Nau'in abinci mai arha da uwa za ta iya ci domin samun ruwan nono ga jaririnta

...

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

A yayin da ake fama da tsadar rayuwa da na hauhawar farashin kayan masarufi, iyaye mata masu shayarwa na fuskantar ƙalubale wajen shayarwa.

Ba sa samun abinci mai gina jiki da ake buƙata domin shayar da jarirai.

Zainab Suleiman wata uwa ce mai shayarwa, ta ce kamar watanni bakwai da suka gabata, tana iya sayen kayan abinci da ke taimaka mata wajen samun isashen ruwan nono.

Takan sayi abubuwa kamar dankalin turawa da kayan haɗa shayi irin su madara, da shinkafar tuwo da nama da kifi.

Tana kuma iya sayen kayan marmari irin su ayaba, tuffa da dai sauransu, amma yanzu waɗannan kayan abinci sun yi tsada sosai.

Shayar da nono uwa wani abu ne mai matuƙar muhimmanci ga lafiya da ci gaban jarirai.

Amma matsalar tattalin arziki na zama cikas ga iyaye mata musamman masu ƙaramin ƙarfi wajen samun abinci mai kyau da zai samar musu da ruwan nonon da za su shayar da jariransu.

Dakta Suleiman Idris Haɗejia na sashen kula da lafiyar al'umma a jami'ar Ahmadu Bello ya ce isasshen nonon uwa ya dogara ne ga yanayin lafiyar uwa da kuma ingancin abincin da take ci.

"Saboda haka idan tana da cikakkiyar lafiya kuma tana cin abinci mai iganci wanda ba sai lalle mai tsada ba, uwa za ta samu ruwan nono sosai."

"Amma idan babu isasshiyar lafiya ko kuma ba ta samun abinci mai inganci, to za a samu ƙarancin fitowar ruwan nono," in ji shi.

Dakta Idris ya ƙara da cewa duk da cewa idan ana fama da yanayi na tsadar rayuwa, da ƙarin hauhawar farashi, akwai nau'ukan abinci masu arha da uwar da ke shayarwa za ta iya ci kuma su taimaka mata wajen samun isashen ruwan nono.

Ko waɗanne abinci masu arha ne waɗannan?

...

Asalin hoton, Getty Images

"Akwai nau'ukan abinci da dama masu arha da mata za su iya ci a lokacin shayarwa waɗanda ke da sinadirai masu gina jiki da sanya kuzari ga uwa da jaririnta" in ji Dakta Idris.

Irin waɗannan abincin in ji daktan sun haɗa da;

  • Tafasa
  • Zogale
  • Rama
  • Kabaiji
  • Kankana
  • Yalo
  • Gero
  • Dawa
  • Masara
  • garin alabo
  • Wake ko waken suya
  • Dankalin hausa
  • Ugu
  • Alayyahu
  • Yakuwa
  • Rake
  • Gyaɗa
  • Shuwaka
  • Rogo
  • Kuɓewa
  • kabaiwa
  • Ruwa

Daktan ya ce mace mai shayarwa za ta iya amfani da waɗannan abinci da ya lissafo a madadin wasu nau'ukan abinci wadanda a yanzu suka gagari talaka.

Yanzu haka a Najeriya ana sayar da buhun shinkafa kan farashi naira 76,000 wanda a wasu shekaru da suka gabata ake sayarwa kan naira 35,000.

Hatta tuffa wanda a baya za a bai wa mutum guda uku kan 450, yanzu ƙanana uku ake bayarwa kan 1000 ko kuma manya guda biyu kan 1000, ayaba ma da a baya ana samun ta 300, yanzu ta haura haka.

Kayan lambu

Asalin hoton, bbc

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dakta Idris ya ce duka waɗannan abinci da ya lissafo, ba wai su kaɗai kawai za a ci ba, haɗa su za a yi da juna kafin a samu biyan buƙata na samun kuzari da kuma gina jiki.

Ya ce ya kamata a haɗa abinci mai gina jiki kamar su wake, da gyaɗa, da su ganyayyaki da kuma wanda yake ƙara kuzari kamar su rogo, gero, dawa, masara sai kuma abu mai babban muhimmanci wanda shine ruwa.

