Me ya sa Majalisar Amurka ke son a hukunta Kwankwaso?

Lokacin karatu: Minti 7

An gabatar da wani ƙuduri a gaban Majalisar wakilan Amurka wanda ke son ganin Amurkar ta ɗauki mataki kan Najeriya game da zarge-zargen gallazawa da kuma musguna wa mabiya addinin Kirista.

Ɗan Majalisa Riley Moore da takwaran aikinsa Chris Smith ne suka jagoranci gabatar da ƙudurin, inda suka ce kwamitinsu ya gano abubuwa da dama da suka nuna cewa "an daɗe ana musguna wa Kiristoci a Najeriya".

Sai dai wani abu da ya fi ɗaukar hankali a cikin ƙudurin shi ne anbaton sunan tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Kwankwaso a matsayin mutum ɗaya tilo da ya kamata a hukunta, kan hannu a cikin taimaka wa ayyukan da suka shafi cin zarafin Kiristoci.

Sauran waɗanda rahoton ya ambato ƙungiyoyi ne, waɗanda su ma ƙudurin ya ce suna cikin masu aikata abubuwan da ba su dace ba kan Kiristoci a Najeriya.

Martanin al'umma kan ƙudurin majalisar Amurka

To amma me ya sa sunan Kwankwaso ya fito ɓaro-ɓaro a rahoton?

Wannan ne babban abin da ya shige wa mutane da dama duhu kasancewar a bayyane babu wani ƙwaƙƙwaran zargi da aka taɓa yi wa Kwankwaso a batun rashin tsaro ko kashe-kashe a Najeriya.

Hasali ma Kano, wadda ita ce jihar da ya mulka ba ta da alaƙa da kashe-kashe ƙabilanci a baya-bayan nan, ba kamar jihohi irin su Benue, Filato ko Kaduna ba, waɗanda su ne suka fi ƙaurin suna a kan haka.

Haka nan da dama daga cikin ƴan Najeriya ba su kallon Kwankwaso a matsayin mutum mai tsattsauran ra'ayi na addini ko goyon bayan hakan, kuma siyasarsa ba ta nuna hakan ba.

Shi ya sa wasu da suka mayar da martani a shafukan sada zumunta suka soki batun sanya sunan ɗan siyasar a cikin waɗanda suka kamata a hukunta.

Shehu Sani ya ce "Duk ƙungiyar da ta ɗauki makami domin kisa ko sace mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ta kowane irin salo, ta cancanci a ayyana ta a matsayin ƙungiyar ƴan ta'adda. To amma ƴan Majalisar dokokin Amurka na buƙatar yin bincike mai zurfi domin tantance bayanansu. Sanata Kwankwaso bai taɓa zama mai tsattsauran ra'ayi, ko goyon baya ko kuma ƙarfafa musguna wa wasu a dalilin addini ba."

"Ba wai ina kare Sanata Rabi'u Kwankwaso ba ne, amma na yi matuƙar mamakin yadda aka sanya sunansa (a cikin rahoton majalisar wakilan Amurka). A iyakar sanin da na yi masa a tsawon lokacin da ya riƙe muƙamin gwamna, ministan tsaro, sanata da kuma jagoran siyasa, yakan dage kan yaƙi da ta'addanci da ƴan ta'adda ta kowane fanni."

Omojuwa ya ce "...ina kallon shi (Kwankwaso) a matsayin mutumin da aka ambata ba bisa adalci ba, kawai saboda ya goyi bayan ƙasarsa. Musamman ma ganin matsayarsa ba ta zamo barazana ga wata ƙasar ba."

Mene ne dalilin Amurka na zargin Kwankwaso?

Wani abu da mutane ke nuni da shi a baya-bayan nan shi ne yadda aka samu musayar kalamai tsakanin Rabi'u Kwankwaso da ɗan majalisar Amurka Riley Moore, bayan matakin shugaban Amurka Donald Trump na ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kanta.

A saƙon da ya wallafa, Sanata Kwankwaso ya ce "Na damu ƙwarai game da matakin Shugaba Donald Trump na baya-bayan nan. Wannan ya biyo bayan yadda ya ayyana Najeriya a matsayin 'ƙasar da ake da damuwa a kanta'.

"Yana da muhimmanci a nanata cewa ƙasarmu ƙasa ce mai ƴanci, wadda al'ummarta ke fuskantar barazana daga marasa bin doka a faɗin ƙasar. Rashin tsaron da muke fuskanta ba ya bambancewa tsakanin mabambanta addini, ƙabila ko siyasa," kamar yadda ya bayyana a wani ɓangare na saƙon da ya wallafa a shafinsa na X.

Sai dai a martaninsa kan haka, ɗan majalisa mai wakiltar West Virginia a majalisar dokokin Amurka ya soki Kwankwaso kan matsayarsa.

A martanin da ya mayar wa Kwankaso, Moore ya ce "Gwamna – shin za ka mayar da martini kan hannun da kake da shi wajen kisan Kirsitoci?

"Ka kafa shari'a. Ka sanya hannu kan dokar da ta tanadi hukuncin kisa kan abin da kuka bayyana da saɓo," a cewar Moore lokacin da Kwankwaso ya wallafa wani bayani da ke sukar matakin Amurka na ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kan ta, a shafin X.

Mece ce alaƙar Kwankwaso da Shari'a?

A watan Yulin shekara ta 2000 ne Kano ta zama jiha ta biyu da ta amince da fara aiki da shari'ar Musulunci lokacin mulkin Rabi'u Kwankwaso.

