Ma'aikata fiye da 2,000 sun shiga mawuyacin hali bayan rufe sansanonin soji a Afirka

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Mamadou Faye
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Dakar
- Lokacin karatu: Minti 5
Rufe sansanonin soji a ƙasashen Afirka ya haifar da rashin ayyukan yi tsakanin fararen hula aƙalla 2,000 a wuraren da lamarin ya shafa. Da dama da suka shafe shekaru suna aiki a sansanonin sun ce rayuwar su ta taɓarɓare saboda matakin.
Rufe sansanonin soji da ke Afirka ya janyo wa mutane aƙalla 2,000 masu aiki a wuraren rasa ayyukansu, duk da cewa akwai waɗanda suka shafe shekaru fiye da goma suna aiki a sansanonin. A yanzu suna cikin fargaba a kan halin da za su shiga nan gaba saboda rashin aikin yi.
Kawo yanzu Faransa ta rufe sansanonin sojin ta a jamhuriyar tsakiyar Afirka da Mali da Burkina Faso da Nijar da Chadi da Senegal da kuma Côte d'Ivoire, bayan ƙasashen sun nemi sojin Faransan su fice daga cikin su.
Amma wasu ƙasashen Yamma ma sun rufe sansanonin sojin nasu, ciki har da Amurka da ta rufe nata a Nijar, da kuma rundunar haɗin gwiwa ta wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, United Nations Multidimensional Integrated Stabilization Mission in Mali (MINUSMA) da aka rufe a Mali.
Binciken BBC ya nuna cewa ma'aikata aƙalla 859 lamarin ya shafa a Mali, yayin da a Chadi ma'aikata 400 abin ya shafa, sai kuma a Nijar da ya shafi ma'aikata 350. A Senegal ma ya shafi 162, sai Cote d'Ivoire da matakin ya shafi mutum 280. Ba a dai tabbatar da yawan mutanen da lamarin ya shafa ba a Jamhuriyar tsakiyar Afirka.

Asalin hoton, Courtesy to Mr Djibril Ndiaye
Yayin da dakarun ƙasashen wajen ke ficewa daga ƙasashen Afirkan, ana barin mutanen da ke yi masu aiki a waɗannan ƙasashe ba tare da wani zaɓi na inda za su karkata domin cigaba da aiki ba. Wani abin da ya yi muni kuma shi ne yadda suke zaune babu wata hanyar samun kuɗi domin gudanar da harkokin su na yau da kullum, musamman sauki haƙƙin kula da iyali.
A Senegal, Djibril Ndiaye ya shaida wa BBC cewa rayuwarsa ta yi canjin ba-zata bayan shafe shekara 26 yana aiki a sansanin sojin Faransa da ke Ouakam, inda yake daga cikin ma'aikata 162 da ke zaman jimamin rasa aikinsu.
Yana da ƴaƴa huɗu kuma ya yi aiki ne a matsayin injiniya mai kula da na'ura mai ƙwaƙwalwa, yayin da kuma shi ne ke kula da sauran ƴan‘uwansa 21, kasancewar shi ne babba.
Niaye ya shaida wa BBC cewa "Karatun ƴaƴanmu tun daga firamare har jami'a yana cikin haɗari''.
Ma'aikatan da suka rasa ayyukansu a ƙasashen Afirkan sun haɗa da ƙwararru a fannin na'ura mai ƙwaƙwalwa da ƙwararru a fannin sadarwa da kanikawa da kuma masu dafa abinci.
"Muna da dukkan ƙwarewar da ake buƙata domin mayar da mu wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnati don mu ci gaba da aiki," in ji Ndiaye.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A jamhuriyar Nijar, inda wannan matakin ya shafi ma'aikata 274, Aboubacar Ousmane ya shafe shekara fiye da 20 yana aiki a sansanin sojin Amurka da ke Niamey a matsayin mai dafa abinci, ya ce an bar su a cikin halin rashin tabbas.
Wata bakwai ke nan da hayar Aboubacar ta ƙare kuma bai sake biya ba, kuma ya kasa biyan FCFA 50,000 ɗin ne saboda rasa aiki da ya yi, da kuma rashin biyansa haƙƙoƙinsa.
Shi ma Rhissa Sadikan Saloum, wani akawu a sansanin sojin Faransa na Niamey ya ce irin halin da yake ciki ya yi muni.
"Halin da muke ciki yana da ruɗani sosai saboda ba abu ne mai sauƙi ba mutum ya samu aiki yanzu, bayan ka yi wa dakarun Faransa aiki.'' Saloum ya shaida wa BBC.
Ya yi bayanin cewa da zarar an samu labarin sun taba yi wa dakarun Faransa aiki to ba a ba su aiki.
A Chadi ma wasu mutum 400 da a baya suka yi wa dakarun Faransa aiki suna fama da mawuyacin halin da suka shiga bayan rasa aikin nasu.
A wajen wani taron manema labarai a ranar Asabar 8 ga watan Fabrairu, a Bourse du Travail in Ndjamena, wasu tsoffin ma'aikatan sun koka da rashin samun haƙƙoƙinsu na sallamar aiki da kuma gaza ba su wasu guraben aikin a gwamnatin Chadi.
Me zai faru da waɗannan mutanen?

