Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Martanin da Miyetti-Allah ta mayar wa Amurka kan zargin kisan Kiristoci
Ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a Najeriya ta ce babban aikinta shi ne kare muradun makiyayan Najeriya.
Cikin wata hira da BBC, Shugaban ƙungiyar na ƙasa Baba Othman Nganzerma ya bayyana Miyetti Allah da kasancewa ƙungiyar masu sana'ar kiwo, ba tare da la'akari da addini ko ƙabila ba.
'' A cikin ƙungiyar mu babu ƙabila ko addinin da babu a ciki, kama dga Hausawa da Yarabawa da Al'ummar Igbo da sauran ƙabilu, haka ma akwai mabiya addinin Musulunci da Kirista duka a cikinta'', in ji shi.
A watan da ya gabata ne dai Amurka ta lissafa ƙungiyar cikin waɗanda ƙasar ke duba yiwuwar sanya musu takunkumai, saboda zarginsu da hannu a kisan Kiristoci a Najeriya.
Sai dai shugaban ƙungiyar ya ce ya yi mamakin ganin sunan ƙungiyar cikin wannan jeri.
''Dalili shi ne kuwa shi ne mu ba ma riƙe da makamai, sannan ba mu taɓa ɗaukar nauyin wani hari a ƙasar nan ba, haka kuma gwamnati ba ta taɓa kama mu da laifi ba'', in ji shi.
Me Amurka ta ce kan Miyetti Allah?
A farkon watan nan ne ƴan majalisar wakilan Amurka suka gabatar da wani ƙudiri a zauren majalisar wanda ya ƙunshi rahoto kan kwamitin bincike game da zargin cin zarafin Kiristoci da musguna musu a Najeriya.
Riley Moore da takwaransa Chris Smith ne suka jagoranci gabatar da ƙudurin, inda suka ce kwamitinsu ya gano "an daɗe ana musguna wa Kiristoci a Najeriya".
Ƴanmajalisar waɗanda na jam'iyyar Republican ne sun nemi Amurka ta sanya takunkumai kan wasu ƙungiyoyi - ciki har da Miyetti Allah - da kuma ɗaiɗaikun ƴan Najeriya saboda zargin da hannu a kisan Kiristoci.
Ƴanmajalisar sun zargi ƙungiyoyar Miyetti Allah da Kautar Hore da hannu a kashe-kashen da ake yi wa Kiristoci a Najeriya.
Don haka ne suka buƙaci a sanya wa ƙungiyoyin biyu takunkumai da hana su izinin shiga Amurka da ma kwace wasu kadarorinsu.
'A ko'ina akwai ɓata-gari'
Dangane da zargin da ake yi wa mambobin ƙungiyar da aikata laifuka, Shugaban Miyetti Allah ya ce bai kamata a alaƙanta ayyukan ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyar ba.
''Kana iya samun ɓata-gari cikin ƴansanda da sojoji, amma hakan baya nufin duka hukumomin su zaɓa ɓata-gari ba'', in ji shi.
Don haka ne ya ce bai kamata a riƙa ɗora wa ƙungiyar alhakin laifukan ɗaiɗaikun mambobinta ba.
''Kuma ba Miyetti Allah kaɗai ce ƙungiyar makiyaya a Najeriya ba, akwai ƙungiyoyin makiyaya masu ɗimbin yawa, don haka ba duka makiyaya ko Bafulani ne ke zama mambanmu ba'', kamar yadda ya yi ƙarin bayani.
Wane martanin ƙungiyar ta yi wa Majalisar Amurka?
Baba Usman Ngenzarma ya ce ƙungiyar MACBAN ta mayar da majalisar Amurka martani ta hanyar rubuta mata wasiƙa domin fayyace mata wace ce ita da kuma irin ayyukan da take yi.
