Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda 'yan bindiga suka kori makiyaya daga gidajensu a Kaduna
Daruruwan Fulani makiyaya na cikin tsaka mai wuya a yankin karamar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya, saboda yadda 'yan bindiga suka raba su da shanunsu, sannan kuma suke musu dauki dai-dai don neman kudin fansa, baya ga kona musu gidaje.
Yawanci makiyayan da sauran jama'ar garuruwa akalla biyar da ke yankin arewacin Kagarko a yanzu sun yi gudun hijira zuwa garin Kagarko, inda suka sami mafaka a kangaye da makarantu da gidin bishiyoyi.
Wata mata da ke gudu hijira sakamakon wannan iftila'i da BBC ta zanta da ita ta waya, ta ce gaskiya suna cikin hali marar dadi domin sun baro gidajensu da gonakinsu inda yanzu haka suke cikin gonakin wasu mutane suna fakewa.
" Ba wani daki ba wani kara , a zube muke kawai a gindin itace muna kwanciya, kuma dan abincin da muka samu mu ka gudu da shi shi muke riritawa, amma batun ruwan sha kam sam babu domin sai mun je nesa muke samu." In ji matar.
Shi kuwa wani magidanci daga cikin 'yan gudun hijirar, ya shaida wa BBC cewa yanzu suna cikin gonakin mutane kuma sun shafe makonni uku a wajen saboda 'yadda bindiga suka addabi garuruwansu, kuma suna zaune a cikin yanayi na iska da sanyi,sannan wadanda suke ke zaune a inda shi ya ke sun kai 200.
" Masu garkuwa mutane sun addabi garuruwanmu su kwashe mana shanu, sannan kuma su sace mutane har su nemi kudin fansa."In ji shi.
Honarabul Is'ahaka Ahmad Mo-Gauri, shi ne shugaban reshen kungiyar Fulani makiyaya ta Mi-Yetti-Allah na yankin karamar hukumar Kagarko a jihar ta Kaduna, ya shaida wa BBC cewa wadanan 'yan gudun hijira na cikin halin kaka-ni-ka-yi:
" Da naje wajen da wadannan makiyaya suka nemi mafaka sai da na ji kamar a zubar da hawaye saboda duk mutane nan kwance a gindin bishiyoyi ga 'ya'ya mata ga kuma yara kanana abin dai akwai tausayi, sannan ga wasu kuma a makarantu duk suna neman mafaka." in ji shi.
Ya ce," Idan ban da shugaban karamar hukumar ta Kagarko da ya ziyarci wadannan fulani makiyaya, babu wani jami'in gwamnati da ya kai musu ziyara ballantana tallafi, kuma lamarin nan ya fi karfin shugaban karamar hukuma."
Daga bisani shugaban reshen kungiyar Fulani makiyaya ta Mi-Yetti-Allah na yankin karamar hukumar Kagarko a jihar ta Kadunan, ya yi kira ga gwamnati ta jiha da ma ta tarayya akan ta kai wa wadannan bayin Allah daukin da ya dace saboda a cewarsa idan damuna ta sauka suna cikin wannan yanayi to akwai babbar matsala.