Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne zai gaji jagoran addinin Iran Ayatollah Khamenei?
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Iran na shirin sanar da "sabbin matakai" game da shirinta na nukiliya domin samun damar cimma yarjejeniya da Amurka.
Matakin zai bayar da damar ɗage wa ƙasar takunkumai da kuma amincewa da shirinta na sarrafa makamashin nukiliya ƙarƙashin shirinta na zaman lafiya.
Reuters ya ambato wani babban jami'in gwamnatin Iran na cewa ɓangarorin biyu sun sha bamban a wasu fannoni, ciki har da batun sassauta tsauraran takunkuman Amurka da ke kan ta.
Wannan na zuwa ne yayin da Oman, ƙasar da ke shiga tsakanin ɓangarorin biyu, ta tabbatar cewa za a shiga zagaye na gaba na tattaunawar a birnin Geneva, ranar Alhamis.
Wani jami’i ya kuma ce Iran “na tunanin yanke shawarar fitar da rabin makamashin uranium dinta da ta inganta zuwa waje.
Ya ce Iran za ta dauki wannan mataki ne bisa sharadin cewa Amurka za ta amince da shirin Iran na sarrafa makashin nukiliya na zaman lafiya, kuma yarjejeniyar za ta kunshi cire wa Iran takunkumai.
Haka nan daga cikin yarjejeniyar, Iran za ta bai wa kamfaninin Amurka damar gudanar da kwangila a wasu bangarorin tattalin arziki na kasar, kamar bangaren man fetur da gas.
A bangare daya, shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce akwai alamun haske a tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka, sai dai ya nanata cewa Iran a shirye take kan ko ma mene ne zai faru.
A cikin wani bayani da ya wallafa a shafin X, Pezeshkian ya ce “Iran a shirye take ta rungumi zaman lafiya a yankin. Mun tattauna kan matakan da za a dauka a tattaunawa ta baya-bayan nan. Sai dai muna ci gaba da lura da take-taken Amurka kuma mun shirya game da duk abi da zai iya faruwa.”
Magajin Khamenei
A watannin baya-bayan nan jaridar New York Times ta Amurka ta bayar da rahoton yadda jagoran addini na Iran Ali Khamenei ya miƙa ragamar wasu ayyukanshi ga wani babban jami'in tsaro, Ali Larijani, yayin da lamurra ke ƙara rincaɓewa tsakanin Iran da Amurka, inda har ake tunanin cewa yaƙi zai iya ɓarkewa tsakanin ɓangarorin biyu.
Rahoton ya kafa hujja ne da tattaunawar da ya yi da manyan jami'an gwamnatin Iran shida - ɗaya daga cikin su na da alaƙa da ofishin jagoran addinin - wasu uku kuma na cikin dakarun juyin-juya-halin ƙasar, sai kuma tsofaffin jami'an diflomasiyyar Iran, da kuma rahotannin da jaridun Iran.
Daga ɓangaren Khamenei, ya bai wa Larijani - wanda gogaggen ɗan siyasa ne kuma tsohon sojan juyin-juya-hali - wanda a halin yanzu shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta Tsaron Ƙasa - ya riƙe wasu ginshiƙan ayyukan gwamnati.
Majiyoyi sun tabbatar cewa tasirinsa ya faɗaɗa, har ta kai ga sanya ido kan zanga-zangar da ake yi a cikin ƙasar, da tafiyar da tattaunawa da ƙasashe irin su Rasha, da tattaunawa da ƙasashe irin su Qatar da Oman da kuma lura da tattaunawar da ake yi da Amurka game da shirin nukiliyar Iran.
Jami'ai sun bayyana cewa yana bayar da umarni wajen tabbatar da tafiyar da al'amuran gwamnati, ko yunkurin kashe jagororin ƙasar, ciki har da jagoran addini.
Bayanai sun tabbatar da cewa an samar da tsarin waɗanda za su gaji jagororin soji da gwamnati, waɗanda jagoran addinin ƙasar ke naɗawa, inda aka ɗora wa kwamandoji nauyin zaƙulo waɗanda suke ganin za su iya zama magada.
Haka nan wasu majiyoyin sun ce Iran na ta ƙoƙarin fitar da shirinsu idan har Amurka ta ɗauki matakin kai hare-hare a ƙasar, duk kuwa da ci gaba da ake yi da tattaunawa ta diflomasiyya, inda suka ce an sanya dakarun sojin Iran cikin shirin ko ta kwana.
Khamenei ya yi gargaɗin cewa makaman Iran na da ƙarfin da za su nutsar da jiragen ruwan yaƙi na Amurka, kuma ya yi gargaɗin cewa duk wani mataki na kai wa Iran hari zai iya haifar da rikici a ɗaukacin yankin.