Da gaske ne yawan kallon waya na dakushe ƙwaƙwalwar yara?

- Marubuci, Zoe Kleinman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Technology editor
- Lokacin karatu: Minti 8
Rannan ina cikin aiki sai na miƙa wa yarona waya domin ta taya shi fira. Sai dai bayan wani lokaci sai na ji kamar ba na sa masa ido yadda ya kamata kuma ya kwashe tsawon lokaci yana amfani da wayar. Sai na yi ƙokarin karbar wayar daga hannunsa.
Daga nan ne rikici ya tashi. Ya yi ta ihu yana shure-shure, ya riƙe wayar ƙam yana kokawa da ni saboda ba ya so na karɓi wayar. Idan zan faɗi gaskiya, ban ji daɗin abin da ya faru ba, kuma yadda ya nuna turjiya a ƙoƙarinsa na ci gaba da amfani da wayar ya jefa ni cikin tunani.
Sauran ƴaƴana waɗanda suka girme shi ma suna amfani da shafukan sada zumunta da buga wasan gyam, shi ma hakan na damu na ƙwarai saboda lokacin da suke kwashewa a kan wayar.
Marigayi Steve Jobs, wanda ya kasance shugaban kamfanin Apple a lokacin da aka saki wayar iPad, bai bar yaransa sun yi amfani da su ba.
Attajirin nan na duniya Bill Gates shi ma ya ce ya taƙaita wa yaransa yadda suke amfani da kayan laturoni.

Asalin hoton, Justin Sullivan/Getty Images
Yawan kallace-kallace ko amfani da waya ya zama tamkar wani mummunan labari, ana ganin cewa yawan amfani da waya ya jefa matasa da dama cikin damuwa, ya lalata tarbiyyarsu kuma yakan ahan su samun isasshen bacci.
Ƙwararriya kan yadda jikin ɗan'adam ke aika saƙo zuwa sassa daban-daban Baroness Susan Greenfield ta taɓa cewa amfani da yanar gizo (intanet) da wasan gyam na kwamfuta na iya cutar da ƙwaƙwalwar yara da suka fara tasawa.
A shekarar 2013 ta taɓa kwatwanta illar yawan amfani da waya da abin da ya faru a farko-farkon sauyin yanayi: wani babban sauyi da mutane ba su lura da shi ba da wuri.
A yanzu mutane da dama na damuwa kan yadda yara ke amfani da waya. Sai dai da alama gargaɗin da ake yi game da illarsa ba zai iya fayyace abubuwan da ya kunsa ba.
Wani rubutu da aka yi a mujallar kiwon lafiya ta Birtaniya, wato British Medical Journal, ya soki ikirarin Baroness Greenfiel kan tasirin yawan amfani da waya a kan ƙwaƙwalwa.
Bayanin ya ce ikirarin Baroness "bai yi daidai da sakamakon binciken kimiyya ba...kuma kuskure ne ga iyaye da kuma al'umma baki ɗaya".
A yanzu kuma wani gungun masana kimiyya na Birtaniya sun yi ikirarin cewa babu wani bayani ƙwaƙƙwara kan illar yawan amfani da waya.
Ko hakan na nufin mun yi kuskure game da yadda muke damuwa idan yaranmu na yawan amfani da waya?
Da gaske ne yana da illa sosai?
Wani masani kan tunanin ɗan'adam Pete Etchells, da ke aiki a Jami'ar Bath Spa University, na daga cikin gungun masana kimiyyya da ke ganin har yanzu babu cikakkiyar shaida kan illar yawan amfani da waya.
Ya yi nazari kan ɗaruruwan bincike da aka yi kan tasirin yawan amfani da waya ga lafiya, da kuma bayanai masu yawa kan yadda matasa ke amfani da waya.
A cikin littafinsa mai suna 'Unlocked: The Real Science of Screen', ya bayyana cewa akwai abubuwa da dama da ke ƙunshe kan wannan lamari, kuma sau da yawa an akwai kuskure kan abubuwan da ake faɗi.
"Babu wasu ƙwararan hujjoji da za a dogara da su kan illar yawan amfani da waya ga lafiya," kamar yadda ya rubuta a littafin.

