Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka kubutar da sauran ɗaliban makarantar St. Mary 130 da ke jihar Neja
Hukumomi a Najeriya sun ce an sako sauran dalibai 130 da aka yi garkuwa da su a jihar Neja.
Wasu 'yan bindiga ne suka sace daliban da ma'aikatan makarantar ta Katolika ta Saint Mary a a watan da ya gabata.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Sunday Dare a shafinsa na X ya sanar cewa a: yanzu: 'Ba bu wani dalibi ko ma'aikacin makarantar da aka bari a hannun yan bindga'.
Mai makarantar kuma shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Neja, Bishop Bulus DauwaYohanna, ya shaida wa BBC cewa Gwamnan jihar Neja ya tabbatar masa da alamarin:
"Gwamna ya kira ni yanzu inda ya sanar da ni cewa an sako sauran 'yan makaranta da malamai. Ya ce na zo na karbe su," in ji shi.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Neja, Adamu Abdullahi Elleman ya shaida wa BBC cewa a halin yanzu jamian tsaro na duba lafiyar daliban da malamansu kuma a ranar Litinin ne za a mika su ga iyayensu.''
Sai dai bai bayyana ko an biya kudin fansa ba.
Wadanda aka sako na cikin dalibai 303 da kuma ma'aikatan makarantar ta Katolika ta St Mary 12 da yan bindiga suka sace lokacin da suka kai wa dakunan kwana hari a ranar 21 ga watan Nuwamba.
Mahukantan makaratar sun ce wasu dalibai 50 sun tsere a lokacin da aka kai hari inda aka yi garkuwa da dalibai fiye da 200.
A farkon watan da muke ciki mahukuntan Najeriya sun sanar da sakin dalibai 99 da kuma wani malami 1 inda aka bar akalla wasu dalibai 165 a hannun yan bindiga.
Sai dai kwamishinan 'yan sandan jihar Neja ya shaida wa BBC cewa mutum 130 da aka sako a ranar Lahadi kuma su ne wadanda suka rage a hannun yan bindiga inda ya ce an samu akasi kan alkaluman farko da mahukuntan makarantar suka fitar.
Daliban da aka sace a jihohin Neja da Kebbi a baya--bayan nan sun sa hukumomin Najeriya rufe makaratun sakandire na tarayya 47 kan dalilan tsaro kodayake a baya bayan nan sun sake bude makarantun su na masu cewa sun yi haka ne bayan da aka karfafa tsaro a ciki da kewayen makarantun
A halin da ake ciki dai, makarantu a jihar ta Neja gaba daya sun ci gaba da kasancewa a rufe yayin da hukumomin jihar suka dage cewa za su bude su ne kawai idan sun tabbatar da tsaro a cikin makarantu da kewaye.