Matakan da iyaye za su ɗauka don hana yara kallon batsa

Asalin hoton, Getty Images
Wasu iyaye da suka kai ƴaƴansu makaranta don samun ilimi sun koka game da koma-bayan da ake samu a hazaƙar ɗaya daga cikin ƴayansu mai shekaru 15 wadda suka kai wajen likitan ƙwaƙwalwa domin ya binciki lafiyarta:
"A da ita ce ke zuwa ta ɗaya a ajinsu har zuwa aji na shida, amma yanzu ta daina mayar da hankali kan karatun."
Likitan ya yi nasara wajen gano damuwar yarinyar sakamakon tattaunawar sirri da suka yi tsakaninsa da ɗalibar.
Bayan wasu shawarwari da likitan ya ba iyayen yarinyar, sun ci gaba da kula da ita har tsawon watanni, abin da ya sa ɗalibar ta canza hali tare da mayar da hankalinta kan darasin da ake koyarwa a makaranta.
Ƙorafin da iyayen yarinyar suka yi wa likita da farko:
Iyayen sun shaida wa likita yadda yarinyar take riƙe da waya dare da rana:
"Sai ta shiga ɗaki ta kulle ƙofa kuma kullum wayarta na kulle da lambobin sirri, idan mun tambaye ta sai ta ce tana magana ne da ƙawayenta kuma tana saurin fusata.''
Likitan ƙwaƙwalwa da Jima'i Ashok ya bayyana cewar kallon hotunan batsa ne suka jefa yarinyar cikin yanayin ƙaurace wa harkokin karatu da mu'amala da mutane har ta fifita rayuwar kaɗaici.
Yayin da matsalar kallon hotuna da bidiyon batsa ta fara damun makusantan masu irin wannan ɗabi'a, a kwanakin baya wata kotu a Kerala, ƙasar Indiya ta karɓi ƙorafi daga wani mutum da ke neman ta kori tuhumar da ake yi masa kan kallon bidiyon batsa a bainar jama'a.
A dokar kotu, kallon batsa ba laifi ba ne sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba:
"Kallon hotunan batsa ba laifi ba ne [a tsarin doka]. Amma idan yara suka fara kallo tun suna ƙanana, ana samun illar da za ta jima tare da su, iyaye marasa kula na sayawa ƴaƴansu waya ne don su faranta wa yaran rai.''
"Ya kamata iyaye su san haɗarin da ke tattare da hakan. A bari yara su kalli fina-finai na ilimantarwa a wayoyinsu a gaban iyaye, ko kuma su koyi wasannin motsa jiki masu sanya nishaɗi.''

Asalin hoton, Getty Images
Shawarwari ga iyaye daga likita Ashok
"Idan aka kwatanta da ƙarnin baya, yaran yanzu sun fi samun damar sanin mene ne jima'i saboda samuwar fasaha. Hatta manyan kafofin sada zumunta na ɗauke da hotunan batsa.''
“Tun bayan annobar Korona ilimi ya zamo ba tare da sanya idon malamai ba, na'ura mai ƙwaƙwalwa da wayoyi sun maye gurbin malamai da iyaye, ya kamata iyaye su zaɓar wa ƴaƴansu mafitar da ba za ta cutar da su ba.''
Kada hankalin iyaye ya tashi idan suka gano cewa yaransu na kallon batsa.
Ya kamata mu sani cewar yara na ƙara samun sha'awa a lokacin da suke ƙara girma.
Abin da ya kamata shi ne a sanar da su cikin hikima, irin matsalolin da ke tattare da mayar da hankali kan kallon bidiyoyi na batsa.
Idan har muka fusata da su, wannan ba zai ƙara musu komai ba sai dai ya ƙara munana lamarin."
Mu sani cewa, "yaran da suka haura shekara 11 a wasu lokutan sukan so kaɗaicewa daga iyayensu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Babu matsala idan suka fita domin yin wasa a waje a irin waɗannan lokuta, to amma idan muka lura da cewa suna yawan kaɗaicewa tare da manne wa wayoyinsu, ya kamata a yi musu magana domin jin dalili.
Ku tambaye su ko suna da wata matsala. Ku zauna tare da su. Ku sanya su su fahimci cewa iyayensu na ƙaunarsu.
Cin abinci tare da su da kuma fita yawo tare zai ƙara kusanci tsakaninku.
Ashok ya ce wannan zai sa su faɗa muku abin da ke cikin ransu.
Ɗabi'ar ɗan'Adam ce ka ga yara da suka haura shekara 11 suna neman sanin abubuwa game da abubuwan da suka shafi jima'i.
Saboda haka akwai buƙatar a fitar yara daga cikin duhu domin gudun kada su bauɗe, in ji Ashok, masani kan lafiyar ƙwaƙwalwa.
“Misali a shekarun baya akwai tsananin rashin fahimta game da jinin al’ada wanda wasu suka camfa. A yanzu an wayar da kan mutane sun fahimta.
Ana buƙatar hakan a ɓangaren jima'i.
Ya kamata yara da suka haura shekara 11 su samu cikakken bayani kan batutuwan da suka jiɓanci shan sigari, da illar barasa da kuma batun jima'i.
Ta haka ne kawai za su samu cikakken bayani game da waɗannan abubuwa.
Yayin da yara suka fara balaga, akwai tambayoyi da canjin da suke gani a jiki da tunaninsu ke haifarwa, da zarar ba su samu gamsasshiyar amsa ko bayani ba sai su faɗa tarkon kalle-kallen batsa ta hanyar amfani da shawarwarin sa'o'insu.
Likitan ƙwaƙwalwa da ilimin jima'i Ashok ya jaddada muhimmancin koyar da ilimin jima'i a makarantu don kawo ƙarshen janyewar da samari da ƴan mata suke yi daga jikin iyaye da zarar sun fara sha'awa.
Rashin ɗaukar waɗannan matakai daga Malamai da iyaye ya na jefa yara a shaye-sheyen kayan maye.