''Mu a tarihin ƙungiyarmu hukumomin Najeriya ba su taɓa zarginmu da wani laifin tallafa wa ta'addanci ko matsalar tsaro a Najeriya ba'', a cewarsa
Baba Usman Ngenzarma ya ce ƙungiyarsu na aiki da jami'ai da hukumomin tsaron Najeriya domin tabbatar da aiki bisa doka da oda.
Ya ce ƙungiyar ta rubuta wa majalisar wasiƙa tare da bayyana mata hujjoji masu ƙarfi da ke nuna cewa tana aiki da jami'an tsaro da kuma gwamnatin Najeriya.
''Hatta cibiyoyin gwamnati da na ƙasashen waje duka muna hulɗa da su, sannan muka muna musu cewa su kansu makiyaya wannan matsala ta shafe su'',.
Ya ce sun rubuta wa majalisar Amurka cikakkun bayanan mambobinsu da aka kashe sakamakon matsalar tsaro.
''Mun rubuta sunayensu da kwanan watan ranakun da aka kashe su da ma hotunan irin kisan da aka yi yi ƙananan yara da matasa daga cikin al'ummar makiyaya'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa sun rubuta duka waɗannan sun bai wa jakadan Amurka a Najeriya, bayan sun zauna da shi sun kuma bayyana masa ainihin matsayarsu.
''Haka kuma mun zauna da wasu ƙunyoyi na ƙasashen waje domin bayyana musu matsayin, mun kuma rubuta wa shugaban majalisar dattawan Najeriya da kakakin majalisar wakilan ƙasar da ministan ƙasashen waje da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro''.
''A zaman namu mun shaida musu matsayarmu, da faɗa musu cewa haƙƙinmu na kansu, don haka dole su fito su fahimtar da Amurka game da yadda ta fahimce mu, saboda su sun sanmu fiye da shekara 40'', kamar yadda ya bayyana.
'Gasar mallakar filaye ne ke kawo faɗa a Najeriya'
Shugaban ƙungiyar ta Miyetti Allah ya ce gasa kan mallakar filaye ne ke haifar da rikici tsakanin al'umomin Najeriya ba addini ba.
''Faɗan da ake yi galibi ana yi ne saboda gasar mallakar filaye ba saboda addini ko ƙabilanci ba'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya ci gaba da cewa wannan ne ainihin abin da ke haifar da rikicin da ya shafi makiyaya a Najeriya, ba addini ba kamar yadda ake yayatawa.
''Faɗan da ake yi da ya shafi makiyaya a Najeriya, ya samo asali ne daga gasar amfani da ƙasa,wadda ikta kuma wannan ƙasa ba ta ƙaruwa, saboda matsalolin kwararowar hamada da take fuskanta'', in ji shi.
''Idan ka ce faɗan Filato na addini ne saboda tana da tarihin faɗan addini, to a jihar Benue fa?, can ma na addinin ne''?
Shugaban ƙungiyar ya kuma yi nuni da hare-haren da ake yawaitar samu a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna.
''Ai su waɗannan jihohin Musulman ake kashewa su ake kamawa su ake kora daga gidajensu, don haka matsalar tsaron Najeriya ba ta addini ko ƙabila ba ne'', in ji shi.
Wace ƙungiya ce Miyetti Allah?
''Miyetti Allah'' kalmomin Fulatanci ne guda biyu da ke nufin ''Na gode wa Allah''.
An yi wa ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) rajista a matsayin ƙungiyar ƙasa, ranar 12 ga watan Fabrairun 1986, a cewar Baba Othman Ngenzarma.
Sai dai ya ce kafin wannan lokaci ƙungiyar na aiki da rajista ta jihohi daban-daban galibi na arewacin ƙasar.
''Kafin nan tana aiki a matakin jihohi, alal misali Borno da Kaduna, kafin a haɗe ta ta zama ta ƙasa baki ɗaya'', in ji shi.
Kuma ƙungiyar na da shalkwatarta ta ƙasa a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.