujerar ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta Kudu a ƙarƙashin jam'iyyar NNPP.

Kawu Sumaila ya samu nasara a kan Sanata Kabiru gaya na jam'iyyar APC wanda ya shafe shekara 16 yana kan kujerar.

Hassan Dankwambo

Ibrahim Hassan Dankwambo na jam'iyyar PDP ya samu nasarar lashe kujerar majalisar dattawa mai wakiltar Gombe ta arewa, bayan da ya doke abokin takararsa wanda ke kan kujerar na jam'iyyar APC mai mulkin jihar Sanata Saidu Ahmed Alkali.

Dankwambo wanda tsohon gwamnan jihar ne ya yi takarar kujerar sanatan a shekarar 2019 inda Sanata Alƙali ya kayar da shi a wancan lokaci.

Danjuma Goje

Goje

Asalin hoton, Goje/Facebook

Hukumar INEC ta bayyana Sanata Danjuma Goje na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe kujerar sanatan Gombe ta tsakiya a zaɓen da aka gudanar.

Goje wanda ke kan kujerar a halin yanzu ya taba zama gwamnan jihar har sau biyu tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011, daga nan kuma ya koma majalisar dattawan, wanda har yanzu yake jan zarensa.

Sanata Abdul Ningi

Tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Ningi a majalisar tarayyar ƙasar ya samu nasarar lashe kujerar majalisar dattawa mai wakiltar Bauchi ta tsakiya.

Hukumar zaɓen ƙasar INEC ce ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe kujerar sanatan ƙarƙashin jam'iyyar PDP

Abdulmumini Kofa

Kofa

Asalin hoton, Abdulmumin/Twitter

Abdulmumini Jibrin Kofa na jam'iyyar NNPP ya samu nasara a zaɓen majalisar wakilai ta tarayya.

Kofa zai koma majalisar wakilan ne a karo na uku domin wakiltar Mazabar Kiru/Bebeji.

Bello El-Rufa'i

El-Rufai

Asalin hoton, BELLO ELRUFAI/FACEBOOK

Bello El-Rufa'i, ɗan gidan gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya lashe zaɓen majalisar wakilai daga mazaɓar Kaduna ta arewa, inda ya ka da Sama'ila Sulaiman.

Bello, wanda ya yi takara a jam'iyyar APC ya samu ƙuri'u 51,052, yayin da abokin hamayyarsa ya samu ƙuri'u 32,802.

Sama'ila Sulaiman na jam'iyyar PDP shi ne yake wakiltar mazabar ta Kaduna ta arewa a majalisar wakilan Najeriya.

Zaɓen dai ya ɗauki hankali sosai, inda jama'a da dama suka riƙa sanya ido don ganin wane ne zai samu nasara.