Amincewa da shari'ar ta zo ne a daidai lokacin da jihohin Najeriya da dama ke hanƙoron fara aiki da tsarin shari'ar Musulunci bayan ƙaddamar da ita karon farko a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin ƙasar.

A wannan lokaci an riƙa yin zazzafar muhawara game da batun amfani da shari'ar Musulunci, inda mabiya wasu addinan suka nuna adawa da hakan, lamarin da ya kai ga an samu rikicin addini a jihar Kaduna tsakanin watan Fabarairu zuwa Mayun shekara ta 2000, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiya.

Amincewa da shari'ar Musulunci na nufin amfani da hukunce-hukunce da addinin Musulunci ya tanada a rayuwar al'umma ta yau da kullum.

Ƙarƙashin tsarin, akan zartar da hukunce-hukunce kamar na yanke hannu ga wanda aka samu da laifin satar da ta kai wani mizani, da yin bulala ga masu yin ƙazafi ko kuma zina, har ma da hukuncin kisa ga wanda ya kashe wani da gangan ko kuma ma'auratan da aka samu da aikata zina.

Sai dai Rabiu Kwankwaso na daga cikin gwamnoni da suka riƙa jan ƙafa wajen amincewa da shari'ar Musulunci a jihar ta Kano.

Wasu ma na ganin rashin mayar da hankalinsa wajen aiwatar da shari'ar na daga cikin abubuwan da suka sa ya faɗi zaɓe a shekara ta 2003, lokacin da Malam Ibrahim Shekarau ya kayar da shi.

Bayan Zamfara da Kano, sauran jihohin da suka biyo bayan wajen amincewa da shari'ar Musulunci su ne Sokoto, Katsina, Bauchi, Borno, Jigawa, Kebbi, Yobe, Kaduna, Niger, da kuma Gombe.

Wane ne Rabiu Kwankwaso?

Rabiu Kwankwaso na daga cikin sanannun ƴan siyasa a Najeriya, inda yake jagorantar ƙungiyar da ake wa laƙabi da Kwankwasiyya, wanda aka samu daga sunan da aka fi saninsa da shi, wato Kwankwaso. Kuma shi ne jagoran jam'iyyar NNPP.

Tsohon gwamnan jihar Kano, jiha mafi yawan al'umma a Najeriya.

Ya mulki jihar na tsawon shekarar takwas a wa'adi biyu. Da farko ya mulki jihar daga shekarar 1999 lokacin da Najeriya ta koma mulkin dimokuradiyya, har zuwa shekara ta 2003, lokacin da ya faɗi zaɓe a ƙoƙarin komawa a wa'adi na biyu.

Daga nan ne tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya naɗa shi ministan tsaro na Najeriya.

Bayan shekara takwas, Rabi'u Kwankwaso ya sake yin takarar gwamnan Kano a shekara ta 2011, inda aka sake zaɓen sa, kuma ya yi mulki har zuwa watan Mayu na shekara 2014.

Daga nan ne kuma aka zaɓe shi sanata mai wakiltar Kano tsakiya a majalisar dattijai.

Rabi'u Kwankwaso ya yi takarar shugabancin Najeriya a zaɓen shekara ta 2023 ƙarƙashin inuwar jam'iyyar NNPP, sai dai bai yi nasara ba.

An haife shi ne a watan Oktoban 1956 a ƙauyen Kwankwaso dake ƙaramar hukumar Madobi ta jihar Kano.

Abubuwan da Amurka ta ce ta gano kan zargin musguna wa Kiristoci a Najeriya

Majalisar dokokin Amurkar ta bayyana cewa bincike da ta gudanar, ya gano abubuwa da dama da aka yi wa Kiristoci a Najeriya.

Ta ce "an daɗe ana kashe Kiristoci a Najeriya, inda tun 2009 ake kashewa, garkuwa, fyaɗe da kuma tarwatsa ƙauyukan da Kiristoci ke zama".

Har ila yau, ta ce ƙungiyar Boko Haram da ISWAP sun tilasta wa Kiristoci da dama yin gudun hijira.

Kudurin na majalisar dokokin Amurka ya kuma kiyasta cewa Kiristoci tsakanin 50,000 zuwa 125,000 ne aka kashe saboda yin imani da addininsu daga shekara ta 2009 zuwa 2025, tare da far wa majami'u kusan 19,000.

Sai dai alƙaluma daga masu bincike da masana kan tsaro da dama sun sha bamban da irin wadanda Amurkar ke fitarwa.

Sauran abubuwan da majalisar ta ce ta gano sun haɗa da:

  • Ƙungiyoyin ƴanbindiga sun kai hare-hare da dama kan al'ummomin Kirista, abin da ya janyo tarwatsa su daga matsugunansu.
  • Tsakanin watan Mayun 2023 da Mayun 2025, ƙungiyoyin Fulani ɗauke da makamai sun kai munanan hare-hare a jihohin Benue Plateau.
  • Garkuwa da malaman addinin Kirista waɗanda suke da'awar zaman lafiya
  • An kashe shugabannin addinin Kirista sama da 250a shekaru goma da suka wuce, ciki har da rabaren Sylvester Okechukwu a 2025
  • Najeriya na da kashi 72 na Kiristocin da aka kashe kan imani da addininsu a faɗin duniya
  • An ɗaiɗaita Kiristocin Najeriya kusan miliyan biyar
  • Kusan 343,000 ne ke gudun hijira a Tafkin Chadi