Asalin hoton, Arthur Debat/ Getty Images
Wani bincike da ƙungiyar masana halayyar ɗan'adam (American Pschology Association) aka wallafa a 2021, shi ma ya bayyana abu makamancin haka.
Mutane 14 da suka gudanar da binciken, daga jami'o'i daban-daban, sun yi nazari kan bayanai 33 da aka wallafa tsakanin 2015 zuwa 2019.
Yawan kalle-kalle, kamar amfani da wayoyin hannu masu intanet da shafukan sada zumunta da kuma buga wasannin gyam na yara "ba sa yin wani babban tasiri ga lafiya ƙwaƙwalwa", kamar yadda suka gano a bayanin nasu.
Haka nan kuma yayin da wasu bincike-binciken suka bayyana cewa haske launin shuɗi wanda ke fita daga waya - na yin cikas ga samun bacci - saboda yana danne samuwar sinadarin 'melatonin' a cikin jiki, wani bincike a 2024 da ya yi nazari kan wasu bincike-bincike guda 11 daga sassa daban-daban na duniya ya nuna cewa babu wata hujja da ta nuna cewa kallon waya sa'a ɗaya kafin kwanciya na haifar da wahala wajen samun bacci.
Matsalolin da ke tattare da binciken
Ɗaya daga cikin matsalolin da ake samu shi ne yawancin bayanan da ake da su kan yawan amfani da waya sun dogara ne kan "abin da wasu suka faɗa", in Farfesa Etchells.
Wato masu bincike kawai kan tambayi matasa ne yawan lokacin da suke kwashewa wajen amfani da waya, da kuma yadda suke ji idan suna amfani da ita.
Ya kuma ce akwai miliyoyin hanyoyi da za a iya bi a fassara waɗannan bayanai da aka tattara.
Ya bayar da misali da ƙaruwar sayar da alawar 'ice cream' a lokacin zafi idan aka kwatanta da ƙaruwar alamomin cutar kansa. Dukkanin su na da alaƙa da yanayin na zafi, amma ba su da alaƙa da juna. Alawar ice cream ba ta haifar da cutar kansa.

Asalin hoton, Universal Archive/Universal Images Group via Getty Images
A wani bincike, wanda masana ƴan Birtaniya da kuma ƴan Amurka suka gudanar, sun nazarci hoton ƙwaƙwalwar yara 11,500 waɗanda shekarunsu suka kama daga 9 zuwa 12 da bayanin kan lafiyarsu da kuma lokacin da suke kwashewa suna amfani da waya.
Yayin da yawan kallon waya yakan kawo sauyi kan yadda sassan ƙwaƙwalwa ke alaƙa da juna, binciken bai samu wata hujja da ke nuna cewa yawan kallon waya na da alaƙa da lafiyar ƙwaƙwalwa ko fahimta ba, hatta kuwa a waɗanda ke shafe sa'o'i suna amfani da waya a kullum.
Nazarin wanda aka yi shi daga shekara ta 2016 zuwa 2018, ya kasance ƙarƙashin kulawar Farfesa Andrew Przybylski wanda ya yi nazari kan tasirin wasan kwamfuta na bidiyo da shafukan sada zumunta kan lafiyar ƙwaƙwalwa.

Asalin hoton, John Nacion/Getty Images
Farfesa Przybylski da Farfesa Etchells sun yi watsi da barazanar da illolin abubuwan da ake yaɗawa a intanet kan haifar sakamakon yawan kallon munanan abubuwan da ke lalata tarbiyya.
Farfesa Przybylski ya damu da muhawarar taƙaita amfani da waya ko ma daina amfani da ita - kuma yana ganin idan aka ci gaba da sa ido kan yadda ake amfani da wayar, to za ta ci gaba da zama haramtaccen abu.

