Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba mu da tabbas kan adadin ɗaliban St. Mary da aka sace - Gwamnan Neja Bago
Gwamnan jihar Neja Umar Bago ya ce duk da cewa ba ya so a mayar da hankali kan ɗora wa wani laifin sace ɗaliban makarantar St. Mary's ta Papiri, ya dasa alamar tambaya kan haƙiƙanin adadin ɗaliban da aka sace.
A ranar Juma'a da ta gabata ne aka wayi gari da labarin sace ɗaliban makarantar 303 da wasu malamai 12 a makarantar da ke yankin ƙaramar hukumar Agwara a jihar Neja.
Sai dai lamarin ya fara jawo muhawara mai zafi ne bayan da gwamnatin jihar ta ce sai da ta bayar da umarnin a rufe makarantun yankin da abin ya faru baki ɗaya, sakamakon samun rahoton barazanar tsaro, amma makarantar ta yi gaban kanta wajen sake buɗe karatu ba tare da neman izinin gwamnati ba.
A cikin wata hira da BBC, shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN reshen jihar, Bishop Bulus Dauwa Yohanna ya musanta iƙirarin gwamnan cewa an buƙaci su kulle makarantar.
''Ba wanda ya ce mana mu rufe makaranta saboda barazanar tsaro, ba inda aka taɓa faɗa mana haka'', in ji shi.
Amma a zantawarmu da gwamnan jihar, Umar Bago ya nanata cewa lallai gwamnati ta bayar da umarnin rufe makarantar saboda matsalar tsaro, sannan ya ƙara da cewa "ko bayan samun labarin hare-hare a jihar Kebbi da Kwara mun sake bayar umarnin a rufe makarantun da ke yankin Neja ta Arewa," in ji shi.
Barazanar Trump
An fara samun saɓanin ra'ayi tsakanin gwamnati da ƙungiyar CAN, tun bayan da ƙungiyar ta ce ɗalibai 50 daga cikin waɗanda aka sacen sun kuɓuta.
Bayan da CAN ta fitar da sanarwar da a ciki ta ce tuni aka mayar da ɗaliban wajen iyayensu, ƴansanda suka ce suna da shakku game da labarin kuɓutar ɗaliban, musamman kan adadin ɗaliban.
Ƴansandan sun ce sun buƙaci ƙungiyar ta ba su hujjar kuɓutar ɗaliban, amma ba su samu ba, don haka rundunar ta ce, "ba mu da tabbacin alƙaluman yaran da suka tsere da ma inda sauran suke a yanzu."
A nasa ɓangaren, gwamnan Neja ya ce yanzu ba lokacin da za a tsaya ana ka-ce-na-ce ba ne, "saboda yara dai sun riga sun ɓace. Don haka aikinmu a yanzu shi ne nemo hanyoyin ceto su."
Ya ce maganar an sace sama da mutum 300 "shi ne ƙalubale. Na farko an shiga makaranta ɓangaren firamare an yi harbi da bindiga, inda wasu suka tsorata suka gudu. Amma an ce wasu daga cikin yaran kusan 51 sun kuɓuta har ma sun koma gida."
"Na biyu mun buɗe rajista cewa duk wanda yake da yaro da ya ɓace ya kawo mana sunansa da bayaninsa domin mu duba abin da makaranta ta ba mu da kuma abin da iyayen suka ba mu, amma zuwa yanzu (ranar Talata) mutum 14 ne kawai suka cika rajistar cewa an sace yaransu," in ji gwamnan na Neja.
Sai dai ya ce ba sa kokwanton an sace ɗaliban, domin a cewarsa ana garkuwa da mutane, "amma maganar gaskiya lambar ta tsoratar da mu, ta tsoratar da duniya," in ji shi, sannan ya ƙara cewa, "Dole ne mu yi hankali wajen tabbatar da zaman lafiyar Najeriya."
Ya ce dama babban burin maharan shi ne su ƙara haifar da tashin hankali, "kuma tunda suka ji maganar Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump, sai suka ƙara ƙaimi domin ta'azzara masifar. Maganar Trump ta ƙara ta'azzara matsalar saboda za ki ga sace-sacen ya ƙaru a ɓangarorin ƙasar, shi ya sa muka kulle makarantu saboda rigakafi."
Haɗin kan makaranta
A game da dalilan da ya sa gwamnatin take dasa alamar tambaya kan adadin ɗaliban da aka sace, gwamnan ya ce makarantar ta gaza wajen fitar da haƙiƙanin adadin ɗaliban.
"Mun ce makaranta ta ba mu rajista, amma ba mu samu ba. Makaranta kaɗai ba za ta ba mu takarda ba, a ba mu rajista idan an ɗauki ɗalibi dole akwai hotonsa da iyayensa, ba zai yiwu hukumar makaranta kaɗai ta fito da bayani ba. Shi ya sa muka buɗe rajista tare da jami'an tsaro cewa duk wanda yake da wanda ya ɓace ya zo ya ba mu sunansa."
Ya ce da rajistar za su yi amfani wajen tantance waɗanda suka kuɓuta, sannan su samu bayanai muhimmai kan asalin abin da ya faru.
Ya ce jami'an tsaro sun ce makarantar ba ta ba su ba su haɗin kai, domin a cewarsa ko ɗalibai 51 da aka ce an kuɓutar, "bai kamata a kai su gida ba, ya kamata a miƙa su ga jami'an tsaro ne a duba lafiyarsu, sannan a samu labari daga wajenu, amma sai aka kai su gida, shi ya sa aka samu ƙalubale," in ji Bago.
Amma a game da abin da gwamnatin ke yi wajen kuɓutar da yaran, gwamnan ya ce jami'an tsaro da gwamnatinsa suna aiki tuƙuru domin tabbatar da yaran sun koma gida lafiya.
A game da rufe makarantu a jihar, gwamnan ya ce makarantun kwana ne za a rufe, sannan idan aka samu tabbacin tsaro, za a buɗe wasu.
Hare-hare a Naja ta Arewa
A game da yadda yankin Neja ta Arewa ta daɗe tana fama da matsalolin hare-hare, gwamnan ya ce yanki ne mai girma sosai, inda ya ce amma suna ƙoƙarinsu domin magance matsalar.
Ya ce yankin Neja ta Arewa bai fi ƙarfin gwamnatinsa ba, "Jihar Neja kaɗai ta fi girman wasu yankunan a kudu, sanna yankin da ake magana ya fi girman Enugu da Anambra baki ɗaya, saboda haka Neja ba karamar jiha ba ce, kuma muna da bakin iyaka da ƙasashen Nijar da Burkina Faso da Mali da jihohin Zamfara da Kebbi,"
Ya ce ana fuskantar matsalolin tsaro daga sassan da suke maƙwabtaka da jihar, amma a cewarsa, "wannan gandun dajin da aka tanada a baya domin adana namun daji, shi ne a yanzu za mu nome mu samar da abinci," in ji shi, inda ya ƙara da cewa tun sun fara aikin.
Sai dai ya yi albishir ga iyayen ɗaliban, inda ya ce gwamnati na jajanta musu, sannan ya ce za su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da ak kuɓutar da ɗaliban lafiya ƙalau.