James Webb: Sabon abin hangen nesan da zai sa mu ga aurarin kololuwar samaniya a karon farko

Webb deployed (artistic rendering)

Asalin hoton, NASA

A ranar 18 ga watan Disamba ne za a ƙaddamar da madubin hangen nesa na sararin samaniya na James Webb kuma zai yi wahala a bayyana irin abubuwan da ake sa ran madubin zai iya ganowa.

An ƙera sabon madubin ne don leƙo halittun da ke can cikin sarrain samaniya - da kuma yin waiwaye kan yadda yanayin wajen ya kasance a baya kaɗan - fiye da yadda muka iya sani.

Ana fatan madubin Webb zai gano haske daga taurarin farko a sararin samaniya, shekara biliyan 13.5 da suka gabata.

Wata masaniyar kimiyyar sararin samaniya kuma ma'aikaciya a Nasa, Dr Amber Nicole Straughn, ta ce: "Babban abin ƙayatarwa a wannan shiri na gagarumin madubin shi ne akwai wasu tambayoyi da ba mu ma taɓa tunanin yin tambaya a kansu ba tukunna."

"Ta wannan shiri, za mu koyi abubuwa game da sararin samaniya da za su matuƙar ba mu mamaki. A wajena, wannan shi ne babban abu mafi ƙayatarwa game da wannan madubi."

Amma ta yaya zai yi aiki kuma yaushe za mu samu ganin ainhin manyan biranen da ke sararin samaniyar ta cikinsa?

Zai nannaɗe tamkar takarda

Madubin na Jebb wato JWST a taƙaice, zai yi amfani da wani babban madubin taurari da aka taɓa aikawa samaniya, mai girman mita 6.5 na diyamita. A taƙaice, ya yi girman da sai ya kai mako biyu yana nannaɗe wa a sararin samaniya, tmkar takarda.

Wannan shiri na hadin gwiwa ne tsakanin tasoshin sararin samaniya na Amurka da Turai da Kanada inda aka kashe kuɗi dala biliyan 10. Za a ɗora madubin ne a kan wata roka ta Turai Ariane 5, a kuma ƙaddamar da shi daga French Guiana.

Annotated view of James Webb

Daga lokacin da aka harba madubin daga roka, kamar minti 30 bayan tashinsa, zai bi ta a ƙalla hanyoyi 344, Domin isa wajen da ake so ya je, zai yi tafiyar kilomita miliyan 1.5 daga duniyarmu ta Ard, inda madubin zai shafe kusan kwana 30 yana tafiya.

Size of mirror

Yaushe zai fara aiki?

Dr Straughn ya ce za a ɗauki wata shida cur kafin madubin ya fara aiki ka'in da na'in har ma ya fara aiko da hotunan farko.

"Da zarar mun aika madubin sararin samaniya, akwai wani tsari mai sarƙaƙiya da zai bi. Sannan zai shafe wata da dama kafin madubin ya yi sanyi, ya jera madubansa sannan na'urorin jikinsa su kunnu, kowane ɗaya a lokaci daban," a cewarta.

"Don haka sai a bazarar shekarar 2022 ne (a arewacin duniya) kafin mu ga hotunan farko."

Schematic of deployments

Bin sawun abin hangen nesa na Hubble

An tsara wannan sabon madubin ne don ya hango wasu cincirindon taurarin da madubin Hubble da aka ta ba ƙerawa a baya bai hango ba, wanda shi ma a wancan lokacin ya gano abubuwan da suka sauya tunaninmu kan kallon da muke yi wa sarrain samaniya.

Cikin shekara 30 da ya yi yana aiki, madubin Hubble ya ba mu muhimman hotunan yadda sararin samaniya yake, kamar gano birane 10,000 da ya yi.

Duk da cewa ana sa ran madubin Hubble zai ci gaba da aiki na wasu shekaru 10 ko 20 ɗin, ana ganin madubin Webb ne zai maye gurbinsa, da kuma samar da wani muhimmin ci gaba.

Images of the Pillars of Creation appear in visible and in near-infrared light

Asalin hoton, Nasa/ESA

Sannan Webb yana da gagrumin madubin da ya fi na Hubble. Wannan babban madubi da ke tattaro haske na nufin cewa madubin Webb zai fi gano baya fiye da yadda madubin Hubble ya iya yi.

Madubin Hubble yana zagayawa ne a kurkusa da duniyarmu ta Ard, yayin da shi kuwa madubin Webb zai kasance nesa da duniyar da kilomita miliyan 1.5 - nisan da ya ninka na wata sau hudu.

"Madubin Webb zai dora ne kan aikin da Hubble ya shafe shekara 31 yana yi na zagaye a sarrain samaniya," a cewar Dr Antonella Nota ta Hukumar Sararin Samaniyar Turai.

Ta kara da cewa: "Hubble, duk da cewa ɗan ƙaramin abin hangen nesa ne da madubi mai girman mita 2.4, zai iya waiwaye don gano abubuwna da suka faru a sararin samaniya a tsawon miliyoyin shekaru da suka wuce tun daga babbar ƙara ta Big Bang.

"Sannan zai iya gano yadda manyan biranen taurari suka jeru a samaniya."

Me abin hangen nesan Webb zai gano?

A cewar Nasa, dogayen maduban za su bai wa Webb damar gano abin da ya faru tun farkon halittar sammai.

Hubble Ultra Deep Field

Asalin hoton, Nasa/ESA/S. Beckwith (STScI)/HUDF Team

Sannan abin hangen nesan zai yi duba cikin ƙurar sararin samaniya inda taurari da duniyoyi ke samuwa sakamakonta.

Gano ko an taba ayuwa

Zai kuma taimaka mana wajen gano alamun ko an taɓa rayuwa a wasu duniyoyin, saboda zai kutsa ya gano irin sinadaran da suke sararin samaniyar kowace duniya.

Sai dai Dr Straughn ta ce, "Tabbas, ba za mu iya alkawarin cewa za mu gano alamun rayuwa a can ba."

"Amma tabbas wannan madubi shi ne gagarumin matakinmu na gaba na gano ko za a iya rayuwa a duniyoyin da suke birnin Milky Way."

Artwork of the Webb telescope

Asalin hoton, NASA

Bayanan hoto, Ana sa ran madubin Webb zai gano alamun rayuwa a wasu duniyoyin

"Akwai abubuwa da dama dangae da wannan madubin," ta ce, ba ba mu sabon ilimi kan sararin samaniya kawai zai yi ba, har ma da kara karfin dangantakarmu kan duk wani abu da ke zagaye da mu."

"Idan muka kalli taurari, idan muka kalli sarrain samaniya da daddare, na kan ji kamar akwai alaƙa a tsakaninmu," in ji Dr Straughn.

"A wani ma'aunin, mu a matsayinmu na ƴan adam an halicce mu ne daga ragowar ɓurɓushin taurarin da suka fashe biliyoyin shekaru da suka shuɗe.