Hatsarin saye da sayar da tsofaffin wayoyinku

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, அஷ்ஃபாக்
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, பிபிசி தமிழ்
"An samu garaɓasa...Zan iya sayar da wayata na sayi sabuwa? Amma wane ne zai sayi tsohuwar waya da tsada?" Idan wani ya yi maka wannan tambayar, za ka iya tunanin abubuwa da dama.
Amma ƙila abin da ai fi kyau shi ne ka ragargaza ta, sannan ka zuba ta a rami ka binne, in ji wasu masana a fannin fasahar sadarwa.
"Fasaha ka iya zama abu mai amfanin gaske, amma wani zubin kan zama mai haɗari." Wannan ita ce fahimtar Christian Lanke, wani masanin tarihi ɗan Norway da ya lashe kyautar Nobel.
A cewar alƙaluma na baya-bayan nan daga ƙungiyar masu sayar kayan latironi ta Indiya, Cellular and Electronics Association of India, an sayar da tsofaffin wayoyin hannu sama da miliyan 20 a ƙasar a 2020 kawai.
Alƙaluman sun kuma nuna cewa akwia yiwuwar tsofaffin wayoyi sama da miliyan 10 da ke ajiye a wajen mutane.
Kazalika, ƙungiyar ta yi hasashen za a samu wayoyin zamani da aka yi amfani da su kusan miliyan 25 a kasuwannin waya nan da shekarar 2025.

Asalin hoton, Getty Images
Zan iya sayar da wayata?
Idan ba ka damu da wasu abubuwa ba kamar lambobin waya, bayananka na banki, lambobin sirri, hotuna, bidiyo, hirarraki, da kuma tarihin zirga-zirgarka a intanet, to za ka iya sayar da tsohuwar wayarka.
Idan ba haka ba kuma, akwai abubuwan da ya kamata mutum ya lura da su. Shekara 10 da suka wuce, da wuya mutum ya iya dawo da bayanai daga tsohuwar wayarsa.
Amma yanzu ba haka lamarin yake ba. Ko kana amfani da iPhone ko Android, abu ne mai sauƙi yanzu ka iya dawo da bayananka.
"Akwai manhajoji da suke yin wannan aikin, waɗanda da taimakonsu mutum zai dawo da bayanansa daga tsohuwar wayarsa," in ji Siva Bharani, wani ƙwararre kan fasaha.

Asalin hoton, Getty Images
"Misali, bari a ce muna da memori mai girman 1GB. Yana cike da hotuna da bidiyo, saboda haka bayanan suna ajiye ne a wuri ɗaya.
"Idan ka goge shi, komai zai ɓace daga kan memorin. Amma za a iya dawo da su. Ko da an goge kayayyaki, za su bar shararsu a wajen [junk files]," a cewar Siva Bharani.

Asalin hoton, Getty Images
'Ba a goge kayayyaki ba'
"A kwanan nan, na karɓi manyan wayoyi 10 zuwa 15 na sayarwa, a mma babu wadda aka goge kayan da ke cikinta. Su 'yan kasuwar waya ba bu ruwansu ko an goge bayanai ko ba a goge ba, burinsu dai su samu riba nan da nan ta hanyar sayar da wayar da aka kawo musu,"kamar yadda wani mai gyara ya bayyana.
Amma Mohammad Nisar, wanda ya shafe shekara sama da 12 yana sayar da tsoffin wayoyi, ya ce "ba mu saba jin an kwashi bayanan wani a tsohuwar wayarsa ba don zalinci".
Ya ƙara da cewa: "Amma kuma ko da an lalata waya ta hanyar hatsarin mota ko gobara, za a iya kwasar bayanai cikin sauƙi. Za ka iya sayar da wayarka idan ka tabbata babu wasu muhimman bayanai a kanta. Idan ba haka kuma, zai fi kyau ka bar ta a wajenka."
'Shi ma salon kasuwanci ne'

Asalin hoton, Getty Images
Salo ne na kasuwanci mutum ya ce zai sayar da wayarsa don sayen sabuwa ta hanyar musaya a lokutan bukukuwa.
Dalili biyu da za su sa 'yan kasuwa su sayi wayar mutum su ne; ko dai su saya a farashi mai sauƙi, ko kuma su saya don su yi mata kwaskwarima kuma su mayar da ita kasuwa. Ko kuma su ciri wasu ɓangarori na wayar don amfani da su.
Kowane suka yi a nan zai ba su damar ci riba. "Akwai kamfanoni da yawa da ke sayen tsoffin wayoyi kuma su sayar, ko kuma su yi musaya da sababbi," in ji Siva Bharani.
"Kamfanonin da ke sayen tsofaffin wayoyi kan tambaye mu idan an goge bayanai daga wayoyin yadda ya dace. Sukan yi amfani da wasu manhajoji don goge bayanai daga waya kafin a yi mata farashi gwargwadon irin saurinta."

Asalin hoton, Getty Images
'Saye da sayarwa na buƙatar kulawa'
Baya ga tabbatar da cewa wayar da aka yi amfani da ita tana aiki yadda ya dace, ya kamata kuma mutum ya duba don gane ko wanda ya yi amfani da ita ya bi hanyar da ta dace wajen amfanin.
Ma'ana, a tabbatar cewa bai yi amfani da ita wajen aikata wani laifi ba.
Don tabbatar da hakan, ya kamata ku dinga sayen waya daga hannun mutum ko shagon da kuka aminta da shi.
Idan za ku sayi tsohuwar waya ko a hannun wane ne, ya kamata ku duba muhimman abubuwa, kamar lambar IMEI da kuma rasitin cinikin wayar.
Ya kamata ku duba ko akwai wasu manhajoji da ba su da amfani, da batiri, da hasken wayar ko suna aiki yadda ya kamata.
A wasu lokutan, akan saka ƙarin wasu manhajoji a tsohuwar waya don a kwashi bayananmu.
"Saboda haka, yana da kyau mutum ya yi shawara kafin saye ko sayar da wayarsa ga wanda bai sani ba," in ji Bharani.