Asalin hoton, Getty Images
Mafi yawan ƙasashen da wannan mataki ya shafa dai sun fito fili sun bayyana aniyarsu ta sake bai wa mutanen da suka rasa aikin wasu sabbin ayyukan na daban. Amma sojin Faransa sun shirya wani taro inda suka yi tayin samar da ayyukan yi a wani kamfani ga ma'aikata 162 da za su rasa ayyukansu a bana.
A lokacin taron kuma kamfanoni ƙalla 70 sun yi tayin guraben aiki 300.
Birgediya-Janar Yves Aunis, kwamandan rundunar Faransa a Senegal, (EFS), ya sanar da tsari na musamman da zai bayar da ayyuka ga ƴan Senegal 162 da za su rasa ayyukansu a watan Yuni mai zuwa. Ya kuma ce za a biya mutanen da za su rasa ayyukan nasu diyyar euro miliyan 983 na kuɗin FCFA.
Haka nan kuma Janar Aunis ya ce za a shirya taron bita na koyar da sana'oin hannu domin dogaro da kai ga masu buƙata a cikin ma'aikatan da za su rasa aikinsu.
Sai dai Ndiaye ya ce "Mun yi zaton za a sauya wuraren aiki ne ga ma'aikatan da wannan abu ya shafa domin mayar da su zuwa wasu hukumomi da ma'aikatun gwamnati saboda suna da ƙwarewar da ake buƙata.''
A Côte d'Ivoire, majiya daga ma'aikatar tsaro ta shaida wa BBC cewa akwai tsarin da aka yi na samar da guraben aiki 280 ga waɗanda wannan batu ya shafa.
Majiyar ta ce akwai yiyuwar ɗaukar wani kaso na ma'aikatan da suka rasa aikin nasu, don su cigaba da aki tare da dakarun Faransa da ke aikin haɗin gwiwa da dakarun Ivory Coast a tsohon sansanin rundunar mai aiki a Port-Bouët, da ke kudu maso gabashin birnin Abidjan.
BBC ba ta samu martani a hukumance daga gwamnatin Nijar ba, amma wani ma'aikacin ma'aikatar ƙwadago ya ce ma'aikatan da aka kora sun yi ƙoƙarin ganin an ɗauke su aikin gwamnati amma kawo yanzu babu abin da aka yi a kai.
A ChadI, BBC ba ta samu amsar saƙon da ta aike wa ma'aikar kula da walwalar ma'aikata ba kuma haka abin yake a jamhuriyar tsakiyar Afirka, inda wata majiya ta ce babu wani shiri kan sauya wajen aiki ga ma'aikatan da aka sallama daga aikinsu a sansaanonin soji.
A Mali da Burkina Faso, BBC ba ta samu wanda zai yi mata bayanin halin da waɗannan mutane ke ciki ba.











