Dubban mutane sun yi zanga-zanga a faɗin Spain kan matsalar gidaje

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
Dubban mutane sun fito kan tituna a babban birnin Spain, Madrid, da kuma fiye da birane 50 a faɗin ƙasar, suna neman gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar gidaje da ke ƙara tsananta.
Fushin jama'a ya ƙaru ne bayan majalisar dokokin ƙasar ta ƙi amincewa da wani ƙudirin doka na gaggawa da aka gabatar domin ƙara kare haƙƙin masu haya.
Wakilin BBC da ke Madrid ya ce masu zanga-zangar na neman a ɗauki matakai masu faɗi da tasiri wajen warware matsalar gidaje, kuma suna jin daɗin yadda suka yi nasarar sanya batun gidaje ya zama babban abin da siyasar ƙasar ta fi mayar da hankali a kai a halin yanzu.
A lokaci guda, an fara hasashen cewa Firaministan Spain, Pedro Sánchez, na iya amfani da rashin jin daɗin jama'a domin kiran zaɓen gaggawa kafin wa'adin da aka tsara.
Shawarwarin da gwamnatin Sánchez ta gabatar a majalisar dokoki sun fuskanci adawa daga jam’iyyun masu ra’ayin dama da na matsananciyar dama, lamarin da ya sa ba a samu amincewa da su ba.
Masana siyasa na ganin cewa matsalar tsadar gidaje da ƙarancin gidajen haya masu araha na ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke fuskantar gwamnatin Spain, yayin da matsin lambar jama'a ke ƙaruwa kan shugabanni su samar da mafita mai ɗorewa.

