"Kinga uwa mai shayarwa za ta iya yin tuwon dawa, ko na gero ko na masara ko ma na rogo sai ta haɗa ko da miyar tafasa ko ugu, ko alayyahu, ko miyar gyada ko ma ta yakuwa ko ta kabeji ko kuɓewa ko kuma a saka kabewa."

"Za ta kuma iya haɗa waɗannan abinci bayan ta gama cin su kenan da ko yalo, ko rake, ko kankana, sai kuma ta sha ruwa da kyau idan har tayi wannan haɗin, tabbas, ruwan nono zai ƙaru." in ji Idris.

"Duk waɗannan kayan haɗa miya suna da arha a wurare da dama a arewa ko Kudu ko Yammacin ƙasarmu."

"Idan kuma ba ta sha'awar tuwo, za ta iya dama kokon dawa ko na gero ko na masara ta haɗa da faten wake sai ta saka ugu ko ɗaya daga cikin waɗannan ganye da na lissafo cikin waken." in ji Idris.

Idris ya ƙara da cewa "Uwa za ta kuma iya dafa zogale ko rama tayi kwaɗo ta saka albasa da ƙuli-ƙuli ta ci, wannan haɗin shima yana da kyau sosai."

"Za ta kuma iya yin dambun rogo ko na gero ko na masara ta saka kabeji ko ɗaya daga cikin ga ganyen da na lissafa ta kuma bi da ruwa sai kankana ko rake." in ji daktan.

"Akwai dai dabarun girki dayawa da mata suka sani wanda za su iya amfani da waɗannan abubuwan ci da na lissafo su haɗa abinci mai ma'ana."

Idris ya ce ba wai uwa za ta dafa duka waɗannan abinci a lokaci ɗaya bane, za ta iya yin jadawalin cin abinci na mako, inda za ta shirya abubuwan da za ta haɗa ta dafa, ko da a ce sau biyu a rana ne.

...

Sauran shawarwari ga iyaye mata masu shayarwa

Daktan ya kuma ce duk inda yaro ya kai wata shida, nonon uwa kaɗai ba ya isansa saboda yana girma ne kuma kuzarinsa na ƙaruwa wanda dole ne sai an ƙara masa da wani abinci.

"Duk inda aka ce yaro ya kai wata shida, muna ba wa iyaye mata shawara a fara ba shi wani nau'i na abinci wanda zai kula da lafiyarsu kamar irin su kakon dawa ko na gero ko masara da za a haɗa da ɗan waken suya ko kuma a madadin waken suya a saka gyaɗa sai a saka ɗan crayfish a markaɗa su.

"Kuma waɗannan kayan abinci, duk da cewa ana cikin yanayi na wahalar yunwa da kuɗi, abubuwa ne wanda ba sa wahalar samu balantana a irin wuraren Arewa haka kuma suna da arha."

Idris ya ce akwai wani bincike da suka gudanar inda suka yi wata uku suna bai wa yaro wannan haɗin na koko har tsawon wata uku a wasu ƙananan hukumomi guda biyar na jihar Kaduna, kuma abinci yayi tasiri sosai wajen gina jikin jaririn da ƙara masa kuzari da kuma lafiya.

Ya kuma ce abun da yake ƙara yalwatar ruwan nono ga uwa shine ilimi akan yadda ake shayarwa.

"Akwai wani lokaci iyayen namu mata ba su da ilimi da kuma yadda za su shayar da yaro ko da kuwa sun taɓa shayarwa."

"Akwai yadda za ka riƙe kan yaro da kuma yadda za ka sa bakin yaron cikin nonon da kuma lokacin da za ka bashi nonon."

"Wani lokacin za ka ga bakin yaro bai shiga cikin nonon ba, uwa ba ta tallabo yaro ya zauna sosai ba, kuma a ɗan bashi nono na minti 3 an ƙyale shi."

"Kamata yayi uwa ta tallabo yaro kusa da ita, bakinsa gaba ɗaya ya rufe wannan baƙin kan nono, kuma ta tabbatar ya sha nono na minti 10 zuwa 15 haka."

"Wannan shima yana ƙara sa nonon ya sake ɓaɓagowa."

Dakta Idris ya ƙara da cewa duka abubuwan nan na abinci da ya lissafo suna taimakawa sosai wajen gina jiki da ƙara kuzari saboda sinadiran da suka ƙunsa wanda shine babban abin da uwa mai shayarwa take buƙata haka ma jaririnta.