Nawa kamfanonin sadarwa suka ƙara kuɗin kira da data a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan Najeriya sun wayi gari ranar Talata da sabon ƙarin kuɗin kiran waya da na data daga kamfanonin sadarwa, inda ƙarin ya ruɓanya sau uku kwatankwacin kaso 150.
Wani ƙarin abin da ke baƙantawa ƴan Najeriya rai shi ne yadda suka wayi gari da ƙarin ba tare da sanarwar yin hakan ba kamar yadda suka saba a baya ba, duk da daga baya kamfanin MTN ya nemi afuwa.
Masu sharhi kan al'amura na cewa ƙarin kuɗin zai ƙara jefa ƴan Najeriya cikin halin matsi bisa lura da yanayin da ƴan ƙasar ke ciki tun bayan ɓullo da jerin matakan tattalin arziƙi da gwamnatin ƙasar ke yi da suka haɗa da haraje-haraje.
Nawa ne ƙarin da aka yi?
Duk da cewa da ma ƴan Najeriya na zaman jiran kamfanonin sun yi ƙarin kuɗin kiran da na data kamar yadda hukumar kula da sadarwa ta Najeriya, NCC ta amince wa kamfanonin su yi amma ka da ya wuce kaso 50 cikin 100 na farashin.
BBC ta fahimci cewa kamfanin MTN ya sauya farashin data misali tsarin 15GB a mako guda daga naira 2,000 zuwa naira 6,000.
Dangane da kuɗin kiran waya, BBC ta fahimci cewa MTN na ɗaukar kwabo 75 a kan kowace daƙiƙa maimakon kwabo 13 da kamfanin ke yi a baya.
A shafinsa na X, MTN ya ce "sun yi ƙarin ne domin kyautata aiki" sannan kamfanin ya nemi afuwar ƴan ƙasar cewa "muna neman gafararku dangane da irin tasirin da al'amarin zai yi a kanku da kuma jan ƙafa wajen sanar da ku halin da ake ciki."
Masu amfani da layin Airtel suna ta faman kunfar baki a kafafen sada zumunta inda suka ce kamfanin ya ruɓanya farashin sau fiye da biyu.
Sai dai har kawo yanzu ba a ji kamfanin ya ce uffan ba.
Sai dai kuma ba a ji masu amfani da kamfanin Glo ba na nuna takaicinsu ba, wani abu da ke nuna cewa wataƙila sai nan gaba kamfanin zai yi ƙarin.
Wane tasiri ƙarin zai yi?
Mubarak Uniquepikin wanda mai yin shirye-shirye ne a shafukan intanet ya shaida wa BBC cewa ƙarin kuɗin kiran waya da na data ka iya yin babban tasiri musamman ga mutanen da ke gudanar da harkokin kasuwancinsu a intanet.
"Tattalin arziƙin da ma yana tangal-tangal kuma zuwan wannan ƙarin a yanzu lokacin da jama'a ke kasuwancinsu a shafukan intanet saboda mutane da dama ba sa iya karbar hayar shaguna, zai yi muni ƙwarai."
"Matasa da dama ba sa iya sayen data kuma yanzu wannan ƙarin zai ƙara ta'azzara al'amarin gare su." In ji Mubarak
Me ƴan Najeriya ke cewa?
Yanzu haka dai babu wani batu da ake tattaunawa a kai a Najeriya kamar na ƙarin kuɗin wayar da data da kamfanonin suka yi.
Mun duba wasu shafukan sada zumunta domin ganin abin da jama'a ke faɗi kamar haka:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Wani mai suna Silva a X ya ce:
"Batun gaskiya, Najeriya ƙasa ce mai wuyar sha'anin zama. MTN sun wayi gari da ƙarin kuɗin data na mako-mako na 15gb daga naira dubu biyu zuwa naira dubu shida ba tare da sanarwa ba, wani abun da ke nuna rashin martaba jama'a.
Yanzu kenan a wata farashin ya koma naira dubu 24, kusan albashi mafi ƙanƙanta na ƙasar kenan za a kashe a kan data, ɗan uwa wannan azabtarwa ce."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Adewale wanda shi ma mai amfani da X ya wallafa cewa:
Ƴan Najeriya sun zama zakarun gwajin dafi. Ɓerayen da ake gwaji a ɗakin gwaji.
Sun gwada abubuwan daban-daban a kanmu kuma mu yi na'am.
Me ya sa farashin data ya ƙaru daga naira dubu biyu zuwa dubu shida?
....Me ya sa haka?
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Morris wanda shi ma mai amfani da shafin X ne ya yi tambaya dangane da ƙarin:
Yaya matasa ke fama a Najeriya?
Wani ƙarin farashi daga MTN?
Shin matasa za su yi ƙorafi ne kawai sai kuma su ci gaba da rayuwa haka?