Asalin hoton, Matt Cardy/Getty Images
Mutane da dama ba su yadda da hakan ba.
Ƙungiyar da ke fafutukar ganin an daina bai wa ƙananan yara waya a Birtaniya ta ce mutum 150,000 zuwa yanzu sun sa hannu don neman a haramta wa yara ƴan ƙasa da shekara 14 amfani da waya da kuma jinkirta lokacin fara amfani da shafukan sada zumunta har sai sun kai shekara 16.
Lokacin da Jean Twenge, wata farfesa a ɓangaren halayyar ɗan'adam daga jami'ar jihar San Diego, ta soma bincike kan ƙaruwar damuwa a tsakanin matasa a Amurka, ba ta fito ta bayyana hujjar cewa shafukan sada zumunta da wayoyin hannu na da illa ba, kamar yadda ta faɗa. Amma ta gano cewa suna bayar da gudummawa.
A yanzu, ta yi amannar cewa raba yara da waya abu ne da ya dace, kuma tana shawaratar iyaye su yi bakin koƙarinsu wajen raba yara da wayar.

Asalin hoton, Matt Cardy/Getty Images)
Wani bincike da aka gudanar a 2024, ya ƙunshi yara 181 daga iyalai 89.
An kwashe mako biyu, inda aka taƙaita wa rabinsu amfani da waya zuwa awa uku a mako daya, inda aka umarce su su bayar da wayoyinsu.
Binciken ya ce rage wa mutanen yawan amfani da shafukan sada zumunta "ya nuna alamar taimaka wa tunanin yaran da matasa" kuma ya bunƙasa "ƙaunar da suke samu ta hulda da al'umma", duk da cewa nazarin ya buƙaci a zurfafa bincike.
'Hukunci ya danganta ga iyaye'
Lokacin da na tattauna da Farfesa Etchells, ɗaya daga cikin ƴaƴansa da kuma karensa na ta zirga-zirga, suna shiga suna fita. Sai na tambaye shi ko yawaitar wayoyi ta sauya tunanin yara, sai ya yi dariya, ya ce ai komai ma na canza tunanin yara: ta haka yanayin ɗan'adam yake.
Sai dai ya nuna tausayi game da yadda iyaye ke nuna damuwa kan fargabar illar da waya za ta iya yi wa ƴayansu.
Abin damuwa ne yadda babu takamaiman bayani da shawarwari a kai - sannan kuma batun na cike da bayanai na son rai.
Batun yawan kallon waya abu ne da ke tasowa sosai a duk lokacin da nake tattaunawa da iyaye. Wasu na tsaurarawa fiye da wasu.
Yanzu haka akwai shawarwari daban-daban da ake bayarwa. Daga ƙungiyar likitocin yara ta Amurka har kwalejin ilimin lafiyar yara ta Birtaniya, babu wadda ta iya bayyana lokacin da ya kamata yara su kwashe suna amfani da waya a rana.

Asalin hoton, FABRICE COFFRINI/AFP via Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ɓangare ɗaya kuma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta bayar da shawarar daina barin yara ƴan ƙasa da shekara ɗaya da kayan kallo, sannan kuma kada a bari ƴan ƙasa da shekara huɗu su zarce awa huɗu suna kalle-kalle. (Duk da dai an bayar da shawarar ce domin haɓɓaka sauran wasanni tsakanin yara).
Sai dai akwai taƙaddama game da haka saboda babu wata hujja da aka dogara da ita wajen yanke shawarar, kuma wannan ya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin masana kimiyya - duk kuwa da buƙatar da al'umma ke da ita ta ganin an taƙaita yadda yara ke amfani da kayan kallo.
Kasancewar babu matsaya kan taƙaita amfani da kayan kallo ga yara, hakan na nufin za a samu rashin daidaito ga yara.
Ko ma dai mene ne, abu ne mai matuƙar muhimmanci. Idan har yawan kallace-kallace na da illa ga yara, zai ɗauki shekaru masu tsawo kafin kimiyya ya iya tabbatar da hakan.
Idan har aka gano ba ya da illa, hakan na nufin mun riga mun ɓata lokaci da kuɗi wajen ƙoƙarin hana yara yin abu da wataƙila ke da matuƙar amfani.
A yanzu dai wayoyi na zama jiki, amfani da shafukan sada zumunta ya shiga jikinmu, sannan mutane na amfani da manhajojin AI wajen gudanar da jingar da ake ba su a makaranta ko kuma wurin magani - fasahar zamani na ci gaba da sauyawa cikin sauri, ko da mun ƙyale yaranmu su yi amfani da ita ko a'a.
Zane: Jodi Lai












