Yadda za ku kalli jeruwar duniyoyi biyar a sararin samaniya

Jeruwar duniyoyi a samaniya

Asalin hoton, Getty Images

Watan Yuni zai bai wa masu sha'awar dube-dube a sararin samaniya wata dama da ba a faye samu ba ta kallon yadda duniyoyin unguwar rana biyar za su jeru a lokaci guda tare da watan duniyar Earth.

Daga arewacin duniya, za a hango duniyoyin Mercury da Venus da watan duniyar Earth da Mars da Jupiter da Saturn da asuba, inda za su jeru reras a layi ɗaya. Amma za a fi ganin wannan al'ajabi ne a ranar 23 da 24 ga watan Yuni.

Jerin duniyoyi daga arewacin duniya

Ana kiran irin wannan haɗuwar "celestial conjunction", wato haɗuwar duniyoyi a sararin samaniya da daddare, kuma ana iya ganin su da ido ƙuru-ƙuru.

Lokaci na ƙarshe da hakan ya faru shi ne a shekarar 2004.

Jerin duniyoyi daga kudancin duniya

Daga kudancin duniya, za a ga duniyoyin Mercury da Venus da safe, kuma tauraruwar Aldebaran za ta kasance a tsakanin su.

Aldebaran wadda kalmar Larabci ce da ke nufin "Fure" - na daga cikin taurari mafiya haske da za mu iya gani daga duniyarmu.

Faɗinta ya nunka na rana sau 44 kuma da ɗan shuɗin launi a jikinta.

A conjunction is when celestial bodies appear in a line

Haɗuwar duniyoyi a hanya ɗaya

Idan har kuka tashi da daddare don kallo, to duniyar Saturn za ku fara gani. Za ta bayyana ne da tsakar dare.

Zuwa ƴan sa'o'i kafin faɗuwar rana kuma, duniyoyin Jupiter da Mars ma za su bayyana a gan su.

Sai gabanin fitowar alfijir Venus kuma za ta bayyana, sannan sai Mercury ta ɓullo a daidai fitowar rana.

A ƙasa za mu yi muku bayanin yadda za ku gane kowace duniya idan kun ganta.

A picture containing planets

Ilimin taurari

Masana ilimin taurari sun yi amannar cewa wannan haɗuwa ta duniyoyi za ta zama gagaruma.

Wasu kuma sun yi amannar cewa haɗuwar duniyoyin na da alaƙa da wani gagarumin sauyi, da ke shigar da mutane wani yanayi na nutsuwa da kwanciyar hankali daga bala'o'in yaƙi. Hakan na nufin masifun da suka addabi ɗan adam ka iya gushewa a samu soyayya da haɗin kai.

Me za ku iya gani?

Jupiter and Saturn viewed in the night sky through a telephoto lens

Saturn

Za a samu damar ganin duniyar Saturn sosai a lokuta irin da ba bazara ba ba hunturu ba da kowane yammaci a bana.

Amma a yanzu, tana ɓullowa ne kafin tsakar dare.

A planet in space

A idon masu kallo, Saturn na kama da wata tauraruwa mai haske fara-fara kuma launin ɗorawa- ɗorawa.

Amma idan aka yi amfani da madubin hangen nesa na telescope za a iya ganin zobunan da suka zagaye duniyar Saturn ɗin, waɗanda a yanzu suke ƙanƙancewa. Suna ƙara faɗi ta kudu da arewacin duniyar.

Da asuba kuwa ana iya ganin Saturn a sauƙaƙe a Kudu maso Gabas zuwa Kudu maso Gabashin sararin samaniya.

Mars

Mars, with dark ridges visible across the centre and to the right

Asalin hoton, NASA

An fi ganin duniyar Mars da tsakar dare, musamman a watan Yuni.

Ta kan fito ne daga Gabas zuwa Kudu maso Gabashin samaniya jim kaɗan bayan gotawar ƙarfe biyu na tsakar dare, kuma ta kan yi haske irin na tauraruwa Achernar, tauraruwa ta tara mafi haske da ake iya gani daga duniyar Earth.

Ana iya ganin launin ruwan goro da ɗorawa na duniyar Mars.

Watanmu na duniyar Earth zai wuce ta gaban Mars ranar 22 da 23 ga watan Yuni - inda zai zama abu na shida da za su jeru a layin da za a ga duniyoyin sararin samaniyar.

Jupiter

A picture containing Jupiter

Da yawanmu tuni muna gane duniyar Jupiter a sararin samaniya da duku-duku.

Haskenta ya kan nunka na tauraruwa Sirius sau biyu, wato tauraruwa mafi haske da muke iya gani daga Earth.

Ta hanyar amfani da madubin hangen nesa, ɓarin yammacin duniyar ya kan fi ɓarin gabashinta haske a watan Yuni.

Daga ranar 22 ga watan Yuni ma za a fi ganinta da kyau.

Venus

Venus, with a number of dark ridges and brighter features

Asalin hoton, NASA

Venus kan fito gabanin alfijir kuma ta fi Jupiter haske.

Za a fi ganinta sosai minti 30 kafin rana ta fito a ranar 30 ga watan Yuni.

Madubin hangen nesa zai taimaka wajen ganin tauraruwa Pleiades daga gefen hagu kafin gari ya waye haske ya fito sosai.

Mercury

Mercury with computer enhanced craters, glowing in space

Asalin hoton, NASA

Ita ma duniyar Mercury ana iya ganinta a sauƙaƙe minti 30 kafin fitowar rana ran 30 ga watan Yuni kuma ita ce wacce aka fi ganin a kurkusa daga ƙurewar gani.

Sai dai takan yi nisa sosai kuma takan dusashe yadda take wahalar gani da asuba idan watan Yuni ya kama.

Tun 16 ga watan Yuni ake iya ganinta da ido ƙuru-ƙuru a gabas zuwa arewa maso gabas, minti 30 kafin fitowar rana.

Ana iya ganinta daga gefen duniyar Venus ta ƙasa-ƙasa.

Mercury kan ɓullo ta saman Arewa maso Gabas a ƙarshen ganin awa guda kafin rana ta fito ranar 27 ga watan Yuni.

A camera lens is pointed at a crescent Moon and two bright bodies in the night sky

Asalin hoton, Getty Images / Library Picture