Milkyway Galaxy: An gano wani abu mai jujjuyawa da ba a san shi ba a can sararin samaniya

Asalin hoton, ICRAR/Curtin
Masana kimiyya a Australiya sun gano wani abu mai jujjuyawa wanda ba a san shi ba a can sararin samaniya a birni Milkiwe Galakzi, wanda kuma suka ce ba wani abu da aka taba gani kamarsa.
Abin wanda wani dalibin jami'a ya fara gano shi, an ga yana fitar da tarin tururin maganadisu tsawon minti daya a duk bayan minti 18.
Yawanci abubuwan da ke fitar da wani abu da ya danganci makamashi kamar haske ko dumi ko turiri a sararin samaniya, an sansu an kuma yi rubutu a game da su. To amma masu bincike sun ce wani abu da yake jujjuyawa har tsawon minti daya, abu ne da ya zaman a daban, wanda za a ce ba a taba gani ba.
Masu binciken dai sun dukufa aiki a yanzu domin kara fahimtar wannan abu da suka hanga a samaniya.
Wani dalibin jami'ar Curtin, da ke yammacin Australia mai suna Tyrone O'Doherty ne ya gano abin a sararin samaniya da na'urar hangen nesa mai wata fasaha da ya kirkiro.
Dalibin na cikin wani ayarin masu bincike da ke karkashin jagorancin masaniyar kimiyyar samaniya Dr Natasha Hurley-Walker, ta jami'ar ta Curtin (ICRAR).
Malamar ta ce: "Abin yana fitowa sai kuma ya bata har tsawon wasu sa'o'i a lokacin da muke duba shi.''
Ta kara da cewa : "Wannan abu ne da ba a taba tsammani. Wannan abu ne bako mai daure kai sosai ga masanin sama jannati, saboda babu wani abu a sararin sama da aka san yana irin wannan abin."
Abubuwan da ke walkiya a samaniya ba wasu sabbi ko bakin abubuwa ba ne ga masana kimiyyar samaniya ko 'yan sama jannati, in ji masaniyar.
To amma a ce ga wani abu wanda zai yi haske har tsawon minti daya sannan hasken ya dauke, to wannan bakon abu ne ga masana in ji Dr Gemma Anderson ta cibiyar da ke nazari a kan abin.
Sanarwar da jami'ar ta fitar ta kara da cewa bayan da masanan suka yi bincike na bayanan da aka tattara a baya na shekara da shekaru, masanan sun ayyana cewa abin yana da nisan tafiyar haske ta kusan shekara 4,000 daga doron duniya.
Sanarwar ta ce abin yana da haske sosai da kuma maganadisu mai karfin gaske.
Nazariyyar da ake dangantawa da abin ta hada da cewa wata nau'in tauraruwa ce ko kuma wani bangare ne na wata tauraruwa da ta fado.
To amma galibin abubuwan da aka gani a tattare da abin har yanzu suna da daure kai.
Dr Hurley-Walker ta ce : "Gano Karin wasu abubuwan dangane da wannan abu da yake fitar da wannan haske, zai kara wa kwararru fahimta su san cewa wannan wani abu ne guda daya tilo da ya faru ko kuma wata duniyar taurari ce ta daban da ba mu taba gani ba.
Ta kara da cewa : "Ina fatan kara fahimtar wannan abu sannan kuma mu kara fadada binciken domin gano Karin masaniya a kann abin."











