Ana iya rayuwa a wata duniya da ke nesa da duniyoyin rana

Asalin hoton, Mark A. Garlick
- Marubuci, Daga Pallab Ghosh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakili kan kimiyya
Masu bincike na ganin akwai wata duniya da ake iya rayuwa a cikinta a kusa da wata tauraruwar da ta kusa mutuwa.
Idan aka tabbatar da haka batun yake, zai kasance karon farko da aka gano wata duniyar da za a iya rayuwa cikinta wadda ke zagaya irin wannan tauraruwar da ake kira farar wada.
An gano duniyar cikin wani yankin tauraruwar da halittu ke iya rayuwa, wanda bai cika sanyi ba kuma bai cika zafi ba.
An wallafa binciken ne a mujallar Royal Astronomical Society mai nazari kan ilimin sararin samaniya.
Farfesa jay Farihi na jami'ar University College da ke birnin London, wanda shi ne ya jagoranci binciken, ya ce wannan sabo lamari ne ga masu nazarin ilimin samaniya.
"Wannan ne karin farko da aka taba ganin irin wannan duniyar a yankin da halittu ke iya rayuwa a yankin wata farar wada. Shi yasa muke ganin akwai yiwuwar samun halittu a wata duniyar da ke zagaya ta," kamar yada ya shaida wa BBC.
Yayin da manyan taurari ke zama bakin rami bayan sun mutu, kanan kamar Ranar mu na zama fararen wadanni ne - taurarin da makamashinsu na nukiliya ya kare kuma ba ta da jerin bawon da suke da su a doronsu.
Yawanci girmansu bai wuce na duniyoyi ba kuma suna fitar da wani haske mai launukan shudi da fari da farkon kasancewarsu fararen wadanni.
Wannan tauraruwar, wadda ke da nisan shekaru 117 na gudun haske daga duniyarmu, ana tunanin ta fi kusa da tauraruwarta sau sittin idan aka kwatanta da nisan duniyarmu da ranar da take zagayawa.
Sai dai masu binciken ba su da kwararan hujjoji cewa duniyar na wurin da suke tunanin za a same ta - amma yadda wasu duniyoyi 65 masu girman watanmu ke zagaya farar wadan a yankin da ake jin halittu za su iya rayuwa, ya karfafa hasashen nasu.
"Gano wannan duniyar abin al'ajabi ne ga masu binciken," inji Farfesa Farihi.
Yankin da ake magana akai wani wuri ne da ke zagaye da tauraruwar da za a iya samun ruwa a wata duniya da ke cikin wannan yankin. Akan kira yanki da sunan "yankin Goldilocks," saboda idan duniyar ta cika kusantar tauraruwar za ta cika zafi, kuma idan ta cika nisa daga tauraruwar sai ta cika sanyi, amma a cikin yankin na Goldilocks komai "daidai yake."
Sakamakon binciken na iya zaburar da masu nazari domin su gano wasu duniyoyin da ke zagaye fararen wadanni.
"A ilimin sararin samaniya, idan muka gano abu daya, to akwai yiwuwar samun wasu masu dama ke nan," inji Farfesa Farihi.
Ana iya bin Pallab a Twitter











